JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 24

Umma tace “Toh je ki dauko abinda xaki dauka mu wuce yanxu” Abuturrab ya bude ido da sauri yace “Umma ta fara karatu fa” Daga kasa Umma ta kallesa har sama sannan tace “Is that so?” Ya sunkuyar da kansa yace “Eh Umma, tare xa mu koma kano da ita” Lkci daya hawaye ya kawo idon Jiddah tana kallonsa, Umma tace “Toh shkkn, Allah ya taimaka, dama anguwan na shigo shine nace bari in karaso mu gaisa, i will take my leave now, tunda na same ku lafiya Alhmdlh” Yace “Umma da wuri haka, ki bari after magrib….” Ta katse sa tace “Ohk da magariban xa ku dau hanyan kanon kenan?” Shiru yayi bai ce komai ba, ta mike tana kallon Jiddah tace “Toh xan koma jiddah” Kasa dago kai Jiddah tayi, Abuturrab yace “Toh mun gode Umma, Allah ya kara girma” Jiddah ta share idonta a hankali tace “Sai anjima Umma” Duk da tausayinta da Umma ta ji sosai amma sai bata wani nuna ba ta nufi kofa tace “In dai xan xo ki dinga kuka gwara kar in sake xuwa, kusan sati biyu ai ya kamata ki sake haka ko…” Jiddah ta bi ta da kallo hawaye na sauka idonta, wani kallo Abuturrab yyi mata sannan ya bi bayan Umma, Umma bata wani sauraresa ba har ta hau motar ta ta wuce, ya shafa kansa ya bi motar da kallo, juyawa yayi ya koma cikin compound din, bai tadda Jiddah a parlon ba, hakan ya sa ya wuce sama ya bude kofar dakinta ya shiga yaga bata ciki, shesshekar kukanta ya ji a bandaki, ya karasa kofar ya murda yaji ta kulle da makulli, ya hade rai yana knocking kofar yace “Ohh har kuka kika samu damar yi kenan, toh bude kofar kar ki bari in bude da kaina” Kin bude kofar tayi ta kara rushewa da kuka kamar an aikota, bude baki yyi da mamaki, duk yanda yayi Jiddah ta bude kofar kin budewa tayi, har dai ya dawo kwantar da murya amma kamar yana dada tunxurata, banda kuka babu abinda take, kallon agogo dake nuna shiddah da few minutes yayi ya xauna gefen gado yayi wani sigh, a ranan ya ke son komawa kano but he just can’t go like that…. spare key din bandakin ne ya fado masa ya mike da sauri ya fita xuwa bangarensa, sai bayan da ya dauko ya koma dakin ya fara addu’an Allah yasa ta cire makullin daga jikin kofar, yana sa makullin kuwa ya ki budewa alamar makulli na jiki, rungume hannunsa yayi yace “Baxa ki bude kofar ba malama, kin san kina bata min lkci kano xan wuce?” Bai ji alamar xata bude kofar ba, but kukan nata da ya daina ji yasa yaji hankalinsa ya tashi bayan ya tuna da vow din da tayi kwanki wai xata kashe kanta, ya ga fa kamar ba seti gareta ba, ya kwantar da murya yace “Jeeddarh…” Nan ma bata amsa ba, rasa abinda xai yi yyi, a haka har aka kira magrib, hankalinsa ba a kwance ba ya tafi yyi alwala a parlor sannan ya wuce masallaci, ana idar da sllh da ya shigo gida dakinta ya kara shiga, har lkcn tana cikin bandakin, jingina yayi da kofar a hankali yace “Jeeddarh” bata tanka sa ba, hakan yasa yace “Ohk to ki gaya min me kike so, ni kuma xan maki” Jiddah dake durkushe jikin kofar ita ma, ta daga kai a hankali jin abinda yace, ya kara kwantar da murya yace “Kin ji?” Tana goge idonta tace “Gidanmu nake son in koma” Buda ido yyi da mamaki jin abinda tace, yace “Wani gidan naku?” Tace “In da ka gan ni mana” Rungume hannunsa yyi, bai san lkcn da yayi murmushi ba yace “Can hayin rigasa?” Tace “Ehh” yace “Kin tabbatar?” Hawaye ya silalo idonta tace “Ehh” Yace “Tohh shkkn bude kofar, sai mu tafi” Tana goge idonta tace “Ni ban yarda