Innalillahi wainna ilaihirrajiun An sace wata Dattijuwa Mai Shekaru 67 a jihar Katsina
Innalillahi wainna ilaihirrajiun An sace wata Dattijuwa Mai Shekaru 67 a jihar Katsina
Zuma Times Hausa ta ruwaito Yadda Yan bindiga Suka sace wata dattijuwa mai shekaru 67 tare da danta a Karamar hukumar Ingawa ta jihar Katsina.
Katsina Post ta samu labari daga majiya mai tushe cewa, wasu ‘yan bindiga da ba a tantance yawansu ba, sun kai hari a garin Ingawa ta jihar Katsina, inda suka sace wata dattijuwa mai suna Gwaggo ‘Yar Ladi Turaki, wadda take da kimanin shekaru 67 a duniya.
An ce, Masu Garkuwa Da Mutanen sun shiga garin Ingawa da tsakiyar dare, kusan karfe 1:37 inda suka yi wa gidan da dattijuwar take tsinke suka tafi da ita da dan nata.
Shedun da sukaji afkuwar lamarin, sun ce barayin tin da suga shigo suka yi ta harbe-harben bindiga, daga bisani suka yi awon-gaba da mutanen biyu.
Majiyar sun ce masu garkuwa da mutanen bayan sun gama aika-aikarsu, sun kuma tafi hada danta mai suna Umar Aliyu Turaki mai kimanin shekaru 37 a duniya.
Daya daga cikin ‘ya’yan dattijuwar Ahmad Aliyu, shi ne ya tabbatar da afkuwar lamarin.
A yayin hada wannan rahoton, Jami’an ‘yan sandan jihar Katsina, basu ce komai ba game da lamarin, ko kuma rubuta wata takarda a hukumance ba.