MUTUM DA DUNIYARSA 59 – 60

*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[59➖60]_*
…………Duk da agidan Maimunatu ta
girma, kuma akwai mariƙiyarta Iya Habi, hakan baisakata kaisu canba itada Jiddah, saita nufi ɗakin hajia bah-bah uwargidan Malam.
Sosai Hajia bah-bah taimusu tarbar mutunci, hakama Na’ima tafito fuskarta ajiƙe da alamar alwala tayo tana musu oyoyo.
Harara Maimuna ta zuba mata tana faɗin “Anƙi a amsa ɗin, aini yarinya mun ɓata”.
“Haba-haba Uwar ukunmu, yi haƙuri, nasan nayi laifi amma wlhy tafiya nayi tun bayan bikin yaya Ali, kuma tambaya bah-bah kiji. Aunty Amarya sannu dazuwa kinji”.
Murmushi Jiddah tayi tana amsawa.
Hajia bah-bah ta katse musu jancen da faɗin, “Da wannam surutun da kika tsaresu dashi da alwala kika kaisu sukayi ga Aliyu can zai tada salla”.
“To bah-bah. Kunga kumuje to”.
Ɗakin Na’ima suka koma, domin yin sallar acan.
Bayan an idar da sallah Aliyu na gaisuwa da mutane wayarsa tayi ring, cirota yay daga aljihu ya duba, ganin Uncle yahya saiya faɗaɗa murmushinsa, bai ɗagaba saida ta tsinke sannan shi ya kirashi da kansa.
Daga can shima Uncle yahya murmushin yayi ya ɗaga, cikin girmama juna suka gaisa, Uncle yahya yama Aliyu bayanin halin da Abba ke ciki kusan kwana uku.
Sosai hankalin Aliyu ya tashi, yace, “Uncle aida an sanar mana, babu wata damuwa, ko yau aka kaita washe gari hakan ta faru ai dolene tafito, kuma koni aida nazo dubashi. Insha ALLAH gamunan zuwa bayan isha’i”.
“ALLAH ya kawoku, nagode a gaida min malam”.
“Zaiji insha ALLAH”.
Sosai lamarin ya zauna a zuciyar Aliyu, duk zuciyarsa taimasa babu daɗi, tausayin Abba sosai ya ɗarsu a ransa. Matsawa yay kusada malam dake zaune yana duba alƙur’ani ya sanar masa da abinda ke faruwa.
“Ya Salam, ALLAH yabashi lafiya, yasa kaffarane a gareshi, insha ALLAH zanje na dubashi nima”.
“Amin baba, to ALLAH ya bada iko, suma tare muke dasu sunzo gaisheku, daga nan zamu wuce mu dubashi insha ALLAH”.
“To masha ALLAH, hakanma yayi”.
Bayan an idar da salla malam yasaka Abba a cikin doguwar addu’a, wadda ta saka Aliyu jin daɗi sosai.
A cikin gida kuwa su Jiddah suna idar da salla sukazo suka gaida hajia bah-bah, cikin fara’a ta amsa musu tareda sanya musu albarka. Sanan tace suje su gaida su Gwaggo.
Sun fara zuwa sashen gwaggo amarya, itama ta tarbesu da fara’a, basu baro sashenba saida za’a kabbara sallar isha’i, sashen iya habi suka shiga, itama ta tarbesu da barkwancinta, tareda jin daɗin ganin Maimunatu ta bata cikin damuwa, saitaji Jiddah ta kwanta mata arai, nanma sunɗan jima dan saida sukai sallar isha’i, suka koma sashen Hajia bah-bah saboda kiransu da Na’ima tayi suzo suci tuwo.
Lokacin da Aliyu ya shigo gidan ya iskesu sunacin tuwo a falon hajia bah-bah. Bayan sun gaisa da bah-bah Na’ima ma ta gaisheshi, bisa kuskure Jiddah ta ɗago kai suka haɗa ido, gira yaɗan ɗaga mata yana nuna mata tuwon da ido.
Murmushi ta masa haɗe da ƙaramin gwalo, ya murmusa shima yana miƙewa domin zuwa gaida sauran matan gidan.
“Aliyu ka zauna a kawo maka tuwo”.
“A’a Bah-bah, Alhmdllh, kinsan ni ba cin abincin darenma nakeba kwata-kwata”.
