Allah Yayiwa Maryam Rasuwa Ana Gobe Daurin Auren Ta Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raju’un
Innalillahi wa inna ilaihir raju’un Allah Yayiwa Maryam Lawan Rasuwa Ana Gobe Daurin Auren ta.
Innalillahi Wa Inna Ilaihit Raju’un, Ta Rasu Ana Gobe Aurenta
Bincike ya nuna cewa a gobe ne aka sa ranar auren marigayiya Maryam da angon ta Yunus, a garin Ofa dake Jihar Kwara.
Amma yau tace ga garin ku nan bayan fama da ‘yar gajeruwar jinya.
Kamar Yadda Kuke Gani Maryam Lawan Ta Rasu Ana Saura Baifi Awa 19 A Daura Mata Aure Ba.
Wannan Rasuwa Tata Ba Karamin Darasi Bane Akan Al’umma Baki Daya Domin Hakan Ka Iya Faruwa Akaina Ko Kai.
Dan Haka Idan Akwai Wanda Kake Gaba Dashi Har Kayi Alkawari Bazaka Taba Shiryawa Dashi Ba, Yakamata Kasan Dudiya Ba Matabbata Bace.
Yanzu Yakamata Mu Nutsu Mu Gyara Tsakanin Mu Da Allah, Watakil Bazamu Ga Goben Da Muke Tacewa Sai Gobe Sai Gobe Ba.
Yayin da take shirye shiryen daurin aurenta a gobe, yau ta rasu. Idan Har Yanzu Kuna Tunanin Wani Yayi Maku Laifi Wanda Baza Ku Iya Yafewa Ba Sai Kun Rama. Ku Tuna, Wannan Zai Iya Zama Kai.
Lallai Mutuwa Babbar Lakca ce, Allah ya gafarta mata kurakuranta, kuma ya saka mata da mafificin alkhairi.
Allah Yasa Mu Kyakykyawan Qarshe