INAYAH 21-30
Rintse idanuwansa yayi cikin takaici da baqin cikin ganin Hadiza agabansa.
Duk shekarun mace hankalinta da tunaninta na banza ne lokuta da dama,
Sam kansu toshewa yakeyi hat basusan me suke fadaba.
Idan Hadiza na tunani haryanzu akan shari’a Zata karba Mata Inayah a hannunsa to zai sakata a spot dinda ko shariar bazata iya dauke inayah daga hannunsaba a gurin.
Bai iya kallontaba sbd siqewa kai tsaye yace.
Kije Ina jiran shariar.
A fusace da baqin ciki ta juya tana hawaye sbd ba haka tasoba son tayi ya amince ya hadata da ‘yarta idan Tai Masa barazana da sharia sbd tasan bazai taba son duniya tasan Inayah ba ‘yarsa bace.
CM da kansa yayi matuqar daurewa da daukan zafi kusan yagama gano kan zancen shine Inayah dai ba Amininsa neba ya haifeta Kuma wannan matar itace mahaifiyar tata.
Baisan ya zancen yafaruba Amma tabbas a wannan tsukakken yanayin yasan akwai matsala Babba matuqar wannan Al’amarin zai shafa daurin auren yau.
Agogo A MAJEED ya kalla yaga Sha daya da rabi harta fara wucwa.
Bai iya cewa Amininsa komaiba yace su tafi kawai.
Shima CM tunda ba qaramin yaro bane yasan yanzu ba lokacinda zai tsaya tambayar MAJEED din meyake faruwa bane saidai idan an natsa zafi da dacin ransa ya sauka.
Suna fitowa Kai tsaye yabawa Bosco odar kada akuma barin motar Abdulsamad tashigo gidansa matuqar bashineba aciki.
Kai tsaye babban masallacin dake kusada gidan iyayen CM suka nufa Inda anan ne zaai daurin auren dama.
Mutane ne tako Ina sun cika anguwar ga securities da jamiaan tsaro kusan tako Ina sbd akwai manyan mutanensu dasun iso tuni Dan mintuna goma Sha takwas suka rage ga daurin auren.
Wani irin zafi da ‘dacin zuciya yakeji ganin tarin jama’ar dasukazo Dan sheda daurin auren ga dangin Abdul ma da dama sun iso shi kansa Abdulsamad din ya iso gurin cikin shigar alfarma ta angon dake cikin tsananin farin ciki.
Qarfe goma Sha biyu daidai aka nutsu aka fara daurin auren Wanda CM ne da kansa yayi wakilcin Amarya mahaifinsa Alhaji babbah yayi wakilcin Ango sauyin daya faru tsananinsu take agurin.
Kafin iyayen Abdulsamad su Ankara sukaji ana shelar an daura auren ABDULMAJEED ABDALLAH da INAYAH A MAJEED.
MAMUH
AFADA ALKHAIRI KO AYI SHIRU/#MASU YI DANI A BAYANA.
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
Mamuhgee
GURBIN IDO
Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902
MTN card????
09134848107
[10/26, 8:45 PM] Sweet sis: 30
Arewabooks@Mamuhgee
Kusan da yawan jama’ar gurin Basu fahimci wane ABDULMAJEED din ake nufiba sai Amin kawai suke amsawa da ita suna qarawa da adduar zaman lafiya da albarkar aure sbd sunan Abdul din da aka ambata cikin sunan basu wani bambamceba tunda dai kowa yasan sunan Ango Abdul.
Iyayen Abdulsamad Wakilansa sune suka saki Ido da Baki cikin zallar mamaki da firgici Jin andaura da wani Abdul din daba nasuba Dan Babu Wanda ya tsaya kawo wani rubabben tunanin AA MAJEED mahaifinta ake nufi.
Shi kansa Abdulsamad kasa tantance meyake faruwa yayi saiyafara tunanin ko matsalar fadan sunan aka samu Mai fadar be kila ya rude ya fada sunan mahaifin Inayah a matsayin uba Kuma yadawo ya fada amatsayin Miki Wanda aka daura auren dashi.
Jin zuciyarsa dai takasa yarda sai tsinkewa data farayi yasashi kokarin baro Inda yake Dan zuwa gaban wakilan daurin auren yaji wane rudadden ne Mai sanarwar dazai saka kansa kuncewa da zancensa.
Kusan dai jama’a tsakani da Allah duk Basu ganeba idan ba wainda suke Yan uwan Abdulsamad ba sbd suka Sarai sunji ba sunan angonsu aka fadaba
Sauran jama’a da Basu ganeba tunda ba hankali mutane ke badawa sosaiba gurin daurin aure sai an daura zu amsa da Amin da fatan Alkhairi su tafi Dan haka aka ringa gaggaisawa ana Allah sanya Alkhairi ana neman fara watsewa.