Cikin hangame baki tace, “Wai wanan halin naka har yanzu baka barshiba Ali? Randa baka yini agidaba shikenan bazakaci abincin iyalinka ba?”.
“Bah-bah ai inacin na safe, rashin cin abinci dare abune mai ƙyau, yana ƙara lafiya inhar mutum zai iya jurewa”.
“A’a wlhy badaniba kam, yoni idan banci tuwo da darebama jinake tamkar banida lafiya a gidan nan”.
Dariya su Jiddah saukayi kaɗan, kujifa hajia bah-bah da wani batu, saikace wadda batayi salla ba.
Shidai Aliyu fita yay yana mata dariya. Bai daɗe sosai ba ya dawo yana faɗin, “Kumuje ku gaida malam akwai inda zamuje insha ALLAH”.
Maimuna da Jiddah suka miƙe, dan dama sungama cin abincin, harma sun wanko hannunsu da baki. Sallama sukaima Hajia bah-bah, suka koma ɗakunan su gwaggo suma sukai musu sallama, harda ƴar tsarabarsu ta kuka da ɗanyen kuɓewa da daddawa suka samo.
Saida sukai sallama a ƙofar falo aka basu izinin shiga sanan suka shiga, sun iske malam da Aliyu zaune suna magana, idan ka gansu dolene su baka sha’awa, harsun tsuguna daga farkon falon malam yace, “A’a ƴaƴana ku shigo mana ciki”.
Duk a kunyace suka koma gabansu sosai, kansu a ƙasa suka gaidashi, ya amsa musu cikin fara’a tareda tambayarsu gidan da rayuwar yau da kullum, sanan ya ɗora da nasiha a garesu su duka ukun mai ratsa jiki, yakuma sanya musu albarka tareda fatan alkairi a zamansu.
Suko kansu na ƙasa sunata amsawa da amin, yayinda ƙaunar tsohon da girmansa na ƙara yalwatuwa a ransu.
Baija zancen yayi tsawoba yace, “Aliy tashi kuje dare nayi, dan ALLAH ka gaidamin shi, ga wanan kabashi kafin nazo”.
Tashi Maimuna da Jiddah sukayi suka fita, dukda basu fahimci zancenba sunga yadace su basu waje ko akwai abinda zasu tattauna.
Bayan fitarsu Aliyu yace, “Zaiji insha ALLAH baba, amma kabar kuɗinka zan bashi injika insha ALLAH”.
“A’a karɓi wanan ai tsakanina dashine, kuma nima ina buƙatar ladan sarkin wayo” yaƙare maganar da tsokana.
Murmushi Aliyu yayi ya karɓi kuɗin, sanan sukai sallama da malam ya fito. Ya iske harsu Maimuna sun shiga mota, sai Na’ima dake tsaye ajikin motar suna magana.
Cikin samarin dake gefe ɗaya yazo ya buɗe masa motar da addu’ar sauka lafiya, dama sunzo suka gaida su Jiddah cikin mutuntawa.
Koda suka tafi a hanya bai musu bayanin inda zasujeba.
Ita kuma Jiddah gaba ɗaya hankalinta ma bakan hanya yakeba, game kawai take a waya tana sauraren hirarsu jefi-jefi suma, saida har suka shigo cikin anguwar sosai ne Jiddah ta ɗago kanta donson ganin inama suka dosane?.
Taɗan waro idanu da faɗin “Ai nan anguwarmune”.
Dariya Maimuna tayi ta juyo tana kallonta, “Wai da gaske dan ALLAH?”.
“Wlhy kuwa aunty”.
Aliyu na jinsu amma yaƙi tanka musu, a ƙofar gidansu Jiddah yay fakin sannan ya juyo yana kallon Jiddah.
“Ku shiga, zan shigo daga baya nima”.
Jikin Jiddah kuma sai yayi sanyi, cikin langaɓar da kai tace, “Basai gobe idan ALLAH ya kaimu kaceminba?”.
Ganin Maimuna ta fita saiya shafa kumatun Jiddah, shima cikin kwantar da murya yace, “Haka naje, insha ALLAHU zan kawoki gobenma kinji”.
Haɗiye ƙwallan daya cika idonta tayi, ta sauke ajiyar zuciya sanan ta fita. Har suka shiga gidan idonsa na kansu, saida suka ɓacema ganinsa ne ya sauke ajiyar zuciya da ɗaukar waya domin kiran Uncle yahya.
