GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 21-30

21_*
Arewabook@Mamuhgee
Tana isowa gidan tun a compound tasan Abbi yadawo gida sbd ganin sabuwar motarsa da tunda sukazo take a gefe rufe ruf Amma gatanan a fake gefe da alama da ita aka daukosa daga airport.

Kofar palonsu ta dosa tana warware nadin qaramin gyalen dake kanta tun daga hanya
Tana isa ta bude kofar Kai tsaye ta shige.

Bakowa a palon sai Qamshin RoseNight da Sanyin AC daya Gama cike palon
Saikuma qatuwar tv dake aiki ba murya sosai.

Su zubbi da Salimat tuni suka Gama aikinsu suka nufi bangarensu tunda Mai gidan na gari Dan haka idan ba aiki ba Babu abinda zai Kuma shigowa dasu saikuma idan kiransu akai.

Dakinta ta nufa direct ta tube tafada toilet tayi wanka ta fito daureda towel.

Kiran Dr ne yashigo wayarta da sauri sauri ta dauka tace Masa”

I’m kinda busy
I will call you.

Aje wayar tayi tareda nufar gaban madubi ta shafa Neutrogena oil dinta ta fesa spray kawai ta koma gurin kayanta ta saka wata chiffon wide neck gown Mara nauyi ta ziro slippers ta fito ko wayarta Bata daukoba.

Kai tsaye hanyar palon Abbi ta nufa tana tunanin yanda ya shammaceta Saida yadawo ya fada Mata da ba lallai ta jima gurin aikinba ayau.

Da farin ciki bayyane kan kyakkyawar fuskarta tayi knocking kofar harso biyu kafin taji muryarsa daga ciki a natse ya furta”

Yes Inayah,
You can cm in.

Shigowa tayi da sallamar dake bayyanarda farin cikinta na ganinsa ta qaraso har gefensa ta zauna tana cewa”

Abbi kana tunawa danima kuwa?
You look more than cool and calm.

Wani qayataccen murmushi Mara sauti ya sake Yana kallon yanda itama tayi Yar rama ta yanayin aikin data samu kanta aciki da cikakkiyar kulawa yace”

Dr INAYAH A MAJEED ko gaisuwa babu tukuna kafin complains su biyo baya.

Cikin murnarta tace’

Abbinah barka da dawowa
Munyi kewarka
Kagani har Rama nayi sbd ban saba dadewa hakaba bakanan,
Ga stress na aiki.

Yar dariya kadan yayi Yana cewa”

Duk kokarin Dr Abdul akanki menene da stress acikin aikin?

Dr Abdul yana fadamun irin kokarin da kike keep it up okay.
Tun yanzu Ina alfahari da ‘yata Zata Zama babbar likita wata ran.

Taji dadin kalmomin nasa Dan babu abinda yafi komai faranta ranta kaman ta faranta ran mahaifinta harya bayyanarda hakan.

Firar familyn CM tafarai Masa tana sanar dashi irin kulawa da kaunar dasuke Mata harma da umma yaganah.

Sosai yaji dadin hakan Kuma a gaban nata yakira Cm yayi Masa godia a gajarce na yanda iyalansa suka karbi nasa iyalin da hannu babbiyu.

Daganan firar Dr Abdul suka koma wadda kusan duk Rabin firar itace taketa fadar halayen Dr Abdul din dakuma yanda take kulawa da tattalinta.

Abbinta saurarenta kawai yakeyi Yana nazarin irin shaquwar data samu da Dr Abdul din lokaci daya,

Yana fatan alaqar da tsaya iya ta aiki sbd irin wannan yabo da Inayah ke Masa baya fatan tasake shiga wata soyayyar yanzu Musamman ko Dan yanayin weak heart nata
Duk da wani bangaren Dr Abdulsamad ya kwanta Masa sosai a Rai.

Sai dare tabaro gurin Abbin Dan abincima acan palonsa sukaci tare sbd shi kansa yariga yashige ne bazai fitoba sai gobe shiyasa shima Bai fito main hall ba cin abincin dare.

Tana baro palon Abbin gurin umma taje sukai Saida safe ta wuce daki ta kwanta bayan tayi waya sama sama da Dr Abdul akan daga gobe a
Shift din dare zasu sake komawa.

Washe gari da safe batada zuwa asibiti Dan haka baccin safe tayi sosai sai 11 ta fito lokacin Abbi baya gida ya fita.

Sanye da Riga da skirt na atampa ta fito tana waya da Neesah.

Breakfast tayi ita kadai sbd tasan ko umma ta jima da yin nata.

Tana gamawa ta nufi dakin umma yaganah acan tayi kwanciyarta tana chatting sama sama saiga su Mimi sun taho gidan dukkaninsu yiwa Abbi barka da zuwa aikuwa take gida ya kaure da hayaniya.

