GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 21-30

Dadyn Faruk yasan saidai afasa auren har abada Amma AA MAJEED bazai zauna yiwa kowa bayaniba Dan a aura ‘yarsa
Kai tsayema za’a samu babbar matsala dashi Dan kuwa suna shegenta Masa ‘ya ne Kai tsaye da kalamansu.

Shi kansa Alhaji baba kakan faruk din Bai wani goyi bayan faruk da mahaifinsaba sbd ganin kaman harda kwadayin suna da arzikin AA MAJEED sukeson rufe Ido su hada zuria dashi koda da gaske Inayah din ‘yar gaban fatiha ce.

Dayake maganar a tsakanin mata tafara har lokacin Abbi baisan abinda yake faruwaba dagashi har CM Dan haka su sun Riga sun Gama rabawa jama’arsu katikan daurin aure da invitations na special lunch da zaai bayan daurin auren sbd abokanan huldodinsu Christians da turawan dake Nan tunda su ba daurin aure suke zuwaba.

Wasa Wasa saiga zance dai yazama Babba Dan kuwa Dadyn Faruk yasamu CM da zancen har gida sbd bazai iya tunkarar AA MAJEED ba,
Ko daya girma MAJEED sosai yanajin kunya da nauyinsa yaje Masa da maganar Dan haka yasamu CM da zancen.

Sosai cm ya girgiza da wannan mugun sakon, dan haka baiyi saurin isarda sakonba saiya samu Alhaji baba dasu hajiyar yayi kokarin fahimtar dasu illar abinda zaayi din Dan tamkar tozarcine Kuma wulaqanci ga AA MAJEED da ‘yarsa ace zaa tambayesa yanda ya Haifa yarsa.

Sam kasa fahimtar juna sukai dasu dashi Dan haka baida wani zabi sai sanarda AA MAJEED halinda ake ciki.

Shiru yayi bayan yagama sauraron bayanin CM cikin nutsuwa.

Bai bayyanarda bacin Rai ko fushiba saidai kam idanuwansa wannan karon sun bayyanarda tsananin ‘dacin daya Kama zuciyarsa.

Ba’a taba cin fuska ko cin mutuncin Martabarsaba sai wannan karon,

Ko alokacinda yake talakansa baida girma ko qima a idon mutane tunda shi talakane baa ci zarafin mutuncinsa kaman wannan lokacinba.

Idanuwansa ya Dan juyo ahankali ya dauki wayarsa dake gefensa ajiye ya Nemo numbern umma yaganah ya saka Kira.

Zaune suke gabaki daya gidan yanzu Murna na Neman komawa ciki tunda wannan muguwar magana ta bayyana.

Tashin hankalin da Faruk yake cikine ya tabbatarwa dasu Inayah Al’amarin ya girmama,
Babban tsoro da fargaba tareda tashin hankalinsu shine idan zancen yaje gaban Abbi yanda zai karbesa.

Sbd farin cikin Inayah sunsan zai iya komai hakama sunsan bazai taba bawa Wainda suka shegantata suka alqantata da ‘yar gaban fatiha aurentaba,
Zancen na zuwa gabansa sunsan maganar bawa su faruk aurenta Kuma ta mutu saidai wani ikon na ubangiji.

Hakan yasa Kiran abbin na shigowa wayar umma yaganah duk jikinsu yakuma sanyi sbd sunsan cm na gidan tun dazu suna magana.

A natse ta dauka tareda sallama a sanyaye tace'”

Naam ABDULMAJEED.

Umma kuzo Palo akwai sako.
Ina Inayah?

Gatanan kwance tana fama da Dan ciwon Kai ne.

Kizo harda ita din.

Yana fadar hakan ya kashe wayar a natse tareda ajiyewa Yana cigaba da sauraren amininsa CM dake fadar rashin dattakon dasu Alhaji suka nuna akan wannan Al’amarin
Magana dai gatanan irinta mata Amma sun biyewa zancen banzan.

Shidai Bai iya cewa komaiba sbd zancen yazo Masa ne a bazata,
Bai taba tunani ko sanin wani zai iya samun guts na aibata ‘yarsaba.

Kuma aibatawa mafi muni bafi tozarci Dan kuwa Saida suka kammala komai na ya’da maganar aure ace an fasa.

Ta wani bangaren Inayah din yakeji,
Tanada rauni sosai
Bata iya saka damuwa ka shiga baqin ciki ba sbd sosai take shiga damuwa,
Da qarancin shekarunta ace itama wannan shine Karo na biyu ana neman aurenta ana fasawa.

Tabbas su Alhaji baba sun tozartasa
Tozarta mafi muni.

