INAYAH 21-30
Meyake Shirin faruwa da ‘yarsa idan komai ya lalace a daidai wannan gabar?
Sake Kiran sunansa Inayah tayi cikin sanyin murya ganin yanda yayi shiru kaman Yana nazarin wani abun.
Waiwayowa yayi ya kalleta da fuskar kulawa yace”
Kukan barin gidan ya isa haka Inayah,
Idan kina wannan kukan zan daga auren zuwa nxt month saiki sake cire kewan gida da kyau.
Murmushi tayi tana share hawayenta tace”
Na Dena kukan Abbi.
Wani murmushin Dole ya saki Yana sake boye damuwarsa yayi maga Yan maganganun dasuka sanyata sakewa sai gata tana dariya Wanda shikuma hakan yasake caza kansa akan abinda zai iya zuwa ya komo.
Lokacin sallar ishai dayayine yasanta ficewa daga palon Abbin Takoma.
Tana fita ya sauke wata nutsatsiyar ajiyar zuciya idanuwansa na neman sauyawa.
Miqewa yayi ya fice zuwa masallacin gidansa sallar ishai.
Ana Gama sallar yadawo ya rufe sashensa ya zauna Dan tattara abinda yake yawo cikin kansa Yana Neman juyawa.
Dafe gashi yayi Yana Jin gaban kansa kaman zaiyi bindiga tsabar nauyi da zafin daya dauka.
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun,
Meyesa wannan matar da Baya fatan sake ganin fuskarta har abada Zata bayyana rayuwarsa da ‘yarsa a daidai wannan lokacin Kuma ta bullo ta mabulla mafi firgici da tashin hankali.
Tun a shekarun baya tsanarta ta ginu cikin ransa tsanarda tasa ya rufe shafinta ruf daga rayuwarsa gabaki daya Dan ko a kamanni baya fatan sake ganin Mai kamarta,
Shin ita dince ma kuwa wadda yake tunani kokuwa?
Bazai taba manta kamannintaba sbd itace ta taka mahimmiyar rawa gurin ruguza rayuwarsa a karon farko,
Itace wadda ta wargaza buri da gatansa na zama cikin iyaye da ‘yan uwansa tasakashi a matsatsen hali mafi matsuwa da Muni.
Kamanninta Zane suke da baqin alqalami a idanuwansa,
‘yarsa Inayah da girman mahimmancinta da qauna Mai tsanani ta uba da ‘ya dayake Mata yasa ya yafewa matar Nan Amma Kuma har abada bayajin zai iya cire tsanarta Mai girma a ransa bare kallonta da daraja ko qima.
Haduwarsu ta farko da ita Bata Zama Alkhairi ba Dan hakan ko yanzu yasan bayyanuwarta rayuwarsa ba Alkhairi bane a rayuwarsa data ‘yarsa Dan haka Dole yanason Jin amsa biyu rak daga bakinta daga ya samu amsoshinsu bazata Kuma ganinsaba dagashi har ‘yarsa har abada.
Shi idan Yana cikin damuwa ko tashin hankali Sam baa wani ganewa sbd alokacin nutsuwarsa da kamewarsa take fin yawa,
Shiru yakeyi Yana nazari batareda buqatan hayaniya ko katse Masa nazariba shiyasa su Inayah dasun gansa irin yanayin suke yin tsit gidan duk da dama ba hayaniya ce dasuba gidansu.
*Qarfe goma da mintuna Ashirin ya fito harabar gidan sanye da black hoodie Thom Browne Riga da wando masu kauri ya nufa White jaguar motarsa ya bude ya shiga tareda tada motar ya nufi gate dama tuni Bosco yaga fitowarsa da sauri ya bude Masa gate ya fice.
Yana fitowa daga street din gidansa motar Abdulsamad Tasha hanasa tareda danno Masa full light.
Wani banzan numfashi ya saki tareda Dan juyar da kansa cikin takaici da baqin ciki ahankali yace”
Wannan matar tabbas zatasan waye AA MAJEED.
Babu tantama yasan itace a motar Abdulsamad din
Itama Babu tantama dama tasan yau komai dare saiya fito nemanta sbd dukkanin Susan amsar tambaya daddaya dake zukatansu kafin daurin auren gobe Dan kuwa amsoshin tambayar dake ran kowannensu itace future din yayansu da zaa daurawa aure gobe Dan haka a wahalce ta saci jiki ta fito bayan tasa Abdul yabar musu motarsa incase idan ciwonta zai tashi da dare su wuce asibiti ya samesu acan.
