INAYAH 21-30
Saidatai wanka tayi sallah taci abinci kafin ta Kira anty Hafsat din wadda tuni takira umma yaganah ta sanar mata ‘dan Yar uwarta yaga Inayah din ya rikice musu tun jiya.
Umma yaganah Bata wani dauki zancen da mahimmanci ba saidai tace musu ya nema Inayah din da kansa idan sun daidaita ai shikenan haka akeso.
Kasancewar Inayah din batada wani saurayi ko daya yasa bata wani damuba tabawa anty Hafsat damar gabatar dashi din.
Ranar farko daya fara zuwa gidan Abbinta bayanan yayi tafiya zuwa Kano da CM Dan haka basu wani samu damuwaba ko fargaba daga ita har umma yaganah.
Faruk Ismail kyakkyawa ne ba laifi Kuma Dan boko da gayun gaske,
Ya waye sbd Yana ganin yayi karatu a Malaysia saidai Kuma daya Gama sanin cikakkiyar waye Inayah da mahaifinta sai ya Dan sassauto daga ‘dagawar dayake Yi na shi baa Nigeria yayi karatu ba,
Shi karatun kawai yaje yayo yadawo ita kuwa acan taqarasa girma acan tayi karatu.
Ranar Ashe Bai yiwa Inayahn kallon tsaf ba sai yau din daya Gama kallonta a natse
Yaga irin kyan siffa data fuska dama sanyin halaye so innocent take yaji ya mutu akanta.
Cikin sanyi da sakewa irinta wayayyu take komai uwa uba ga shagwaba data Zama kamar halinta sbd tasowarta a shagwaben Dan haka tasaba komai Kai tsaye da gaskiyarta take yinsa.
At first Bata tsaya ta karanta Faruk ba sai daga baya daya Gama karantar shikam ya dauki duk wata hanyar mallakar zuciyarta,
Tsananin kulawa da kauna Mai girma yake nuna Mata tareda wata irin soyayya.
Shikansa yayi mamakin daya iya soyayya lokaci kankani sbd Bai taba soyayyar ba.
Halayensa na kulawa da zallar soyayya yasa tuni itama tafada soyayyarsa Mai qarfi taqarasa mantawa da Zaid gabaki daya da babinsa.
Soyayya Mai qarfin gaske sukewa junansa cikin watanni kadan
Ga Dr Abdul dayake fama da tsananin Sonta Amma haka yabawa kansa hakuri ya danne tunda anriga ansha gabansa.
Abbinta Bai damuba sbd tako Ina ya bincika iyaye da familynsu faruk din basuda illa Kuma tunda tagama karatu yanzu baida damuwa da aurenta koba komai auren ne next dama Dan haka yabawa faruk din Daman neman Inayah din.
MAMUH
LOVE/ROMANCE
MAJEED/INAYAH/MARRIAGE
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902
MTN card????
09134848107
[10/21, 12:15 PM] +234 808 711 8630: 22
Arewabooks@Mamuhgee
Lokaci ya tafi sosai dan tuni maganar aurenta da Faruk ta Gama kammaluwa aka saka lokacin biki hankalinta Dana faruk din ya kwanta sbd wata irin soyayya ce sukeyi Mai zurfi da qulafucin juna.
Shi kansa Abbin hankalinsa yafi kwantawa sosai da aurenta da Faruk akan can baya da Zaid.
Ba maganar komawarsu Australia saidai idan sunje hutu saikuma Abbin da shikam zai ringa zuwa akai akai sbd huldodinsa wasu dasuke can.
Daga Nan gidansu har familynsu Anty Hafsat da dangin CM Babu Wanda baya cikin farin ciki da murnar wannan biki sai Mimi wadda baqin cikin datake ciki ya hanata sukuni sbd bazata iya kallo Hafsat tasamu shiga jikin zuriar AA MAJEED ba fiyeda ita Dan kuwa ko yanzu akan wannan auren ba qananan arziki taketa samuba daga AA MAJEED harma da umma yaganah datake Jin Hafsat tagama Mata komai tunda tayi sanadinda Inayarsu tasamu kamilallan miji dayake sonta sosai.
Safnah kuwa Bata wani damu da damuwar da Mimin take cikiba sbd tadauka kishi ne irin Wanda Allah ya halitta a zuciyar Mata shine takeyiwa Anty Hafsat na ganin tasamu shiga a Inda itace taso tasamu shigar.
Neesah kam Dole da qarfi da yaji tazo Nigeria tareda momy Dan haka Murna a gidan takuma Zama sabuwa.
