INAYAH 21-30
Anty Hafsat din batai qasa a gwiwa ba takuma hada wani qaninta dasuke uba daya da Inayah.
Sadeeq qanin anty Hafsat yayi karatun likita shima anan Lagos yatashi Kuma sosai yakeda abun kansa saidai yayi irin wayewar datai qazanta shima Neman Mata yakeyi sosai Amma Kuma bazaka kallesa kace yanayi dinba Dan kuwa a kamile yake a zahirinsa.
Ba laifi ya Dan fara shiga ran Inayah saidai Bata wani zura da yawaba sbd tafara Jin shakkar Al’amarin maza da aure.
Shima dagewa yayi da soyayyarsa da kulawarsa harma da alqawuransa yasamu yashiga zuciyar Inayah din.
Wannan karonma ba Bata lokaci ya aiko iyayensa da maganar aure.
Abbin yaso su saurara Kar ayi rushing din Al’amarin Amma Dr sadeeq din ya dage da iyayensa har abbin ya yarda.
Dr Abdulsamad kusan zaucewa yayi da wannan maganar auren Kuma Saida kusan kowa yakusa gane halinda yashiga,
Kasa hakuri yayi sbd zuciyarsa bazata iya daukaba yabi ta qarqashin qasa ya lalata auren ta hanyar tona asalin waye Dr Sadeeq Kuma can ma gidansu anty Hafsat akai fitinar ta hada ‘dan uwanta da ‘yar gaban fatiha tunda ba uwarsu dayaba.
Wannan karon har asibiti Inayah ta kwanta ciwo sosai sbd zuciyarta tafara kasa dauka
Abubuwan sun fara tabata sosai.
Hankalin umma yaganah da mahaifinta ya tashi sosai sbd Saida suka dangana da zuwa Australia taga likita acan tayi jinya
Ta huta kanta ya Dan sake kafin suka dawo.
Ciwonta ba ita kadai ya taba ba harda Dr Abdul Wanda shima hankalin mahaifiyarsa yafara tashi da wannan mummunan masifar dake tunkarota ‘dan ta namiji guda datake alfahari dashi Yana Neman samun tabin qaqwalwa akan son mace.
MAMUH
AA MAJEED
AYSHATOUH INAYAH
DR ABDUL SALEES/HADIZA
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902
MTN card????
09134848107[10/25, 2:11 PM] +234 913 330 3504: 24
Arewabooks@Mamuhgee
Alaqarta da Anty Hafsat Bata taba girgiza ba sbd fashin auren da aka samu akaro na biyu saima tausayin juna dasuke,
Su suna ganin qoqarinta da tausayinta akan yanda taketa kokarin hada Alkhairi Amma Alamuran na lalacewa,
Itama tausayin Inayah takeji sosai sbd yanda Inayah duk tabi ta sukurkurce akaro na uku da fashin auren.
Alqawari tayi bazata qara kawo kowaba ya nema auren Inayah tun basu fara tsanartaba
Amma duk mijinta Inayah Zata aura alqawarine ta dauka itace Zata jajirce su tsaya sosai da umma yaganah suyiwa Inayah gyaran gaske da duk wainda sukaiwa kansu hasarar rashin aurenta sai sunyi kukan baqin ciki da Dana sani.
Yanzu sosai take tsoron kula mazama kwata kwata basa ranta sunma fice Mata Rai sbd a matsayin da raunin zuciyarta yakai aka Kuma samun matsalar rashin aurenta komai zai iya faruwa da ita Dan haka tayi nesa da duk wata alaqar dazata Kuma jefata soyayya.
Abbinta ma sosai yake data da taka tsantsan akan Wanda Zata Kuma samu yaanzu sbd kaucewa hadari da damuwa,
Duk aka Kuma samun irin wannan matsalar likita ya fada Masa zuciyarta ba lallai takuma daukan wani mummunan tashin hankalinba.
A yanayin weak heart irin na Inayah shi baimasan me zatayi da soyayya ba sbd duk wani disappointment Yana cikin soyayya yake gani.
Haka suketa lallabawa da tunanin ta Inda wani manemin auren zai bullo mata.,
Ita dai umma yaganah fargabarta da babbar damuwarta kada Inayah din itama auren yafita ranta kwata kwata kaman mahaifinta,
Shi namijine bazaiyi tsufa a aurenba Nan kusa barema kusan yanzu ne yake cikin shekarun da neman aure agurinsa abune Mai saukin gaske,
Ita Kuma yanzu tanada sauran kuruciya ayanzu ne auren ya kamaceta kaman yanda take buri da tsananin kaunar yin auren
Dan haka ta ninka roqonta gurin ubangiji Allah yakawo musu abokanan rayuwa masu albarka suyi auren.
