GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 21-30

Bata taba tunanin halinda Zata shigana ranarda Zata rabu da mahaifinta sai yau Musamman idan ta tuna da Heart dinta Dan Adamawa ne can zasu tafi da ita bazata sake Zama gurin Abbinta ba
Tsorone Mai girma ke Neman cika zuciyarta sbd duk Inda Zata tafi jinta safe cikin nutsuwa da kwanciyar hankali agurin mahaifinta.

Tun su anty Hafsat na Mata dariya hardai suka fuskanci da gaske takeyi hankalinta ya tashi matuqa a tsorace take.

Umma yaganah ma jikinta duk yayi sanyi Musamman itama datai wata irin sabo da shaquwa da Inayah din tun jarinta.

Heart dinta hankalinsa ya tashi da kukan nata sbd kowa yayi yayi taqiyin shiru shiyasa anty Hafsat tafada Masa kozai iya zuwa ya lallashi Inayah din
Itama umma yaganah takira Abbi tafada Masa Inayah fa tana nan tana zabga kukan bazata iya zuwa Inda Batasan kowaba ta rabu da mahaifinta.

Cewa yayi idan yagama magana da baqinsa dasuka iso Lagos domin daurin auren goben zai iso gidan.

Dr Abdulsamad Yana tareda mahaifiyarsa da qannan babansa biyu Mata sai ‘yayan yayyun mahaifiyar tasa biyu suma Koda anty Hafsat me Masa wannan bayanin.

Kallon umman yayi yace”

Umma Bari naje gidan Inayah ce tanata kuka wai bazata iya zuwa garinda batasan kowaba.

Murmushi umman tayi cikeda mamakin shirme irin na Inayah
Gata ta girma dai Amma gata yasa yarinyar kasa nuna ta girma.

Wayarta dake gefenta ta dauka tana cewa”

Kaga bara natashi muje tare sbd dama yakamata da muka iso munje gidan an gaisa kafin goben ranar biki muje gidan,
Kaga dama abinda yasa nazo da kaina kenan sbd Inayah din tasake tasan muna kaunarta sosai
Nice zan karbeta da hannuna Inshallah cikin Amana bazamu Bari tayi kukan baro gidaba.

Gaba yayi Yana cewa”

Okay umma saikin fito to.

Bayan fitarsa tsadadden mayafinta dake ajiye ta dauka tareda LV handbag dinta ta nufi kofa tana cewa”

Nafisat zo muje Naga kece a shirye da alama su Asmau akwai sauran gajiya atare dasu kaman wainda sukai tafiyar mota bayan jirgi kuka biyo.

Ficewa suke kokarin Yi yayar mahaifin Dr Abdul dake sallah tana idarwa cikin Dan daga murya tace”

HADIZAH.

cak umman ta tsaya tareda waiwayo tace”

Na’am.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107[10/26, 8:44 PM] Sweet sis: 26
Arewabooks@Mamuhgee
Ku jirani a motar Bara na sauya Kaya muje Nima zan gaisa da iyayen na Inayah tunda dai kaman yanda kikace din yakamata muje a gaisa basai gobe bayan daurin aurenba muje.

Ok Tom muna jiranki a motar.

Juyawa tayi ta fice daga babban dakin ta ratsa palon zuwa babban palon gidan na mijinta Wanda Sam basa Zama anan tunda aikinsa na soja ya maidasa Abuja ita saita koma Adamawa sbd uwar gidantace a Abuja ita Kuma a Lagos to ana Masa transfer zuwa Abuja tabar Lagos Takoma babban gidansa dake adamawa.

Tana Isa motar Haj balaraba na isowa Dan haka sai kawai suka shiga suka wuce zuwa gidansu Inayah din.

Tafiyar mintuna sukayi suka iso lafiyayyar anguwar ta masu abun duniya.

Kai tsaye security ya budewa Abdulsamad din gate Yana daga murya da cewa”

Welcome Sir.

Yauwa thank you Bosco.

Parking yayi tareda kashe motar suka firfito su umman na sake yaba arzikinsu Inayah din Dan kuwa gidan irin tsarin ginin turai ne komai ma kusan yanda Inayah takeso akayisa.

Kai tsaye hanyar kofar palon cikin gida ya nufa dasu
Sbd su din Bai kamata yabi ta hanyar palon Abbi dasuba.

Suna Isa kofa Safnah na fitowa da waya a hannunta tanayi ganinsu yasata katse wayar Dan nuna girmamawa gasu umman Abdul din dasuke manyan Mata sosai.

Cikin sakewar fuska da girmamawa tafara musu sannu da zuwa tana gaidasu.

Juyawa tayi tai musu jagora zuwa can qurya palonda kowa yake Anata fama da Inayah din.

