Labarai

Yanzu Yanzu Nan Kotu ta Tisa Keyar Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid bawa gidan Yari.

Yanzu Yanzu Kotu ta Tisa Keyar Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid bawa gidan Yari.

Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito Mai shari’a Chizoba Oji na wata babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja, ya bayar da umarnin aike shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC zuwa gidan yari bisa laifin ƙin bin umarnin kotu.

Alkalin ya kuma umurci Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar da ya tabbatar da an aiwatar da hukuncin. Oji ya bada umarnin ne a ranar 28 ga Oktoba, in da a ka raba wa manema labarai a Abuja kwafin umarnin.

Hakan ya bayu ne bisa rashin biyayyarsa ga kotu, ya kuma ci gaba da bijirewa umarnin kotun da ta bayar a ranar 21 ga Nuwamba, 2018.

Kotun ce ta umarci EFCC, Abuja da ta mayar wa wanda ya shigar da korafi motsa kirar Range Rover (Supercharge) SUV da kudin ta ya kai Naira miliyan N40.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button