Labarai

Innalillahi- yadda Ango ya rasu sa’o’i kadan bayan daurin auren sa

Wani matashin ango mai suna Shehu Lili Kofar Atiku ya rigamu gidan gaskiya sa’o’i ashirin da hudu bayan an daura maaa aure a jihar Sokoto.

Wani abokin angon, mai suna Shamsudeen Buratai shine ya tabbatar da aukuwar lamarin. Shafin LIB ya rahoto.

Angon ya rasu sa’o’i kadan bayan an daura masa aure

A cewar Buratai, an daura auren angon ne a ranar Lahadi 5 ga watan Oktoba 2022, da misalin karfe biyar na yamma a unguwar Kofar Atiku sannan ya rasu da safiyar ranar Litinin.

“Shehu abokina ne tun na yarinta kuma dan’uwa na tsawon fiye da shekara 30. Yana fama da matsananciyar malaria wacce take taso masa duk lokacin sanyi. Kamar kowace shekara, ciwon nasa ya taso masa a bana a cikin watan Disamba, inda ya sha magunguna ya samu lafiya.” A cewar sa.

“Da safiyar yau misalin karfe tara na safe, ya fito inda muka gaisa yadda muka saba. Kwatsam kawai sai ya fara jin wani bakon yanayi inda yace manan yana tunanin ciwon malaria ne yake kokarin dawo masa. Kafin mu yi aune kawai har ya fadi kasa, shikenan karshen sa kenan.” Inji Shamsu.

Tuni dai har an binne mamacin bisa yadda shari’ar musulunci ta tanada.

Muna addu’ar Allah (SWT) ya jikansa da rahama ya gafarta masa, yasa aljannah ta zama makomana gare sa, mu kuma idan tamu ta zo yasa mu yi kyakkyawan karshe na cikawa da Imani. Ameen summa Ameen.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button