GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 21-30

Ya zabi barinsu zaman wata qasar ne da nesantata da bude Baki wataran ta tambayesa mahaifiyarta kokuma asalinsu,kokuma labarin yanda mahaifiyarta ta tafi tabarsu.

Gashi tun ba’aje koinaba anfara rikita Masa kanta da wainnan fitintinun,

Auren data sakawa ranta ta nace gashinan Bata samu ‘dan amanar dazai iya aurenta dan Allah ba,
Daga Wanda keson aurenta Dan dukiyar mahaifinta sai Mai son wani bangare na jikinta sai masu aibata zuwanta duniya.
Dan hakan yanke shawaran maidasu kawai su koma sai Kuma gaba idan Allah yakawo dalilin dawowar.

Labarin barinsu Nigeria shine ya fidda asalin ciwon dake damun Dr Abdul akan Inayah Dan kuwa har Saida yayi Dana sanin lalata aurenta da Ahmed tunda wuri.,

Kusan zaucewa yayi Dan kuwa baimasan lokacinda yakai kansa gurin Abbinta ba Yana kuka da idanuwansa akan yabasa aurenta shi zai aureta sbd Babu Wanda yakaisa sonta.

Dama yasan za’ai hakan to Amma shi kam soyayyar Dr Abdul din shakku take sakasa,

Son yayi yawa,
Bai taba ganin irin hakan ba,
Basa Inayah din kaman yanada hadari sosai sbd irin wannan ya wuce so ya zama possession.

Amma Kuma ta wani bangaren tausayi Mai zurfi Abdulsamad din yake basa sbd mutum ne Mai nutsuwa da Kamala tareda ilimi sosai Amma sbd soyayya shima duk hakan na Neman gagararsa,
He is loosing everything slowly.

Ta wani bangaren yasan samun Inayah ce warakar Dr Abdul din haka zalika badan tabin kan son dake Neman yawaba yasan Dr Abdul zai Zama Miji nagari Mai kula da kauna ga Inayah.

Dan haka ko yanzu Bai cire ran Dr Abdul din zai kasa kula da Inayah ba,
Yana saka ran idan yasamu Inayah din bazai Bari haukarsa ya cutatar da itaba Dan haka yace yabasa dama ya nema Inayah din idan ta amince shikenan,
Amma da sharadin zai bisu can qasar zai Samar Masa aiki a one of the best hospitals dake qasar
Yaci gaba da aikinsa acan da matarsa.

Baiga abinda zai tsaya tunaniba matuqar zaa basa auren Inayah din Dan haka Kai tsaye ya amince,
Dan koba komai kusan qaruwarsa ce zuwa wata qasar aiki.

A natse abbin ya girgiza Masa Kai Yana cewa”

No Kar kayi rushing abubuwan
Zaje kayi shawara da iyayenka da mahaifiyarka dakace,
Sbd kaman abune da bazaka iya yankewa Kai dayaba Dole kana buqatan iyayenka aciki.

Shidai farin cikinsa ya hanama ya tsaya dogon zance ya amsa da cewa”

Inshallah zan tafi cikin satin Nan na sanar da ita komai Umman tawa.

Allah ya taimaka yasa hakan shine mafi Alkhairi.

Amin, thank you sir,
Ngd sosai Allah yaqara girma da rufa asiri.

Amin.

Abbi ne da kansa ya sanarda umma yaganah da Inayah buqatan Dr Abdul na abasa damar neman auren Inayah din Kuma yabasa damar Amma sai idan ta amince.

Umma yaganah ba Bata lokaci ta bayyanarda farin cikinta sbd ta jima tana yiwa Inayah shaawar auren Dr Abdul din Dan nutsuwarsa da kamalarsa,
Gashi kyakkyawa shima da Dan arzikinsa ba laifi.

Shi kansa Abbi gskia Dr Abdul din ya kwanta Masa fiyeda duka maneman da Inayah din tayi a baya Amma Kuma yafison tayi zabi akan Dr Abdul din da kanta.

Wani iri taji Al’amarin a farko Dan haka batace komaiba.

Neesah tafara fadawa a waya
Aikuwa Neesah ta ringa tsallen Murna sbd tasan Dr Abdul tako Ina yayi gskia,
Ita da harta fara yiwa kanta sha’awar aurensa Amma ganin basa qasa daya yasa bata zurfafawa kantaba dakuma hango tsagwaron son Inayah a idonsa.

Safnah ma tsallen murna ta ringa Yi tana cewa”

Wlh dama nasan zaai hakan sbd Dr Abdul ya dade da mutuwa akan sonki Naga alama.

