GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 21-30

Idan kece kika haifi Abdulsamad menene alaqarki da ‘yar da kika Yar????

Gangaro Mata hawayen daci da danasani sukai muryarta a dashe tace”

‘yatace nice na haifeta da ita da Abdulsamad duk nice na haifesu Kuma mahaifinsu daya idan Inayah itace AYSHATOUH to uwarsu daya ubansu daya da Abdulsamad…….””da kuka ta qarasa zancen Dan kuwa babbar masifa ta diro ta sameta a zazzafan tabon ciwon qunci..

Idan Abdul Mai samu Inayah ba haukacewa zaiyi”” innalillahi wainnan ilaihrrjiun
Na shiga uku Ni Hadiza rayuwata tasake shiga wata babbar jarabawar Mai nauyi…

Mutuwar tsayece ta samu AA MAJEED Dan kuwa yayi fargabar Jin hakan Amma Bai yarda da zaiji tabbatar hakan daga bakintaba.

Qarasa rikidewa idanuwansa sukai jajir yanajin wani gumin zafi da babban tashin hankali na shigarsa.

Abinda yakeson tabbatarwa kenan daga bakinta dan shakku da fargaban daya shigesa na iya yiyiwar hakan Kuma ta tabbatar Masa Dan haka baida sauran buqata da ganinta kona second daya Dan a Karo na biyu ta sake wargaza rayuwar ‘yarsa.

Juyawa yayi Yanayinsa na ninkuwa ada sauti Mai ‘dacin gaske yace”

Zaki iya komawa ki sanar da danki dagani har ‘yata yanzu bamuda alaqa daku Auren anfasa.

Juyawa yayi zai fice Dan hankalinsa gabaki daya yagama yamutsewa qarshe kaman kansa zai buga
Inayah yakejin tashin hankalin yanda Zata karba kaddarar rashin auren Abdulsamad sbd bazai taba fada Mata dalilinba Dan kuwa bazai taba barin Hadiza ta kusantar Masa ‘ya ba.

Da saurin Hadiza Tasha gabansa tana rokonsa cikeda tarin nadama tace”

Dan Allah kafadamun idan Inayah ce Ayshatouh na,
Har abada nasan bazan taba samun yafita a zuciyarkaba Amma Dan Allah kada ka hanani Ayshatouh Inayah,
Wlh nayi Dana sani nayi nadama…..

Sauraronta tafasashi sukeyi tako Ina Dan shi kansa komai ya kunce Masa a yanzu.

Wucewa yayi Yana daga wayarsa zuciyarsa a quntace ya saka kirana Mr Al-amen Yana dauka Kai tsaye yace”

Ai Mana booking tickets da komai na tafiya nida familyna gobe kafin 12 zamu bar qasar….

MAMUH

MARRIAGE/LOVE

AYSHATOUH INAYAH AA MAJEED

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107
[10/26, 8:45 PM] Sweet sis: 28
Arewabooks@Mamuhgee
Tashin hankali Hadiza tashiga Jin abinda ya fada a firgice Tasha gabansa tana rokonsa cikin mummunan hali na kuka tana rokon ya hadata da ‘yarta Ayshatouh Inayah.

Numfashi ya sauke a hankali tareda ajiyar zuciya Mai dumi kafin ya Dan dago ya kalleta kadan cikin nutsuwa kaman Wanda zuciyarsa ba tsananin quna takeba da ‘daci takeba yace”

Babban taimakon da zakiyiwa kanki da Abdulsamad shine ki cirewa ranki da kanki tunanin sanin mahaifin Inayah bare ita Inayah din,

Inayah ‘yatace Kuma Babu Wanda zaizo Rana tsaka yacemun shine ya haifeta,
Bansankiba Baku nada alaqan komai dake..

Ki nema yarki a Inda kikasan son zuciya yasa kin barta.

Zafi maganganunsa suka farai Mata sbd duk yanda tayi aikin son zuciya abaya Inayah dai yartace Kuma tayi danasani daga ranar data gudu ta barta.

Wlh bazata yardaba taga yarta sannan ya dauketa su bar qasar tasan bazata Kuma ganintaba har abada Dan haka cikin rashin tunani da tauna zancen abinda yafada matan tace”

Har abada saidai ka Kira kanka matsayin mariqinta uban daya raineta Amma bazaka taba sauyata daga nice wadda na dauka cikintaba na haifeta.

Bai tsaya saurarentaba ya fito Kai tsaye yashiga motarsa Yana cewa security a rufe Masa koina.

Cikin zafi ga figi motarsa da matsiyacin speed yabar gurin batareda yajira ganin fitowartaba.

Ikon Allah ne kawai da nutsuwa dayayita kokarin sakawa kansa sbd kada su Inayah su gano halinda yake ciki yakaisa gida lfy.

