INAYAH 21-30
Idan kunje komai na hannun Ahmed zai damqa miki komai
Zanzo daga baya.
Tsit suka Dan Yi da mamaki suna kallonsa duk da basu gane komaiba akan Inda zasuje sai jikin umma yagana yayi sanyi taji zuciyarta na Neman shiga wasi wasi.
Inayah ma jikin nata taji yafara sanyi take ta kalli abbin da rauni Amma batace komaiba.
Juyawa yayi yana kokarin Isa motarsa aka bude gate motar CM tashigo ko qarasa rufe gate baayiba motar Dr Abdul ta Sako Kai itama.
Umma Hadiza ce aciki Kuma tanayin parking idonta ya sauka kan Ayshatunta take taji wasu hawayen da tsananin kaunar yarta suna finciko Mata tako Ina,
Kaunace Mai tsananin gaske wadda uwa kewa ‘danta Bayan tacire ran samu ko ganinsa har abada.
Hawaye takeyi sosai tana kallon Inayah din tanajin tamkar taje ta rungumota tayita kissing dinta tana fada Mata yanda take kaunarta da qaddarar datashiga akan cikinta.
Wani zafi da tirnikin bacin Rai da tashin hankali ne ya taso Mata ganin suna kokarin shiga mota tasan wlh qasar zasu Bari suna fita gidan yau bazata Kuma ganin ‘yartaba Wanda haukar da Allah ya taqaita Mata lokacinda tayi danasani tashiga Neman yarta to haukar zatayi yanzu matuqar takuma rasa Ayshatouh.
Hankali tashe ta fito motar da gudu ta nufosu Inayah tana Kiran sunanta.
Dakatawa umma yaganah tafarayi tana kallon Hadizan kafin Inayah itama ta dakata suna kallonta cikeda mamaki.
Inayah kuma umman na isowa gabansu ta kalleta da kyau taga yanda idanuwanta da fuskarta sukai jajir tashin hankali bayyane kan fuskar umma Hadizan
Wani mummunan bugawa zuciyar Inayah tayi har Saida ta dafa Neesah dake gefenta.
Muryarta na rawa itada umma yagana ma data shiga zullumin abinda zasuji Dan dagani ba lafiyaba murya a hautsine sukace”
Umma Hadiza….
Kasa tambayar abinda ke faruwa sukai sbd tsoron abinda zasuji.
Kai tsaye Inayah taji wani jiri na Neman dibanta kafin tayi kokarin dafe kanta taji muryar Umma Hadiza a hargitse tana cewa”
Dan Allah kadaku tafi wlh qasar zaku Bari kuna fita,
Aurenki Inayah da Abdul bazai fas….
Inayah Bata gama jiba qafafuwanta suka yanke zuciyarta na neman bugawa ta tabbatar fasa aurenta yanzuma akai ko ake neman Yi.
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun”
Mezan gani hakan Ni yaganah,
Innalillahi, innalillahi.
Hawayene ke kokarin gangarowa Inayah Amma tashin hankali yaqi Bari umma yaganah dasu Neesah da duk suka shiga tension din suka fara kokarin kamata sukoma ciki da ita
Umma Hadiza ma cikin tsananin tashin hankali da dimuwa ta ringa maimaita ba fasawa nace anyiba Dan Allah Inayah karki shiga wani hali,
Babu fashi aurenki da Abdulsamad,
Zaa daura zamu tafi dake adamwa zan Baki duk wata soyayyar uwa da Baki samuba,
Inayah, Inayah.
Sam Inayah Bata gane kalma daya da umman Abdul din take fada sbd zuciyarta bugawa takeyi sosai da tashin hankali da attack data samu take Dan hakan komai Bata ganewa sai rawa da jikinta keyi.
Su umma yaganah kuwa take ta fara tunanin daqyar idan umman Abdul nada lafiyar qwaqwalwa sbd duk tabi ta rude da Kiran Inayah da suna biyu.
Abbi da hankalinsa nakan CM dayazo daukansa su wuce daurin auren tare Bai lurada Hadiza ce tashigo a motar Dr Abdul ba Saida yaji salatin da umma yaganah ke qwalawa da qarfi hankalinsu duk yakoma Kai cikeda mamaki da zafin zuciya Mai qarfi ya kalli umma Hadiza Yana kallon ‘yarsa dake Neman siqewa cikin tashin hankali numfashinta na neman gagararta.
Cikin bacin Rai Mai qarfi ya qaraso gurin tareda kallon umma yaganah yace”
Ku kaita ciki Dr farhat ta dubata da sauri.
Kan umma Hadiza dake kokarin binsu hankali tashe ya maida kallonsa idanuwansa na Neman sauyawa yace”
Ni Zaki sama da duk abinda kikazo dashi,
Me kika fadawa Inayah yasata cikin wannan halin?