Mimi harda tsarabar wasu kayan atampopin tayiwa Inayah aikuwa umma ta gode Mata sosai itama Inayah din tanajin dadin kayan Dan haka ta gode mata.

Dakinta suka koma itada Safnah suna firarsu ta matasan ‘yan mata,

Fira suke akan anty Hafsat da Bata isoba sun biya sun ajeta gidan yayar mijin qanwarta dasuke tsananin mutunci sosai, daga can zaa kawota Nan din.

Saida suka gama cin abincin Rana kusan karfe biyu da mintuna kafin Anty Hafsat ta iso gidan.

Da farin cikin ganin siyama Inayah tarbota tun daga harabar gidan.

Faruk Ismail shine Wanda yakawo anth Hafsat daga gidansu.

Kallo daya yayiwa Inayah yaji Tai Masa sbd shima tunda yayo karatu a Malaysia yadawo yakasa ganin macen datai Masa gashi dama iyeyensa sun takurasa akan aure.

Ganin dayayiwa Inayah da yanayin gidan nasu yasa Kai tsaye ya ‘dan fahimci wayayyu ne jama’ar gidan,
Da alama sun danyi nasu yawon bude Ido wata qasar.

Inayah gabaki daya batama wani lura dashiba sbd hankalinta dake anty Hafsat da Siyama tana murmushi dukkanin kyanta na Kuma bayyana.

Anty Hafsat ce ta juyo ta kallesa tana cewa”

Ok faruk nagode sosai
Ka Isa gida lafiya.

Gyada Kai kawai yayi tareda tada motarsa yabar harabar gidan ya fice Yana ayyanawa aransa shikam yaga matar aure irin class dinsa dayakeso.

Inayah kam Anata bangaren ko kula batai dashiba Dan a daukarta driver nema yakawo antyn.

A gidan suka wuni Anata fira da hayaniya sai yamma da Abbin yadawo aka kaisu palonsa suka gaisa a matuqar mutunce da girmamawa.

Sai dare suka tafi bayan Abbi yayi musu kyautar kudi na Musamman ga Yara.

Inayah Jin tayi kaman kada su tafi sbd yanzu da qarfi da yaji tafara sabo da rayuwar hayaniya Dan duk Wanda zai Yi rayuwa a Lagos dolensa ya koya daukan hayaniya duk da sukam anguwarsu batada abinda ya hadata da hayaniyar ko hayaniyar ma Kai securities basa Bari magana suke maka sbd gudun shiga haqqin wasu.

Suna tafiya itama wanka da sallar ishai kawai tayi ta shirya cikin Riga da wandon Adidas sai qaramar veilhijab da jakar Nike data goyo ta fito tana qamshi Mai sanyi.

Umma yaganah ce ta rakota har kofa ta fito tana saka wayarta silent.

Abbinta ne da kansa zai kaita Dan haka gaban motar tashiga suka fice ta waiwayo ta kallesa cikin Yar shagwaba tace’

Abbi kaman karnaje Allah
Yau ban wani hutaba sbd baqi da akai.

Murmushi kawai yayi Mata yana cewa”

Zaki Saba Inayah.

Tura Baki kadan tayi tana lafewa jikin kujera.

Suna Isa asibitin Dr Abdul ma na isowa da ‘yar qaramar motarsa.

Ganin Alhaji MAJEED dinne dakansa yakawo Inayah yasa Dr Abdul qarasowa cikin nutsuwa da tsananin girmamawa ya gaida Abbin Yana cewa”

Barka da zuwa Sir.

Kallon Abdul din yayi da kyau cikin sake karantar nutsuwarsa ya gyada Kai shima a natse ya amsa da cewa”

Thank you Dr,
Ya aiki?
Ya fama patients da Inayah?

Murmushi yayi Yana Dan sake kallon Inayah dake kallonsa fuska asake
Ya kasa maida kallonsa sosai akan AA MAJEED din sbd tsananin kwarjini da cika Masa idon da yayi uwa uba ga wata irin nutsuwa da kamewa atare dashi,

Shima Adidas dinne a jikinsa black masu hade da hula yayi fresh acikinsu sosai tamkar sabon saurayi Mai tashen samartaka Dan kuwa shi Yama kasa yarda da shine ya Haifa zuqeqiyar budurwar ‘ya kaman Inayah.

A hankali yace”

Lfy kalau alhmdllh Sir.

Ok Tom Allah ya taimaka
Thank you ko.

U’re welcome Sir.

Jan motar Abbi yayi yabar gurin
Suma suka dunguma zuwa ciki.

Washe gari qarfe 8 tadawo gida wanka kawai tayi ta shige bargo sai bacci.

Bata farkaba sai 1 na Rana shima Kiran Anty Hafsat ne ya tadada.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button