Labarai

Innalillahi wa’inna illaihirra raji’un Ango ya mutu baya kwana 2 da daurin auren shi

Wani ango da aka bayyana sunan shi da alhaji Kabiru Mai Magani Saminaka ya mutu bayan kwanaki biyu da ɗaura auren sa akan hanyar sa ta dawowa Saminaka.

Angon ya mutu sakamakon haɗarin mota

Angon ya mutu ne a sakamakon mummunan haɗarin mota da faru dashi a yayin da yake komawa gida Saminaka, ƙaramar hukumar Lere jihar Kaduna daga Pambeguwa, a jihar ta Kaduna, a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Labarin mutuwar wannan sabon ango dai ya yaɗu cikin ƙanƙanin lokaci a kafafen sada zumunta na zamani musamman ma dai a kafar Facebook inda ‘yan uwa da abokan arziƙin mamacin suka dinga rubuta alhinin su da kuma addu’o’i.

Yaje ta’aziyyar mutuwa ne shima

Ance shima yaje wata gaisuwa ce ta mutuwa da aka yi a garin Pambeguwa dake jihar ta Kaduna a yayin da wannan haɗarin ya same shi kan hanyar komawa.

Wani mai suna Jamilu Suleiman Saminaka ya wallafa labarin mutuwar a shafin shi na Facebook inda ya bayyana cewa kwana biyu kenan da ƙara auren Alhaji Kabiru Saminaka. Ya bayyana cewa ya mutu ne akan hanyar sa ta dawowa daga wajen wata ta’aziyya da yaje Pambeguwa.

Kwanan shi biyu kenan da ƙara aure

“Innalillai wa’inna ilaihi raji’un. Bayan kwana biyu da karin Aurenshi Allah ya karbi rayuwarsa a hanyarsa tazuwa ta’aziya Garin Pambegua.

Allah yajikan Alh Kabiru bilhakki
Mai magani, ya karbi shahadarsa Alfarman Manzon Allah S. A. W. Mukuma idan tamu tazo Allah yasa mucika da Imani ” inji Jamilu Sulaiman.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button