Labarai

Allah sarki Kalli hotunan katafaren gidan da gwamna Zulum ya ginawa wata malamar primary mai hazaka

Gwamna Babagana Umara Zulum Ya Kammala gina Gidan Malamar nan ta primary a Jihar Borno Domin Kasancewar ta Mai Kwazo cikin malaman.

Za ku iya tunawa da Malamar da suka hadu da Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum a 2020 a wurin aikinta inda gwamnan yaje makarantar da sassafe domin duba halin da makarantar firamare da take aiki a ciki?

Obiagelli Mazi wacce yar asalin jihar Abia ce da ta yi bautar kasa a jihar Borno wanda Kuma daga bisani ta cigaba da zama a Jihar, duba da irin kwazonta yasa aka dauke ta aikin karantarwa a makarantar primary wanda yanzu ta shafe tsawon shekaru 31 a Jihar.

Bayan da Gwamnan ya je makarantar bai samu kowa daga cikin malamai ba sai ita, wanda hakan yasa gwamnan ya gana da ita, nan take aka ba ta wasu kudade, sannan daga bisani aka kara mata girma daga Malamar Aji zuwa mataimakiyar shugabar mata, kuma a yanzu an yi mata kayautar sabon gida da aka gyara tare da sauran malamai a Maiduguri.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button