✨✨✨✨✨✨.
Su Umma duk suna tsakar gida zagaye da Abba da Uncle yahya ke bama Abinci.
Hakanne yasaka Jiddah yin turus tana binsu da kallo, dama ƴan uwanta basu tafiba? Idonta ta sauke akan Abba dake kwance ɗaɗɗaure da karan ɗori, sai Hajia Hindu dake gefe zaune ƴaƴanta zagaye da ita itama.
“Lah yaya Jiddah kece?” ‘Cewar walida data fito daga ɗakin Abba ɗauke da kwanon magani’.
Sauranma duk sai suka maido kallonsu ga ƙofar, Zarah tazo ta rungume Jiddah suka saki kuka tare, dan Jiddah ta fahimci gidansu babu lafiya.
Aunty Hanantu data hangi Maimuna ce ta miƙe tana faɗin “Ashe tare kuke? Shigo mana Maimunatu”.
Gwiwar Maimuna a sanyaye itama ta shiga ciki, dan alamu dai sun nuna babu lafiya kam.
Uncle yahya yayma Jiddah da Zarah magana sanan suka saki juna, Jiddah tazo gaban Abba ta durƙusa tana hawaye, “Abbanmu miya sameka?”.
Dukda haushinta da yakeji dan shi duk akanta yadora laifin, data zauna gidan Alhaji garba wanan bala’in da duk bai afka masaba, amma ya daure yace, “Wannan kukan ya isa haka ko?”.
Kasa tsayar da kukan Jiddah tayi, Maimunatu tazo gabansa itama ta durkusa ta gaidashi, da masa ya jiki?.
Amsawa yay cikin alamun yanajin jiki matuƙa, itama Jiddah ta gaidashi, ana cikin haka Uncle yahya daya fita suka shigo da Aliyu, dama su Umma duk sun kimtsa, gashi a kwai wutar nepa.
Tabarmar dake shinfiɗe a farkon shigowa wadda Jiddah taje ta zauna kusa da Abba Uncle yahya ya nunama Aliyu, kansa a ƙasa bai kalli kowaba ya zauna, Jiddah da gaba ɗaya hankalinta baya wajen saijinsa tayi kusa da ita, miƙewa tai tabar wajen, takoma inda Umma take tana sharar hawayenta.
Aliyu ya gaida Abba yana faɗin,
“لاَ بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللهُ .
La ba’asa tahoorun in sha’al-lah. (Ba komai, tsarkaka ce in ALLAH ya yarda).
أَسْأَلُ اللهَ الْعَظِيمُ، رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيكَ .(سبع مرات)
Asalul-lahal-‘azeem rabbal-‘arshil-‘azeem an yashfeek (7). (ina rokon ALLAH mai girma, Ubangijin Al’arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwa).
*_(MANZON ALLAH, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce; “Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya fadi wannan (addu’a) sau bakwai face ya sami lafiya”)_*.
_Falalar Da Ke cikin Ziyarar Mara Lafiya._
*_(ANNABI, tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, yace; “Idan mutum ya ziyarci dan uwansa Musulmi (da ba shi da lafiya) to yana tafiya ne cikin lambunan aljanna yana tsinkar ‘ya’yan itaciyarsu, idan ya zauna sai rahama ta lullube shi. Idan da safe ne Mala’iku dubu saba’in za su yi ta yi masa salati har ya shiga maraice. Idan kuma da maraice ne mala’iku dubu saba’in za su yi ta yi masa salati har ya wayi gari)_*.
Aliyu yaja doguwar addu’a ga Abba yana share kwallar da shima suka cika mada ido na tusayin Abban
Su Aunty Sauda na amsawa da amin.
Duk sun gaidashi da masa godiya, itama Umma ya gaidata tareda jajanta lamarin, Jiddah na jikinta tana hawaye, yayinda Umma keta shafa kan Jiddah alamar lallashi.
Aliyu ya janye idonsa daga jiddah ya maida akalar gaisuwar ga Hajia Hindu data cika tai fam da haushi, itama yay mata addu’ar samun afuwa.
Ta amsane kawai dan yayi mata mugun kwarjini, yanda takema mazajen su Aunty Nafisa yatsine-yatsine shi saita gaza masa, harshenta har sarƙewa yake wajen saurin amsa gaisuwarsa.