Ciki mamaki Mai tsanani da kokarin danne bacin Rai yayan Marigayi salisu ya kalli CM da Alhaji babbah kafin ya maida kallonsa kan AA yace”
Alhaji MAJEED mufa bamu gane abinda yake faruwaba anan,
Auren da zaa daura biyu ne Daman kokuwa dai Wanda zamu daura dinne aka daura da wani ‘dan ba namuba?
Dan idan naji daidai sunan yarinyar dai shine wadda zaa daurawa danmu da ita.
Duk Inda damuwa da ‘dacin Rai Dana zuciya suke sune a dabaibaye da A MAJEED,
Bai taba samun kansa a yanayi Mai ‘daci da qaqa nikayiba irin wannan Rana,
Ko a wancan lokacin daya hadu da qaddarar samun Inayah baishiga damuwa da quncin dayake cikiba yanzu.
Me zaiyi da auren ‘yarsa ta kansa?
Wace mummunar masifa Hadiza ta sakasa daya qare qarshe a auren Inayah ‘yarsa??
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun,
Yau shima yahadu da qaddarar Sharrin shedan Dana zafi da yanke hukunci cikin fushi.
Duniyama idan taji shine ya aura ‘yarsa zai anyi Allah wadai da tunaninsa.
Gashi garin yanke hukunci kada Hadiza ta ra’bi Inayah har Inayah tasan bashine mahaifinta ba yaje cikin fushi da bacin Rai yayi abinda ba iya Inayah kadaiba da bayason ta taba sanin bashine ya haifetaba duniyama kowa zai sani yanzu Wanda harga Allah yaso riqeta amatsayin ya har abada batareda kowane Dan Adam yasan bashine ya haifetaba sbd daga lokacinda mahaifiyarsa datafi kowa saninsa da tarbiyarsa ta tuhumesa tareda yarda da zai iya aikata Zina harma ya Haihu a hanyar Zina yasaka a ransa ya karbi Inayah amatsayin ‘ya dabazai taba barin wani yasan bashine ya haifetaba ciki kuwa harda mahaifiyarsa saigashi Rana tsaka Hadiza ta sakasa a mummunan tarko.
Hadiza itace masifar rayuwarsa yau ya tabbatarda hakan sbd akaro na biyu takuma sakasa masifar da kusan tafi ta baya yaqare da rataya igiyoyinsa na aure a wuyan ‘yarsa baisan wane mummunan Al’amarin Zata Kuma kawo masaba a gaba Dan yasa zaifi wainnan zauta Kai da qwaqwalwa.
CM ne yayi saurin kallonsu Alhaji buhari ganin ransu yafara baci sosai sunason Jin bayanin abinda yake faruwa Dan haryanzu sunkasa yarda da auren matar ‘dansu aka daura da wani sbd har lokacin Babu Wanda yakawo da AA MAJEED aka daura auren tunda ba abune Mai yiyuwaba uba ya aura ‘yarsa Dan hakan kaf gurin Babu Wanda yakawo ABDULMAJEED mahaifinta ake nufi suma su CM da Alhaji babbah sunqi barinma agane wane ABDULMAJEED Dadi da qari kusan duniya da AA MAJEED tasansa bada cikakken sunansaba ABDULMAJEED ABDALLAH.
Cikin qarfin hali Abbin yataso Yana sallama da mutanensa dake wucewa suna Masa Allah ya sanyawa auren ‘yarsa albarka Yana amsawa da amin.
Kaurewa da gurin yayi da jiniyar motocin ‘yan sanda da civil defense ga yawan jama’a kowa nata kokarin miqa barkarsa ya wuce shiya taimakawa su CM gurin Jan su Alhaji buhari zuwa cikin gida palon Alhaji babbah Wanda shine da kansa ya iya fara tankwafarsu sbd fadan tozarci dasukagani qarara dasuka fara yi.
Alhaji buhari ne mai iya dan danne tsananin bacin ran dasuke ciki su Alhaji kabiru ‘yan Nan Hadiza kuwa kasa dannewa sukai suka fara zuba masifar tashin hankali Dan duk Inda ake wulaqantawa an wulaqantasu ankuma tozartasu sun debo jiki tun daga adamawa sunzo Lagos daurin aure ace suna zaune suna kallo kaman wasu gumaka andaurawa amaryar aure da wani koma Dan uban waye ai Basu cancanta wannan tozarcinba.
Abdulsamad a rikice cikin tashin hankalin daya zaburo Masa tako Ina ya ringa kutsa jama’a Yana neman iyayensa maza dasune wakilan Amma Bai gansuba Dan haka ba Shiri ya zare hular kansa Yana Jin akwai gagarumar matsala Mai tsananin girman gaske kuwa.