Yana parking ya fito ya nufi kofar dazata kaisa palonsa na farko direct batareda yabi kofar dazata bi dashi ta palon su Inayah ba kafin ya Isa nasa palon.

Yana Shiga palonsa Kai tsaye hanyar bedroom dinsa ya nufa ya shige tareda Zama kan luxury italian sofa dake dakin ya rintse idanuwansa dasukai jajir.

Ajiyar zuciya yafara jerowa da numfashi Mai zafi yanajin damuwa da tashin hankali Mai tsananin wannan auren da Allah yasa baa dauraba da tako Ina masifun da tashin hankalin bullowa zaiyi,

To Amma babban tashin hankalin da damuwar shine ta yanda Inayah Zata karbi fashin aurenta akaro kusan na hudu.
Tayaya zai iya taro matsalar da Zata iya samunta?
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun.

Miqewa yayi ya nufa toilet ya sakarwa kansa daya dauki tsananin zafi ruwa yanajin zafin kan na tsananta.

Da ruwan dumi yayi wanka ya fito ya saka blue pyjamas sai sanyayyan Chanel na jiki ya kashe wayarsa tareda jefarwa gefe ya hau gado zauna Dan yasan yau koda qyaftawar Ido bazai rintsaba sbd fitina da tashin hankalin dayake jiransu da safe.

Umma Hadiza ma cikin masifaffen tashin hankali da tsoron AA MAJEED yabar qasar da inayah ta iso gida jikinta Babu Inda baya kakkarwa ta silale tashige dakinta batareda kowa yasan fitarta da dawowartaba ta rufe daki tareda zubewa qasa tafara kuka Mara sauti tana cewa”

Ya Allah kagani rashin mafita da madafa da Sharrin shedan ya hanani tawakkali na gudu nabar ‘yata badan bana tsananin sontaba ya Allah nayi shekaru cikin qunci da damuwa da tawakkali ya Allah kada kabari wannan bawa naka ya tafi da ‘yata wata qasarda bazan Kuma jinsu ko ganinsu.,,ya Allah ka duba maraicina ka hadani da ‘yata,
Allah ka kawo Mana sassaucin wannan masifar data kunne Kai da tashin hankalin dazai biyo goben sanadin fashin auren yaran Nan.

Kuka takeyi sosai tana rokon Allah sassauci da mafita.

****Daga AA MAJEED har umma Hadizan Babu Wanda ya rintsa yanda sukaga Rana haka sukaga dare da safiya.

A gidan A MAJEED da zallar farin ciki iyalan gidan suka tashi Dan ko su Anty Hafsat duk a gidan takwana da yaranta gasu Safnah da Neesah dasu Daman tuni suka tare sai Yan uwan umma yaganah guda biyu dasuka zo bikin Dan tayata Murna dakuma samun abun arziki.

Dr farhat dasu Mimi ma tunda safe suka iso gidan kaman dasu aka kwana.

Kowa farin cikinsa bayyananne ne sbd duka aurarrakinta da ake fasawa Babu Wanda yazo ranar Daurin auren  sai wannan yau gashi Allah yayi anzo daurin auren a wanni kadan ne suka rage tazamata cikakkiyar matar Heart dinta Abdulsamad salees halak malak.

Cikin kayan baccin data kwana dasu Riga sa wando masu santsi tafito da hula akanta fuskarta da dukkanin fatar jikinta sunyi fresh sai sheqin kyau da gyara sukeyi gashi yanayin data fito din kaman wata qaramar yarinya.

Kai tsaye dining ta nufa tana cewa”

Yunwa nakeji zubbi kawon tea nafara sha.

Tea da doughnuts masu laushi guda uku zubbi takawo Mata tana cewa”

Mint tea din Sir is ready
Zaa shirya Masa ne a dining kokuwa?

Tana Shan tea dinta tace”

No ki shirya zan Kai Masa palonsa yau da mutane a gidan bazai shigo ciki ba,
Harda dessert din kin kammala hada Masa?

Yes Ma.

Ok kije ki hado zan Kai Masa.

Ok Ma.
Juyawa tayi ta koma kitchen din Dan hadowa takawo Mata.

Wayarta ta daga tana kokarin Nemo numbern Heart sai gashi kiransa yashigo wayarta da farin ciki bayyane kan fuskar ta dauka da Yar muryarta Mai shagwaba tace”

Good morning Heart.

Wani sanyin farin cikine yakuma cika ransa sbd ranar yau din daqyar yaga garin ya waye
Cikin wani irin girmammen farin ciki yake Mai nutsuwa,
Allah yau yacika Masa burinsa na mallakar Inayah amatsayin matarsa dazata Zama uwar yayansa.
Ji yayima farin cikin yasaka jikinsa sanyi Musamman data Kuma kiran sunansa da HEART.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button