Tsokar Abdulsamad tayi da cewa”

Yanzu sbd heart din taka ka tado su umma da magribar fari Dan azo a rarrasheta.

Dariya yayi yana cewa”

Safnah harda ku kuka sake rudar mun da ita gskia
Amma haka kawai baby bazata fara kukan Nan ba.

Shi a palo ya zauna Yana amsa waya sukuma su umma palon ciki tayi dasu.

Su umma yaganah dasu Mimi na ganinsu cikeda farin ciki da mutuntawa suka tarbesu suna musu sannu da zuwa a waye.

Mahaifiyar Abdulsamad hadiza babbar mace ce Mai tattare da Kamala da mutunci sosai Kuma a bayyane ta nuna kaunarta da kulawarta ga Inayah.

Drinks da snacks zubbi da Salimat suketa aikin kawo musu Anata sake musu sannu da zuwa.

Cikin Jin Dadi da farin cikin yanda aka karbesu hannu bibbiyu da mutuntawa suketa amsawa suna sake yaba gatan da Inayah take dashi Dan duk Wanda is kalla yanayinsa a gidan zaka tabbatarda yanda yake kaunarta tunda kusan duk albarkacinta kowa keci acikinsu adai cikin gidan da rayuwar AA MAJEED.

Da ‘yar Raha umma yaganah tace”

Kuna fama da gajiyar tafiya Rigimar Inayah ta fiddoku,
Shima Abdul din dabai daukokuba ai yabari Kun huta shegantaka ne kawai irin na Inayah Zata fara kukan barin gida tun yanzu
Ai tabari har zuwa goben idan andaura aure.

Yar dariya Haj balaraba tayi tana cewa”

Ai Dole zatayi kuka tun yanzu sbd auren nesa na gida Daman sai kaji kaman shikenan katafi.

Umma Hadiza kuwa Inayah data fito daga bedroom sanye cikin Riga da skirt na soft embroidery Swiss Mai kyau da tsada navy blue ta zuba Mata Ido gabaki daya tana kallonta.

Duk hotunan Inayah da vidcall dasuke ganinta idan Abdulsamad na gida basu bayyanar Mata da kamannin Inayah ba kaman yanzu datake ganinta a gabanta.

Da farko zuciyarta harbawa tayi da kyawun fuska Dana jikin Inayah hartana Jin Anya Abdulsamad bazai bartaba akan matarsa Inayah bayan auren
To Amma Kuma zuciyarta tarigada ta kamu da kaunar Inayah tun kafin auren sbd son da Abdulsamad ke Mata to yanzuma data ganta saitaji kaunarta Mai nutsuwa da tsafta takuma shigarta.

A natse Inayah ta qaraso Inda suke fuskarta duk yayi ja sbd har lokacin hawaye takeyi sosai Musamman ganinsu umma Hadiza sai taji kaman sunzo tafiya da itane gabaki daya zatabar gida.

Cikin farin ciki da kulawa tareda murmushi a fuska umma Hadiza ta kamo hannunta ta zaunar da ita a gefenta tana cewa”

Zo ki zauna ‘yata Inayah kinji,
Ki daina kuka sbd inshallah bazamu taba Bari kiyi kewansu umma da Abbinki ba sosai Dan zamuyita tattalinki muma kaman yanda suke Inshallah.

Ba kunya Inayah ta dago ta kalli umma Hadiza alamar da gaske kike fada.

Da sauri umma da Anty Hafsat suka dungure Mata kan suna cewa”

Inayah wai bazakiyi hankaliba ko??

Su umma Hadiza da haj balaraba kuwa dariya suka sake atare harma dasu Neesah
Haj balaraba na cewa”

Eh Inayah Inshallah bazakiyi kukan shigowa zuriar muba da yardar Allah,
Barema wannan ja’irin Abdulsamad duk Wanda ya damar Masa Mata Inayah ai nasan zaburewa zaiyi da rashin arziki kala kala
Shima Kinga muna kaunarsa sosai Dan haka bazamu Bari matarsa ta Shiga damuwar dashima zai shigaba.

Washe Baki su umma yaganah suka hau Yi suna Jin dadin sirikan da Inayah tasamu masu kaunarta.

Murya a sanyaye Inayah ta bude Baki cikin girmamawa ta gaidasu tana Dan sake goge hawayenta.

Inayah daina kukan kinji Inshallah Baki rabu da gida ba duk lokacinda kikaso gida zakizo ki gansu
Kuma kin manta Anan Abdulsamad din yake aiki ne?
Bawani dadewa zakuyi a Adamawanba zaku dawo Lagos mune ma zamu ringa zuwa dubaku basaikunyi wahalar zuwanba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button