***Familyn Dr Abdul hankalinsu yafara tashi akan yanda ya dauko hanyar tabarbarewa akan mace,
Duk Wanda yake Dan uwansa yasan INAYAH A MAJEED a rayuwar Dr wata babbar jarabawace,
Abin haushi da baqin cikin shine duk yabi ya lalace akanta Amma wai Bata saniba hakama iyayenta suna gani sunyi kaman basu ganiba,
Hakan yasa kusan duk wasu Yan uwansa sukaji basa kaunar Inayah din sbd Dan uwansu daya Zama gwanin tausayi baida zance sai nata.
Ana cikin hakan Inayah ta hadu da wani yayan abokin Safnah.
Mimi da gudu ta ringa Jin Dadi sbd yanzu mijin ta bangarensu ya bullo Dan haka ta zaqe tanata sake cusa zancen Ahmed din gurin Inayah da umma yaganah saidai Inayah Sam hankalinta Bai kwanta takuma sakewa sosai akan soyayyaba Dan har yanzu akwai sauran son faruk maqale acikin ranta.
A karon farko da zancen ya Isa kunnen Dr Abdul sanyi jikinsa yayi ya silale ya zaune Yana sauraren Inayah din dake fada Masa da kanta.
Bai iya ce Mata komaiba saima kasa kallonta da yayi sbd kada taga yanayinda yake ciki Dan kuwa Zata girgiza da ganin idanuwansa dasukai jajir.
Bai iya tsayawa yin aiki ba ranar sulalewa yayi ya koma gida sbd ciwon Kai Mai tsananin gaske daya taso Masa.
Itama haka Takoma gida jiki amace sbd yanayin Dr Abdul din daya sakata damuwa.
Baiyi bacci ba ranar haka ya kwana Yana juye juyen ciwon Kai Mai tsananin gaske da azaba,
Yasani matuqar Mai samu Inayah ba wlh zai iya haukacewa
Hauka tuburan ta gaske,
INAYAH tazamar Masa jarabawa Kuma qaddara.
Hawayene suka gangaro Masa masu zafin gaske ya miqe zaune tareda nade jikinsa waje daya Yana fashewa da kuka Mai tausayin gaske.
Washe gari Bai iya fita aikiba sbd ciwo ya kwantar dashi
Haka Inayah tazo tareda Dr Emma ya dubasa.
Ciwon kansa Mai tsanani ne Dan haka yayi requesting suje asibiti ya dubasa acan Amma yace AA ba buqatan hakan Inshallah maganin ma zaiyi Masa.
INAYAH ce tasaka aka kawo maganin daga asibiti yasha ya shige ya kwanta itama Takoma gida jiki duk amace.
Kwanansa biyu a kwance kafin ya Dan warware yaci gaba da fita aiki.
Babban abinda ya bawa Inayah tsoro itada umma yaganah da Anty Hafsat shine tun ba’aje koinaba akan maganarta da Ahmed Al’amarin ya lalace ta hanyar Kama Ahmed a drugs case.
Haka kawai hankalin Inayah yaqara tashi sbd ta tabbatar yanzu kam koma menene yake lalata aurenta daga gareta ne sbd shaidu da komai sun nuna Ahmed gskia mutumin kirkine baya hulda da drugs tako Ina Dan haka akafi tunanin sharri akai Masa.
Kan kace me mutane suka fara canfa daga Inayah ne duk Wanda yazo aurenta to masifu kala kala na zuwa garesa.
Hankalinta ya tashi sosai da wannan mugun Al’amarin har abin yaso tabata,
Abbinta kuwa take yafara Dana sanin dawo dasu Nigeria,
Da suna can duk da kila Canfi da wasu abubuwan rashin wayewa basu faruba,
A qasar waje da qabilu daban daban anan dinma basu damu da auren Wanda aka Haifa bada aureba sbd idanma hakane shi ai ba laifinsa bane,
A taqaicema shi abin tausayi ne Musamman ga Wanda hakan ta kasance dashi Yana musulmi.
Amma duk Anbi an hargitsa Masa rayuwa da tunanin ‘ya Bayan duk tattalinsa da kulawarsa sun qare akan ‘yarsa tilo guda.
Fara tunanin maidasu Australia yayi Nan Kuma hankalin umma yaganah yafara tashi sbd har ga Allah tafison zaman Nigeria sbd kana cikin qasarka kafi nutsuwa da kwanciyar hankali idan ba su dasuke Yan boko ba sunfi son rayuwar turai din.
Dama shi Abbin yafi kaunar zamansu acan ne sbd nesanta Inayah da irin wainnan maganganun dayasan matuqar suna Nigeria yau da gobe sai Mutane sunfara maganganun dazasu saka Mata wasi wasin asalinsu akanta.