Ganin su umma yaganah Basu qarasa shigewa da Inayah ba yasashi juyawa tabiyo bayansa tana cewa”
Dan girman Allah da manzansa kaban ‘yata,
Ka sanar da ita nice mahaifiyarta,
Dan Allah kada ka cutatar da uwar dake cikin qunci tsawon shekaru ta hanyar Hana Mata ‘yarta….
Babban palonsa suka shigo ta tsaya gabansa idanuwanta na zubda hawaye sosai cikin mawuyacin hali tafara rokonsa akan ya sanar da Inayah itace mahaifiyarta.
Mamakine ya Kama CM dake tareda A A MAJEED din tako Ina.
Idan ya fahimta Kuma yagane wannan matar Inayah take Kiran ‘yartace.
Itace mahaifiyar Inayah?
MAJEED da idanuwansa ke bayyanarda tsananin bacin ransa da fushinsa ya kalla yasan yau kam ransa yakai kololuwar baci tunda ya bayyanarda fushinsa.
Bai iya cewa umma Hadiza komaiba sbd baimasan mezai fada mataba,
Da alama tanada ciwon Kai Dan hakan tako Ina lalata Masa Al’amura zatai.
Cikin kosawa da ganinta gabansa ya bude Baki a gundure yace.
“Me kika fadawa Inayah da har kika data cikin wancan halin datake ciki?
Idan kin sanar da itane matsayinki a gunta kinyi babban kuskuren da….
Cikin sauri da bayyanarda gaskiyarta ta katsesa da cewa,
“Banfada Mata komaiba
Maganar aurenta da Abdul kawai nake fada musu.
Wani irin rufe Ido yayi ya bude cikin baqin ciki da takaici yace”
Kinsan shima hakan matsalar da Zaki haifar mata?
Kinsan halinda Zata iya Shiga akan hakan?
Meysa zakiyi kutse acikin Al’amarin da bakisan Yaya yake tafiyaba?
Numfashi Mai zafi ya sauke tareda fitarda ajiyar zuciya Dan bazai iya wannan tashin hankalinba yanzu.
dauke kallonsa daga kanta yayi a natse yace”
Idan harkina kaunarta a matsayin uwa kaman yanda kika fada kibarta taci gaba da rayuwarta batareda kin dandana Mata ‘dacin rashin karbuwa daga uwar data haifeta kokuma dacin hanyar da aka samar da ita.
Maganarsa ta qarshe tayi mummunan girgiza,
Kenan shima daukan yake ta hanyar banza ta samu Inayah tunda yaga ta gudu tabarta?
Wasu hawayen baqin ciki Mai tsanani ne suka gangaro Mata ta dago da jajayen idanuwanta ta kallesa zuciyarta na quna da bacin Rai tace”
Na tsaya rokonkane ka bayyanarwa ‘yata nice na haifeta sbd nabaka haqqinka amatsayin Wanda ya reneta da Amana ba cutatarwa bawai Dan narasa damata ta uwa agaretaba.
Kanason nuna dukiya ka rabani da ‘yata rabuwar har abada Amma hakan bazai taba karbuwaba gurina.
Wlh bazan yardaba Sharia Zata karbamun ‘yata tadawo hannuna.
Mamaki tafara basa ta yanda take iya furta kalamai batareda taji kunyar kantaba na abinda ta aikatawa ‘yar a baya harma dashi.
Idan tana maganar qarfin ikone
To zai nuna Mata qarfin iko akan Inayah.
Cikin sautin bayyanarda gajiya da lamarinta yace”
Wannan shine Karo na qarshe da Zaki iya zuwa gidana ko kusantar daya daga cikin iyalin gidana,
Zaki iya tafiya.
Kallon baqin ciki da damuwa lokaci daya take Masa tace”
Zantafi Amma kasani nice uwa dana Rena cikin Inayah nakuma haifeta har abada babu wani ko sunan dazai sauya mun matsayi akanta,
Nice nafi kowa cikakkiyar dama da iko akanta,
Kaikuma damarka da ikonka akan Inayah ya tsayane a matsayin mariki Kuma zai tsaya ahakan ne har abada.
‘ya mace ce duk iko da isar da zaka nuna akanta saitabarka har abada sbd aure zatayi take gidan wani Kuma a qarqashinsa Dan hakan idan kafi qarfin hukuma bazakafi na shari’a ba,
Sharia Zata dauke inayah daga hannunka tabani ‘yata,
Idanma shariar kafita ikone zamuga wannan sbd duk ikonka akanta bazaka taba aurentaba Dan kuwa aurene kawai zai riqe ‘ya mace aguri wani ikon ya kasa dauketa dauketa
Kuma da yardar Allah Inayah bazata rufa wata a hannunkaba saina karba Yana Koda ta hanyar kawo Mata wani mijin auren ne.