Anty Hafsat ma a nata bangaren hamdala da godewa Allah tayita yi sbd dukkaninsu sun yaba da mutuncin Dr Abdul dakuma shedar irin son dayake Mata bazai taba gudunta ba Dan duk wani abunda zaa fada.

Itadai Inayah tanajin ‘yar shakkar Al’amarin sbd girman matsayin Dr Abdul a ranta idan sanadin auren Nan suka rabu tasan Zata shiga mummunan hali fiyeda lokutan baya sbd matsayin Dr Abdul a ranta jinsa take yafi Mata duk wata soyayyar datake abaya,

Kaunarsa takeyi sosai cikin ranta tana jinsa tamkar wani jininta,
Tasha gwada yimasa kallon wani bangare na rayuwarta sbd mahimmancin mutuncin dasuke da juna.

Umma yaganah, Neesah,anty Hafsat da Safnah ne suka taru suka ringa azalzala Mata soyayyarsa da nacin nusar da ita irin yanda yake Sonta.

Tun tana jin Al’amarin wani iri sbd Bata taba tunani ko kawo kwatancin soyayya harda aure zai shiga tsakaninta da Dr Abdul dinba har tazo nacinsu da kulawarsa daya soyayyarsa da yanzu yagama bayyanar Mata suka sauya matsayi da kaunarsa cikin ranta zuwa tsaftatacciyar soyayya Mai nutsuwa.

MAMUH

RIBA BIYU

AA MAJEED ABBI/AYSHATOUH INAYAH

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107
[10/25, 2:11 PM] +234 913 330 3504: 25
Arewabooks@Mamuhgee
Ganin hankalinta ya kwanta akan auran Dr Abdul din sai kowa yaqara bada himma gurin qarfafa Mata gwiwa da sake kwantar Mata da Al’amarin cikin zuciyarta,

Bata sake sakankancewa ta budewa Dr Abdulsamad zuciyarta ba Saida Abbinta ya nuna Mata goyan bayansa akan auren Abdulsamad
Dan haka ta budewa Dr Abdul dukkanin zuciyarta ta karba soyayyarsa.

Abdulsamad tamkar a mafarki yakejin rayuwarsa yanzu dazai mallaki Inayah amatsayin matarsa halak malak batareda shamakin kowaba.,

Sosai kowa ke mamakin yanda duk yabi ya kasa sukuni ya rude Yana bayyanarda farin cikinsa koina.

Tamkar wani zautacce yakomawa Inayah soyayya yake nuna Mata kamar ba Dr Abdul din data saniba tuntuni.

Ita tausayinsama takeji Mai qarfi dayake qarawa soyayyarsa girma cikin ranta sbd Batasan haka yake tsananin sontaba da bazata taba tsayawa kula kowaba da tuni ta amince dashi anyi aurensu.

Mahaifiyar Abdulsamad kam sosai take qaunar Inayah sbd yanda ‘danta ke tsananin sonta,
Da farko hankalinta yaso tashi sbd tunanin Bazaa bawa Abdul dinta auren Inayah ba duba da matsayinsu na wainda sukafi na Abdulsamad din kudi sosai sai gashi anyi halin girma anbasa aurenta Dan haka take kaunar Inayah har ranta duk da iyakacinsu waya haryanzu Allah Bai saka sun hadu a zahiri ba wata kila sai lokacin bikin Auren.

***Ansaka lokacin bikin Wata biyu masu zuwa Dan haka ko wannan karon su umma yaganah da Anty Hafsat da wuri suka fara shirya ‘yarsu Inayah tako wane fanni.

Gyaranta akeyi sosai Dan kuwa Abbi ya sakar musu kudi suna yanda suke so dasu gurin harkar shirye shiryen bikin.

Wannan karon baiyi wani gayyataba sosai sbd kaucewa hayaniya albarka auren akeso ba taronba,
CM ne ma dai dayafi A MAJEED din shiga mutane sosai ya dauka nauyin gayyatar ta hanyar aikawa manyan mutanen dasuke taredasu special invitations na auren.

Anty Hafsat ta haukace tsima Inayah kawai takeyi tako Ina da abubuwa masu kyau da inganci nasu na manyan mata.

Umma yaganah Kuma masu gyaran jiki takuma sakawa aka kawo matasu daga maiduguri harma da ‘yan uwanta biyu dasuka zo bikin auren Dan haka tako Ina families din guda uku nasu na A MAJEEDs,da iyalan gidan CM saina dangin ango dasuke Adamwa hidimar biki akeyi gadan gadan ta kowane bangare.

Inayah tana cikin wani irin farin ciki Mara misali sbd jikinta da dukkanin imaninta yabata wannan karon Zata auru Inshallah bazaa fasa aurentaba Dan haka taketa Jin farin cikin igiyoyin auren Abdulsamad dintane zasu hau kanta bana kowaba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button