Basu baro gidanba sai goma da rabi, shima saida Uncle yahya yace yakamata su tafi dare yayi, ƴan dubiya daketa shigowa ma sinɗan rage saboda dare ya farayi.
Ƙiri-ƙiri Jiddah ta sanya kuka ita anan zata kwana, tun kowa na ɗaukar abin wasa har suka lura da gaske take, shikuma Aliyu baice uffanba yay musu sallama ya fice abinsa bayan ya ajiye kuɗin da malam yace aba Abba da wanda shima ya bashin, sai kayan marmari dasuka tsaya a hanya suka saya.
Uncle yahya ne yayma Jiddah jan ido sanan ta miƙe su Zarah suka rakota inda Maimuna da Aliyu ke jiranta.
Babu wanda ta kalla ta buɗe bayan motar tashiga tana cigaba da kukanta, Uncle yahya yabama Aliyu hannu sukayi musabaha da godiya shikuma Aliyu nama Abba addu’ar samun lafiya.
Saida suka bar ƙofar gidan su Zarah da Uncle yahya suka koma cikin gida.
A hanyama Jiddah kukanta takeyi, sai dai bamai sautiba, amma su Aliyu na jinta, Maimunatu ce kawai keta lallashinta da bata baki, amma sam Aliyu yaƙi tankawa, ita kuma shirunsa saiya kuma tunzurata takasa yin shiru kodan lallashin da Maimuna ke mata.
Suna isa gida itace farkon fita tabarsu a mota, da kallo kawai Aliyu ya bita, Maimuna zatabi bayanta Aliyu ya dakatar da ita, “Kinga Maimoon barta kinji”.
Cikin langaɓe kai tace, “Haba yaya yazakace a barta, kukafa takeyi?”.
Fitowa yay daga motar shima, “Tunda nace kibarta kawai ki barta, kukan nata harda na hanata kwanane, indai banda rashin son gaskiya taya za’a ƙara musu nauyi bayan wanda suke ciki, idan tayi haƙuri da safe zata koma insha ALLAH”.
Shiru kawai Maimuna tayi, amma ita harga ALLAH bataga laifin Jiddah ba, ko itace sai taso kwana ɗin, to amma ita kanta shaidace akan wannan halin nasa, zata iya rantsewa tunda akai aurensu bai taɓa barinta taje gida ta kwana ba, yini ma yata ɓata rai kenan. Dan haka sai bataja maganarba ta wuce sashenta.
Shima nasa ya nufa batare da yabi ko wannensu ba.
Tunda Jiddah ta shigo ko hijjab bata cireba ta kwanta a gado tana cigaba da kukanta, tausayin Abbansu da baƙincikin an hanata kwana cikin ƴan uwanta yake kuma tunzura kukan nata, ga haushin Aliyu, dan da ace yaso ta kwana ai zaice ta zauna, kuma babu wanda zai hana, rashin amincewar tasane ya saka Uncle yahya korota.
Tana nan kwance harya shigo, dukda taji ƙamshinsa ko motsi batayiba.
Kansa kawai ya ɗan girgiza, ya ajiye kofin shayinsa da Maimuna ta haɗo masa sannan ya zauna kusa da ita.
“Hauwa’u!”. ‘Ya kirayi cikakken sunanta abinda bai cika yiba, saboda sunan mahaifiyarsa kenan’.
Tsoro ya kama Jiddah, saboda jin yanda ya kirata a dake, tamkar ba shiba, hawayenta ta goge sanan ta amsa cikin rawar murya.
“Tashi zaune ki cire wanan hijjabin”.
Bata musa masaba ta tashin, takuma cire hijjabinta amma taƙi kallonsa.
Shima bai kalletan ba yace, “Tashi kiyi shirin barci”.
Tamkar munafuka haka ta tashi sum-sum zuwa bayi. Shikuma ya ɗau shayinsa yafara sha yanamai jin tausayinta da ahalinta, sosai lalurar Abba ta tsaya masa a zuciya, ita kuma tana neman ƙara masa zafi da ƙuruciyarta.
Yana shan shayin ta fito, kayan barcinta ta ɗiba ta dawo ta bayansa ta saka, nanma baice mata ƙala ba, amma da lafiya-lafiya ne cazai shi zai saka mata.
