INAYAH 21-30
Shikan oga Dr Abdulsamad fadar irin farin cikin dayake cikima wasane Dan kuwa jin yake Kamar zai take kan jariri dama uwar jaririn ya wuce sbd zumudi da farin ciki.
Lafiyayyan lefen aure dangin Abdulsamad din suka kawo ana Saura kwana biyar afara bikin Wanda su umma yaganah sun yaba sosai da irin kokari dakuma uwar dukiyar dasu Abdul din suka kashe.
Neesah sai a ranarda aka kawo lefen itama tasamu isowa daga Australia tareda Dr farhat wadda ita ta sauka a gidan Mahaifiyarta dake aure a Lagos din Dan haka tana zuwa suka sake hautsinewa da Murna.
Safnah ma tuni tadawo gidan da kwana sai angama biki so gabaki daya gidan dai a kacame yake da jama’ar biki duk da ba wasu masu irin yawa dinnan bane.
Inayah gabaki daya ta sauya Takoma tamkar wata jaririyar da aka Haifa acikin watan sbd tsananin kyau da taushi da fatarta tayi,
Gyara da rashin fita tareda tsananin hutu da kwanciyar hankalin datake ciki a watannin yasa tayi wani irin zallar fresh sai sheqin fata takeyi.
Tunda Dr Abdul yazo yaga irin kyau data qara da sheqin amarci datake tun yanzu yasa yaqarasa rikicewa akanta duk da soyayyarsa Bata shaawa bace Amma tuni kyanta ya qarasa rikita Dan sauran nutsuwar dayake da ita akan Sonta daya zaburesa.
Ganin yanda yabi ya rude hakuri na Neman gagararsa yasa Anty Hafsat ta hanasu haduwa sosai tace sai lokacin bikin Dan haka yanzu a waya suke koyaushe ba sakat Kamar wasu hanta sa jini.
Abbi kam sosai Al’amarin nasu ke Dan basa mamaki da dariya kawai sbd yanda Inayah tasan ta iya soyayya sosai irin haka Dan shi haryanzu a jaririyar ‘yarsa yake kallonta gashi zatai aure takoma qarqashin ikon wani.
Yau sosai take amatuqar gajiye sbd saka lalle da akai ayau din can gidan CM Dan haka sosai take amatuqar gajiya Koda suka dawo gida zare tsadadden lace din dake jikinta tayi Mara nauyi ko kadan ta nufi toilet tashige.
Gaban mirror ta tsaya tafara goge fuskarta tas da Neutrogena makeup remover wipes.
Wanka tayo da ruwan dumi kafin tafito daureda towel tana kallon Neesah ma dake jiran ta fito wankan itama tashiga tayo Dan duk makeup din fuskokinsu damunsu yakeyi sbd basa wani makeup dama can
Iyakacinsu Liner da mascara sai lipstick masu tsadan gaske dake zaunawa da kyau abakinsu idan sun saka.
Sama sama ta shafa Mai tareda spray dasu khumrahs masu sanyin qamshi da akayo Musamman masu tsada daga maiduguri.
Riga da wango tasaka masu kauri sbd sanyi sanyi datake ji.
Sallolin dake kanta tafara Yi kafin ta miqe ta fito tana waya da Dr Abdul dinta ta nufi dining tana cewa”
Heart yunwa fa nakeji sosai yau banwani ci abinci ba
Zaa ramar maka Ni da yunwar biki.
Cikin kulawa sa so Mai tsanani ya karyar da murya yana cewa”
Ni zasu illata gskia bazan dauka ba,
Kyakkyawar amaryar tawa ce zaa Bari da yunwa
Gskia bazan yardaba
Laifin anty Hafsat ne data hanamu haduwa yanda muka saba kewanki is driving me crazy
Gobe da safe zanzo na ganki kafin su Umma su iso sbd itama tana zuwa Zata qarawa anty Hafsat qwarin gwuwar hanamu ganin juna sai ranar Daurin auren.
Murmushi tasake Mai kyau tana cewa”
Dan Allah kazo goben da wuri Nima nayi kewanka fa sosai.
Zama tayi a dining daidai lokacinda Abbi ke isowa dining room din a kasalance ta ajiye wayar sbd bataso Gama waya da Heart dinta ba Amma Kuma girman Abbinta na daban ne akan komai.
Kallon abbin tayi Yana sanye da Fararen hoodie graffiti print sweatset.
Sanyin qamshinsa ne yake neman danne na Lafiyayyan abincin dake jere kan dining din yayi fresh Kamar ba baban amaryar ba Batasan lokacinda ta sake qaramar dariyaba tana cewa”
Abbi barka da fitowa.