Ta bangaren Dr Abdul son Inayah Bai taba raguwa acikin ransaba saima Jin dayake kaman zuciyarsa bazata iya daukaba ganin Inayah ta aura wani tabarsa,
Amma iliminsa na addini Dana bokon daya kedashi Bai barsa ya qullata komaiba saima nesa nesa daya Dan farayi da Inayah sbd zuciyarsa bazata iya cigaba da daukan kishinta Mai tsananin gaske dayake ji Amma Inayah Bata iya nesa dashi sbd yariga yazama tamkar wani babban bangare na rayuwarta a Nigeria,
Tayi sabo da shaquwa Mai tsananin gaske dashi da har kaunarsa ta ginu a ranta amatsayin aboki Kuma Dan uwan Dan haka idan yaqi kiranta itace da kanta take kiransa.
*Bikinta Saura sati uku Dr Abdul yabar Lagos yakoma Adamawa
Farko hankalin Inayah din yatashi sosai da barinsa Amma hidima da shaanin biki yaqi barinta maida hankali sosai kan tafiyar tasa
Sai kawai tabarshi akan idan angama bikin Zatai magana dashi.
Anfara gyaran Amarya INAYAH tako Ina,
Umma yaganah baji ba gani ta dauko masu gyara daga maiduguri ana gyaran Inayah ta ciki da waje.
Anty Hafsat ma ba Zama kusan kullum saitaxo gidan da nata kayan gyaran.
Neesah dai kam tana gidan sbd suna sauka Abuja can gidan iyayen momy kwana biyu kawai tayi ta biyo jirgi zuwa Lagos Dan haka duk sauran shirye shiryensu tare suke yinsu
Ko Safnah ma kusan kullum gidan take wuni.
Umma yaganah taje maiduguri kusan kwananta biyar acan daqyar daqyar ta iya samun wasu daga cikin ‘yan uwanta Amma sauran kam duk sun rasu wasu Kuma ba’a San Inda sukeba kaman ita.
Wainda ta sama cikin Yan uwan nata bama irin Yan uwan kusa bane
Kawun malam mijinta ne da iyalansa ta samu sunkoma kauyensu da aka watse sai wasu daga cikin amininan iyayenta saikuma kishiyar mahaifiyarta da itama ta tsufa sosai.
Tayi musu Sha Tara ta arziki tabaro tadawo maiduguri tasake kwana daya tabi jirgi Takoma Lagos.
*A daren da zaa saka amarya lalle saqon wani mugun labarin ya isowa umma yaganah ta hanyar Mimi.
Rigimace ta barke a gidansu faruk da iyayensa da shi harma da mahaifin dadynsa..
Wannan wata babbar maganace data girgiza umma da ita kanta Inayah sbd basu taba tsintar wannan mumunar kalmarba sai ranar.
AA MAJEED ya Haifa Inayah bada aureba,
‘yar gaba da fatiha ce…
Tashin hankali Mai girman gaske umma yaganah da Neesah suka Shiga sbd kalmar tayi Muni da yawa.
Inayah kuwa zuciyarta ce taji tana harbawa da sauri da qarfi
Wani irin zufane masu dumi suka ringa tsatsafo Mata.
Dafa kujera tayi ahankali ta zauna tana Jan numfashi da sauri sauri.
Ruwa zubbi taje da gudu takawo tabawa Neesah dake Kiran sunanta da Dan qarfi tana cewa”
Inayah karki daga hankalinki please
Wannan labari ne fa kawai aka kawo.
Karban ruwan tayi takai bakinta da Dan sauri ta kwankwada ta miqawa zubbi cup din tana miqewa tsaye tace”
Faruk yasan wannan zancen shirme ne,
Ina ruwansu data yanda mahaifina ya haifeni,
Idanma Ni shigeyarce an haramta auren shegu ne?
Tunda Ina tareda mahaifi ai banajin zan karba suna kokuma bin layin shegu..
Umma yaganah ma cikin damuwa da tashin hankalin datake dannewa tace”
Menene Kuma na wannan zancen ma Kuma yanzu?
Yarinya da ubanta Dan Allah bamason janye janye da wulaqanci,
Waye yafara kawo wannan zancen?
Wane Mara hankalin ne zai kawo Mana fitina muna shaaninmu cikin Jin Dadi da farin ciki?
Kuka sosai anty Hafsat keyi agaban Umma yaganah din sbd batama San Mimi tafara kawo musu zancen basu yardaba sai yanzu datazo da kanta sbd Al’amarin ya tsananta acan familyn Anata rigima da tashin hankali,
Mahaifiyar faruk da mahaifiyar dadynsa sunyi rantsuwar bazaai aurenba Dan faruk bazai aura Inayah ba sai mahaifinta ya sanar dasu Gaskiar wannan zancen da aka kawo musu.