GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 21-30

Ahankali Inayah ta saki Dan siririn murmushi tana kallon su Anty Hafsat dake Mata dariya.

Da Raha Haj balaraba tasake cewa”

Inayah akwai sauran kuruciya kam,
Gaki ‘yar fari shiyasa aketa shagwaba ko?
Nikam ma menene Ma’anar sunan Inayah Dan naji sunan shima na Yan shagwaba.

Dariya sukai saidai anty Hafsat ce tace”

Ma’anar sunan Inayah shine kyauta daga Allah,
Kaman ace kyautar datazo wadda bayan Allah Babu Mai iya baka ita.

Dukkaninsu murmushi sukai ana cigaba da Dan sake maganganu cikin Raha da mutuntawa har lokacin sallah yafara wucewa Dole suka tashi Dan gabatar da sallah.

A dakin umma yaganah aka Kai su umma Hadizan suyi sallah sai alokacin Inayah tasamu ta Isa Palo gurin Heart dinta.

Yana ganinta ya taso a natse tareda miqa hannunsa ahankali ya kamo nata hannun suka Isa kujera suka zauna Yana kallon fuskarta datai ja cikin damuwa da kulawa sosai yace”

Baby sosai kikai kuka haka?
Oh my God,why baby?

Wasu hawayen takuma gangaro Masa tana sake narkar Masa da fuska tace”

Heart Dan Allah karmu dade Adamawa da yawa mudawo Lagos da wuri.

Numfashi ya sauke Yana goge mata hawayenta da tissue din dake palon cikin kulawa kaman ya janyota ya rungumo yace”

Baby ki daina hawaye da damuwa please,
Idan Dan zakibar gidane na miki alqawarin bazamu dauki lokaciba zamu dawo okay?

Gyada Masa Kai tayi tana tsayar da hawayenta.

Lallabata yayi takoma ciki Dan yin sallah shima ya fice zuwa qaramin masallacin dake gefen gidan yayo sallah Yana dawowa yace su umma su fito ya maidasu gida akwai baqinsa dasuka iso daga Adamawa yau Dan daurin aure zai samesu a hotels din dasuka sassauka su gaisa friends dinsane sosai.

Yana harabar gidan jikin motarsa Yana jiransu saiga motar Abbi tashigo yadawo shima.

Su umma Hadizan ne suka fito tareda su Anty Hafsat da Mimi dasuka rakosu harma da Inayah dake maqale gefen Haj balaraba tana sake rarrashinta cikin kauna da kulawa.

Cikin maroon luxury motar Bentley bentayga yadawo gidan Dan haka suna ganin motar duk suka tsaya Dan gaidashi dakuma su umma Hadizan ma su gaisa tunda yariga yadawo.

Cikin wani Sky blue tsadaddiyar soft Italian cashmere a jikinsa ya fito
Fuskarsa fresh a kamile.

Kyakkyawar fuskarsa ya juyo da ita ya kalli Inda suke gabaki dayansu sun tsaya suna jiran fitowarsa daga motar a girmame.

Hasken fatarsa da dogon hancin zuwa haiba da kwarjini Mai yawa da Allah yayi Masa yasa dukkaninsu Babu Mai iya Masa kallon quru quru saidai a gaisa kana Dan sauke Kai a mutunce.

Inayah ce tabar gefen Haj balaraba ta nufesa tana kallonsa cikin kulawa tace”

Abbi barka da dawowa.

Wani nutsatsen murmushi ya sakar Mata Yana amsawa Kai tsaye da kallon fuskarta datai ja sbd kuka a natse cikin lafazinsa masu nutsuwa yace”

Duk kukan da kikaita yine wannan?

Bata fuska tayi zatai magana anty have ta Dan qaraso kadan tana Masa sannu da zuwa cikin girmamawa tace”

Sirikan Inayah dinne wato mahaifiyar Abdulsamad sukazo tareda yayar mahaifinsa zasu tafi ko zaku gaisa.

Ok ba damuwa”
Ya furta tareda qarasa tahowa cikin nutsuwa Inayah din na gefensa kaman Zata maqale Masa.

Tunda suka doso su kowa ya sake Dan kame kansa suna rage kallonsu akansa sbd kam badai cika Ido da zallar haiba ba.

Umma Hadiza datai Masa kallo daya taga fuskar kaman wadda ta sani Dan haka ita bata dauke idonta akansaba taci gaba da bude idanuwanta dakyau akansa.

Dan juyawa kanta yayi kadan sbd toshewar Dan qwaqwalwanta ke Neman Yi gabaki daya da kamannin nasa.

Baya wani kallon Mata Musamman su din dayaga ba laifi dattijai ne Dan haka a mutunce ya gaisa dasu ya kalli Abdulsamad dake nuna umma Hadiza yace”

Sir wannan itace mahaifiyar tawa.