Tana gama shiryawa ta ɗaura zani tazo ta kabbara shafa’i da wutiri. Shidai Aliyu na zaune yana kallonta harta idar.
Sai kumbura fuska takeyi tana cigaba da share hawayen dake zubo mata, hannu ya miƙa mata alamar tazo, da tayi nufin noƙewa, amma sai taga rashin dacewar hakan, tadai turo baki sanan ta matsa kusa da gadon.
Hannunta ya kamo ya jawota zuwa jikinsa a hankali. Tana jinta kwance a ƙirjinsa saita kuma fashewa da sabon kuka.
“Oh ALLAH, ya isa haka mana Jiddah, ko sokike nima namiki kukan ne?”.
Kanta ta girgiza masa alamar A’a.
“To kiyi haƙuri kinji, insha ALLAH zai samu lafiya, Addu’a ya kamata muyi masa ai ko”.
“Amma shine kaƙi yin magana danace zan kwana?”.
Murmushi yayi yana shafa kanta, cikin kuma sanyaya murya yace, “To nayi laifi amin afuwa, amma kema kinsan hakan bai ƙyautuba, kwananki ai ƙarin wani nauyine, idan ALLAH ya kaimu saikije ki yini kinji”.
Da sauri ta kallesa, “Da gaske dan ALLAH?”.
Yanda tai maganar saita so bashi dariya, amma sai ya gimtse ya sumbaci goshinta yana faɗin “Insha ALLAH Qurratul ain, ALLAH dai ya basu lafiya, yakuma tsare gaba”.
“Amin ya rabbi, ammafa ni babu wanda ya faɗamin abinda ya faru”.
“Ni dai Uncle yace min ƴan fashine suka shiga, amma nasan za’a faɗa miki insha ALLAH, sai kinje gobe idan ALLAH ya kaimu”.
Shiru kawai Jiddah tayi, tausayin Abba nakuma ratsata.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Washe gari da wuri ta tashi ta haɗa breakfast, kunun gyaɗa sai soyayyan dankalin hausa data yankashi dogaye, saita soya miyar attarugu zalla da albasa, harta gama Aliyu bai shigoba daga massalaci dayaje. Tana gyaran bedroom ya leƙo.
Durkusawa tayi ta gaidashi, bai shigoba ya amsa daga inda yake tsaye a ƙofa, “Mizan tayaki dashine?”.
Kanta ta girgiza masa tana faɗin “A’a ka barshi, shara kawai zanyi”.
Kansa ya jinjina mata ya juya ya fita, ta bishi da kallo saida ya fice sannan ta miƙe taci gaba da aikinta. Ko morping yau ƙinyi tayi, tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta atanfa, kayan karin kumallon ta ɗiba zuwa sashensa. Shima har yayi wankan yana shiryawa ta shigo.
Idanu ta zaro tana ɗan dafe ƙirji, sanan ta marairaice fuska tana faɗin, “Dan ALLAH kayi haƙuri, banzo na haɗa maka ruwan wankaba”.
“Tab ai bazan haƙuraba yarinya”..
Durƙusawa tayi agabansa, “Dan ALLAH fa nace”.
“To saikin faɗi sunana”.
Babu shiri ta ɗago ta kallesa, yako yi kicin-kicin da fuska tamkar gaske, “Idan har baki faɗaba gwammajan ma bazaki jeba ko”.
Tuni ta fara hawaye, “ALLAH ni bazan iya faɗar sunanka ba”.
“To saikin faɗi abinda zaki ringa kirana dashi, danni nagaji da maidani surukinki da kikeyi”.
Wai shi dama haka wanan mutumin yake?
Jiddah ta ambata a zuciyarta dan takaici, harga ALLAH da burin zuwa gidansu ta kwana, hardasu mafarki, dan haka gara tafaɗa tasamu taje, kuma kasa tayi da kanta sanan tace, *_“Zauji ghaliy”_*.
Kafaɗunta ya kamo ya ɗagota zuwa jikinsa yana faɗin “Masha ALLAH Aglannissa, daga yau karna sakejin an ɓoyemin suna ana kwana-kwana”.
Kanta ta ɗaga amasa alamar amsawa.
Sakinta yayi ta taimaka masa ya ƙarasa shiryawa, sanan taje kiran Maimuna dansuyi kari……….✍????
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
????????karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*????????????????????????
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????