Sallamar umma yaganah ce tasashi Dan rufe Ido ya bude batareda ya juyo ya kallesuba Dan yasan dukansu Babu Wanda yake cikin yanayi Mai kyau sbd daga Inayah din har umma yaganah baisan Wanda yafi wani qulafucin aurenba,
Ya rasa meyasa suke tsananin son auren tunda komai lokaci ne dashi.

Inayah na ganin yanayin Abbinta tasan maganar fasa aurence zaai Dan haka ta fashe da kuka ahankali tana kwantawa jikin umma yaganah da itama nata idanuwan sukai jajir.

Har lokacin Bai waiwayo ya kallesuba saidai cm ne yafara bayani cikin damuwa da rashin Jin Dadi yace”

Umma nasan dai kinji bayanin abinda yake faruwa daga bakin Hafsat,

Iyayen faruk dai basu amince da auren faruk din da Inayah ba akan wasu dalilansu da Babu amfanin ambatarsu yanzu,
Dan haka ayi hakuri maganar auren dai yanzu abarta babuta saidai bamusan abinda Allah zaiyi agaba ba,
Faruk idan mijinta ne Inshallah duk wainnan tashin hankalin da maganganun zasu wuce.

Inayah ya kalla cikeda tausayi da kulawa yace”

Kiyi hakuri kinji Inayah
Inshallah Zaki samu mijinda yafi Zaid da Faruk,
Wannan fashin auren wata jarabawace da ubangiji ne kadai yasan tanadin da yayi Miki a gaba.

Kallonta Abbi yayi da idanuwansa dasuka sauya cikin nutsuwa da Jin zafin abinda akaiwa ‘yarsa yace”

Karkiyi kuka ki dauka hakan amatsayin wani gwaji daga Allah.

Umma yaganah ki kula da ita sosai kada ta saka Al’amarin aranta tajawa kanta damuwa ko wani ciwon.
Allah ya zaba Mana abinda yafi Zama Alkhairi.

Amin” suka furta CM da umma yaganah
Inayah kam kuka takeyi sosai Wanda kusan Bata taba irinsaba.

Daqyar ta iya Isa dakin umma ta zube jikin umman Yana Jan numfashi zuciyarta na harbawa da qarfi.

Neman yankewa numfashinta keyi da gudu Neesah taje takawo ruwa suka Bata suna Mata firfita duk da sanyin AC daya cika dakin zufa takeyi sosai tana Jan numfashi ga hawaye nabin fuskarta.

Hankalin umma yaganah da Neesah harma da Anty Hafsat da Safnah da mimi dake gidan tashi yayi ganin yanda Inayah take cikin yanayin ban tausayi ga hawayen idonta dasuka qi tsayawa.

Mimi datai wannan mummunan qullin Saida jikinta yayi sanyi tashiga damuwar tausayin Inayah duk da batai Dan cutatar da Inayah ba tayine Dan lalata Hafsat.

Jiki amace suka watse suka koma gida aka bar ssu umman da Inayah suna fama da ita.

Abbinta dayasan hakan Zata kasance da ita da wuri ya Kira likita akazo gida aka dubata
Harda drip akai Mata qari sbd tashiga tension sosai na Al’amarin.

MAMUH

RIBA BIYU

AYSHATOUH INAYAH

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
0913484810723
Arewabooks@Mamuhgee
Da zazzabi ta kwana sosai a daren Dan haka a dakin umma yaganah ma ta kwana sbd tasamu kulawa da ita yanda yakamata Neesah ma kasa kwana tayi daki ita daya ba Inayah tadawo dakin umman suka kwana.

Washe gari ba laifi ta tashi da lafiyar jiki saidai rashin ta zuciyata,

A sanyaye take gabaki dayanta,
Damuwa da ‘dacin zuciya harma da baqin ciki sune takeji mamaye da zuciyarta tako Ina,

Ga faruk tun jiya sai kiranta yake hankalinsa ya tashi dajin batada lafiya Amma bazata iya daga kiransaba ayanzu Dan kukane kawai zatai tamasa,

Sun shirya tareda tsara yanda zasu gudanarda rayuwarsa da tsantsar so da kaunar juna,
Daga ita har faruk suna tsananin son juna sbd tako Ina suna ganin sun dace da rayuwarda suke so da burin gudanarwa a rayuwar aure.

To menene yasa iyayensa zasu datse musu buri da kaunar junansu?

Meyesa zasu aibatata Rana tsaka Dan kawai cin zarafi ga mahaifinta
Dan kuwa wannan da gani ba ita sukeson tozartawa da wulaqantawaba sai mahaifinta…sai dai kuma duk abinda zaa tozarta ko cin zarafin mahaifinta fita ranta yake.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button