Dan sake fuska Abbin yayi kadan tareda kallon umma Hadizan a natse yace”

Barka da zuwa Haj,
Ya hanya?
Allah ya hutarda gajiya……

Tsit yayi bayan yasamu yakai qarshen gaisuwar a Dan rarrabe.

Kallon fuskarta yakeyi dakyau cikin Dan basarwa sbd danne duk wani Abu dayake yunquro Masa cikin Rai.

Mummunan bugawa Mai qarfi zuciyarsa tayi wadda bayajin yataba samun wannan bugawar.

Sam Bai nuna halinda yashigaba saima juyawa da yayi ya wuce ciki Yana musu a sauka lafiya.

Mutuwar tsayece da daukewar hankali na daqiqu agurin ya Kama Hadiza Saida Haj balaraba ta Dan girgizata tana ambatar sunanta.

Kasa motsi tayi sai kawai sukaga tana neman zubewa sbd duhun dayake Neman rufe idonta da qyar ta iya bude Baki murya a hargitse ta furta”

BP Dina ya hau sosai please ku kaini gida Nasha magani bana gani sosai.

Hankali tashe Haj balaraba da Abdulsamad din suka kamata ta shiga mota dukkanin jikinta na rawa a rude sukabar gidan.

Da tausayin umma Hadizan su Inayah suka koma cikin gida Bata tsaya komaiba ta nufi sashen mahaifinta.

Zaune yake numfashinsa na Dan fita da sauri
Qananun zufa na tsatsafo Masa a goshi da alama Yana Jan numfashi ne dake Neman qwace Masa da qyar.

Da gudu tayo kansa tana Kiran sunansa hankali tashe da firgici Dan Bata taba ganinsa hakaba.

Bai dago ya kalletaba ya karba tissue din datake goge Masa zufa
Ya Dan kame kansa Yana kokarin basarwa a hankali yace”

Ya Isa haka, I’m okay kije
Kawai.

No Abbi bakada lfy
Kana gumi fa.

Ahankali ya furta”

I think my BP dropped.

Wat?” Tafada da sauri tana kallon yanayinsa.

Juyawa tayi da sauri tana cewa”

Bara naduba.

BP monitoring machine harma dasu sphygmomanometer ta dauko da sauri tadawo cikin damuwa sosai.

A tsaye ta taddasa kaman ba Wanda tabari Yana Dan hada gumi ba da jajayen Ido.

Da mamaki ta tsaya da Kaya a hannunta tana kallonsa cikin mamaki da kulawa tace”

Abbi?

Magana zatai ya Dan waiwayo ya kalleta a Dan kame yace”

Kibarshi kawai ya wuce
Zanyi baqi yanzu ki koma ciki.

Kallonsa tayi a marairaice da fuska Zata Kira sunansa da ‘dan daga murya yace”

Nace kije Inayah.

Hawayen tashin hankali da tsoro taji suna Shirin gangaro Mata sbd yaune karon farko da Abbi yayi Mata tsawa tunda dai ta girma tasan kanta.

MAMUH

AYSHATOUH MRS AA MAJEED

LOVE/ROMANCE/MARRIAGE

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107
[10/26, 8:44 PM] Sweet sis: 27
Arewabooks@Mamuhgee
Kasa riqe hawayenta tayi suka gangaro Mata ta juya a sanyaye tana Satan kallonsa Zata fice ya sauke wani boyayyan numfashi tareda ajiyar zuciya Mai tafe da hucin zafin da Kai da kirjinsa suka dauka a natse Yana sake kame kansa da basar da yanayin dayake ciki ya bude Baki yakira sunanta a natse.

Da sauri ta juyo ta dawo Dan dama bason tafiyar takeyiba ta kallesa tana share hawayenta tace”

Na’am Abbi.

Sake sauke ajiyar zuciya yayi wannan karon kansa na qara daukan zafi Mai tsanani kawai dannewa yakeyi Yana basarwa kada hankalin ‘yarsa ya tashi babban burinsa a yanzu ya karkata akan baya kauna ko kadan bare fatan wani illa yazo ya gifta a cikin auren Nan da zaa daura gobe dan kuwa wannan karon aka fasa auren ‘yarsa Allah ne kawai zai Raya Masa ita sbd gargadin da likitanta yabasu akan sake shigarta tashin hankali.,

Komai zai iya faruwa da ita idan takuma shiga wani mummunan shock na tashin hankali,
Ganin wannan matar ya girgiza kansa da tun tsawon shekaru masu tsayi kan ya bushe,
Ganin mahaifiyar Abdulsamad babbar masiface tabbas Zata bayyana Dan kuwa idan itace mahaifiyar Abdulsamad akwai gagarumar matsala.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button