Batada lafiya sbd jininta yakai kololuwar hawa ko tsayuwa Bata iyawa sosai Amma bazata iya kwana ayauba batareda tayi magana da mahaifin Inayah ba,
Zuciyarta bugawa zatai da sake sake da fargaba harma da tashin hankali matuqar yau batai magana dashiba taji abinda takeson ji.
Da wani irin speed ya fizgi motarsa yabi ta gefen motarta ya wuce Yana Jin tsohon tabon baqin cikin daya dade Yana dannewa yana taso Masa.
Ribas tayi ta rufa Masa da gudu itama duk da qarfin haline kawai takeyi Dan sosai takejin kaman zuciyarta Zata fashe,
Tsohon famin baqin ciki da quncin da tarin Dana sanin gaske datake dannewa shekaru masu yawa ne suke birkito Mata tako Ina tanajin zuciyarta na azabar zafi da qunci.
Baisan tasan Lagos ba sosai Dan haka ya ringa ratsa manyan anguwannin dazai bacewa ganinta saidai sosai ta nace tana binsa idanuwanta ma tuni suka fara tsiyayar hawaye Dan kuwa hakan ya tabbatar Mata da tunaninta Gaskia ne akansa shine Wanda ta gudu tabarwa Jaririyarta AYSHATOUH.
A daidai gaban ma’aikatarsa ya faka motarsa tareda qin fitowa zuciyarsa na qara daukan wani irin zafi da bacin Rai da baqin ciki Mai zafin gaske.
Baya kaunar ganin fuskarta sbd ganin fuskarta na tunatar dashi kowace daqiqa na lokacinda ya rabu da gatansa da iyayensa harma da farin cikinsa akanta.
Jajir idanuwansa suka kada sosai sbd tsananin zafi da zuciyarsa ke dauka.
Bude motar tayi ya fito ya wuce zuwa ciki tabi bayansa da sauri itama hawayenta na tsananta gudu kaman yanda bugun zuciyarta da tashin hankalinta ke tsananta.
Cak suka tsaya a tsakiyar office dinsa koina tsit ba kowa sai securities din ma’aikatarsa.
Zubewa tayi agabansa tareda fashewa kawai da kuka Mai tsanani da taba zuciya sbd Batasan me Zata fara fadaba ko tambaya.
Kukanta sake zafafa ransa yakeyi Musamman wannan sautin kukan shine ta ringa Yi Masa a wancan lokacin batareda da duba girmewar datai masaba ta lalata rayuwar ‘dan matashin dake tsakiyar karatunsa cikin kwanciyar hankali da kulawar iyaye.
Wani mummunan ‘daci da qunci Mai nauyi ya hadiye ta wuyansa tareda juyowa ya kalleta da idanuwansa dasukai jajir Kai tsaye Yana danne fushinsa da nutsuwa yace”
Bansankiba ko wancan lokacin hakama bansakinba a yanzu,
Banda alaqa kowace iri dake bayan wadda zamu qulla a goben ta auren ‘yayanmu Kuma itama zan bar ‘danki ne kawai ya auri ‘yata sbd farin cikinta dakuma kaucewa abinda zai sameta idan akai fashin auren Dan haka ki amsa mun tambaya daya rak itama sbd kaucewa Mummunan Al’amari.
Kuka takeyi sosai sbd tasan Babu abinda daga ita harshi sukewa tsoro kaman alaqar ‘yayansu
Saidai kafin komai yabiyo baya na abinda ya faru a baya shine susan makomar alaqar dake Shirin qulluwa goben wadda tuna abinda zai biyo batama tashin hankali ne da wata babbar masifar.
Cikeda baqin ciki yakuma kallonta Jin batada niyar amsawa sai kukan datake Yi kaman zata shide.,
Zafi da quna ransa ke qarawa Dan haka ya juya yanajin kansa na sake yamutsewa da babban tashin hankalin da Inayah Zata iya Shiga akan wannan matar…
Yanada zafin zuciyan gaske Mai tsanani Amma tunda rayuwarsa ta sauya ya iya boyewa da dannewa Babu Mai gane yanayinsa duk kafiyarka Amma yau zafin zuciyan tasa ya gagara dannuwa a zafafe ya buga glass table din dake gefensa take ya tarwatse da qara Mai tsanani
Saida Hadizan ta firgita tana dagowa da jajayen idanuwanta dasuka rine take sbd tashin hankali Mai tsanani da kuka.
Miqewa tsaye tayi hawayenta har lokakacin basu tsayaba Dan ba tsayawar zasuyiba muryarta na rawa tace”
Ina AYSHATOUH???
Wani matsiyacin kallon baqin ciki da takaici yayi Mata yanajin duk duniya Babu Wanda yakai Hadiza sonkai
Ya dauke Kai Yana kokarin danne kansa daga zafin fushin dake taso Masa Kai tsaye yace”