Da Dan silent murmushi ya kalleta yana amsawa da cewa”
Barka Amaryan Dr Abdulsamad.
Dariya tasake tana kallonsa tace”
Abbi Naga kamanma ka matsu natafi nabar gida,
Kullum saikace mun amaryar,
Nidai kunya nakeji Gaskia.
Wani qayataccen murmushi ya sake daidai lokacinda Neesah da umma yaganah suka iso dining din cin abinci yace”
Inayah kinsan kunya dama?
Inace you don’t know the name kunya,
Kin manta a gabana kike zuwa kina kukan soyayya da Kiran sunan zayyan ne sunan koma fahat ne I can’t recall
And now kinata tsalle da murnan zakiyi aure shine kike fadamun kunya
Rashin kunya plus lie ko??
Dariya umma da Neesah sukai umma na saka musu Baki da cewa”
Inayah kam ai indai anan cikin gidane Babu Wanda take kunya saidai mutane waje take kunya.
Kai umma yaganah please karki sake batan suna gurin Abbi Kinga zaifi kowa kewata fa idan natafi ko Abbi?
Abincin data Gama zuba Masa yafara ci yana Dan gyada Mata Kai ahankali.
Bayan sun Gama cin abincin bin Abbinta tayi palonsa suka cigaba da maganganunsu na tsakanin uba da ‘ya sai kusan after 9 tafito ta nufi daki ta kwanta bayan tasake goge fuskarta da face cleanser.
Washe gari shine zaai Mata lalle Kuma tasan heart dinta yace zaizo Dan haka da wuri ta tashi tayi wanka ta shirya cikin Riga da skirt na maroon super exclusive wax da qaramin Marron veil ta fito a sace sbd yaca Mata ya iso Yana palon Abbi.
Tana shiga palon Abbin Yana zaune tareda Abbi suna magana cikin nutsuwa.
Bude kofar tareda sallamarta a sirance tasaka su waiwayowa kallon kofar atare take zuciyar Abdul yakusa bugawa.
Ya salam ya furta a fili batareda yasan ya furta hakan agaban Abbin ba.
Qamshintane ya doshi hanyar mamaye palon gabaki daya sbd wasu irin qamshine kala kala na designer turarukanta masu tsada da turarukan khumrahs da akai Mata masu tsananin sanyin qamshi da shiga zuciya.
Kallo daya Abbi yayi Mata yaga yanda daga ita har Abdul din suke kallon juna yaji mamakin gaske yana kamasa ta yanda Inayah duk ta lalace har haka baida sani.
Ahankali ya dauke Kai daga kallonsu tareda gyara murya yana Kiran sunan Inayah din a natse.
Cikin nutsuwa da girmamawa tace”
Yes,
Good morning Abbi.
Qarasowa tayi tareda dauke kallonta daga kan heart din tana Zama kusada Abbinta tasake gaidasa.
Amsawa yayi tareda Dan kallonta yace”
Hafsat tasan kinzo Nan?
Murmushi tayi tana girgiza Kai da cewa”
Abbi Bata saniba banaso ta sani please.
Da mamaki ya Dan kalleta sbd yasan hakan bai kamataba Musamman yanzu irin yanda yaga suna maitar kallon juna bayason ko kadan shedan ya Shiga zukatansu Koda rungumace suyi kafin aurensu tunda daga yau ne sai gobe jibi zaa daura auren Dan haka ya Dan kame fuska a kame yace”
Ok ku gaisa ki koma ciki zanyi magana dashi.
Bata fuska take Neman yi ta marairaicewa abbin Amma ganin ba wannan damar yasata kallon Abdul daya Gama mutuwar zaune gurin satar kallonta ta gaishesa a gutsure.
Amsawa yayi batareda ya kalleta sosaiba tunda Abbi na gurin
Badan sun soba su duka haka ta juya Takoma Inda ta fito.
Shima Bai wani gane sauran zantukansa da Abbin ba sama sama ya gane yayi Masa sallama ya wuce.
Jiki mace akai Mata zanen kunshin sbd rashin ganawa dakyau da heart dinta.
Sai kusan yamma daya kirata yasamu yasaka zuciyarta da ranta ya sake suka Dan zanta a wayar kafin ta aje tashiga wanka sbd anmata dilkan yamma again.
Washe gari Koda ta tashi da murnar sauran kwana daya ta tashi hakama da damuwar rabuwa da Abbinta Dan haka ta ringa samun sauyin yanayi aranar,
Tayi farin ciki tashiga damuwa ahaka dai yamma tayi duk saitaji tashiga damuwar tunda gobene Zata bar gidan gashi har yamma tayi Babu abinda ya rage a wunin yawuce sai kawai ta fashe musu da kuka.