ba” Yace “Kinga ina karya? Da gaske nake xan kai ki, ba dai har kin gaji da xaman gidan nan ba” Tace “Ehh, na gaji… Wajen Baabarmu xan koma” yace “Toh bude kofar, dare na yi” mikewa tayi a hankali ta bude kofar, ya koma gefe yana jiran ta fito, tana fitowa suka yi ido hudu da sauri ta sunkuyar da kanta, ta wani sha kunu, har hakan ya so bashi dariya, yace “Toh hada kayan na ki” Kallon jakan da Umma ta bata tayi sannan ta nufi gun jakar, yana kallonta ta fara hada kaya, har ta gama ta daga jakar sama, yace “Ina ma kika ce in kai ki?” Tace “Gidanmu nace” yace “Toh tafi parlor da jakar ki jirani” Jan trolley din ta fara yi ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fita sannan shi ma ya fita ya tafi bangarensa, Jiddah na parlor ta xauna kasa tana jiransa, banda wasa da yatsunta babu abinda take har ya sakko rike da makullin motarsa, ba tare da ya kalleta ba yace “Mu je” mikewa tayi tana jan trolley din ta bi bayansa, bakin motarsa ta tsaya ganin ya bude Booth ta saka trolley din a ciki, sannan ta tafi ta bude gaban motar ta shiga, ya tada motar suka bar gidan. Tun jiddah na kalle kallen hanya ko xata ga sun shigo titin anguwar tasu har ta fara ganin daji babu alaman gidaje, driving kawai yake da speed amma kuma da nutsuwa, marairaicewa tayi ganin kamar sun fita gari tace “Ina xa mu je?” Ko tanka ta bai yi ba hakan yasa bata sake ce masa komai ba, sai hawaye, duk da baccin da ta dinga ji har suka shigo garin kano wajajen karfe sha daya bata yi baccin ba, hotel din da ya ke sauka ya tafi yayi lodging yayi ordering abinci, bin sa kawai take yana tafiya har suka isa dakin da aka basa, tana shiga dakin ta jingina da bango ya kulle kofar ta dinga bin dakin da kallo, ya ajiye makullin motarsa da wayoyinsa gefen gado ya shiga bandaki ya dauro alwala ya fito, ita dai tana ta tsaye, ya shimfida darduma yayi sllhn isha, bayan ya idar da sllh aka yi knocking kofar, mikewa yayi ya isa kofar ya bude, ya amshi abincin da aka kawo sannan ya kulle kofar, shayi ya sha, sai pepper soup din hanta bai bude takeaway din shinkafar ba ya mike ya dau wayarsa yayi dialing number Aneesah don tun yana hanya take ta kiransa, fita yyi dakin ya kulle daga waje, Jiddah ta bi sa da kallo, xaunawa kasa tayi hawaye na taruwa idonta bayan kusan minti sha biyar ta mike ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito tayi magrib da isha, kwanciya tayi kan darduman nan da nan bacci ya dauketa. Karfe sha biyu da mintuna Abuturrab ya shigo dakin abincin ya fara dubawa ko ta ci ya ga bata ci ba, ya xauna gefen gado ya sa hannu ya buga gefen kafarta bude ido tayi ganinsa ta mike xaune da sauri, babu yabo bbu fallasa yace “Dauki abincin ki ci” Tace “Ni na koshi” wani kallo ya mata, ta jawo abincin ta bude ta fara turawa, bai takurata sai ta ci da yawa ba, bayan ta rufe sauran yace “Tafi ki wanke bakin ki kiyi wanka” Bata iya ta ce masa komai ba amma ji tayi kamar ta fashe da kuka, ta mike ta cire Hijab din jikinta ta linke ta ajiye ta bude jakarta ta ciro sabulu da sponge, toothpaste da toothbrush, xata wuce bandakin yace “Tawul din fa?” Dawowa tayi a hankali ta kara bude jakar ta dau towel dinta ta wuce bandakin, ta kusa minti biyar tsaye bayan ta gama wankan ta rasa yanda xata fito daure da towel, gashi bata shigo da hijab ba, gajiya tayi da tsayuwa daga karshe ta bude kofar a hankali tana lekan dakin, bata gansa a dakin ba, ta fito da sauri, ta fiddo kayan da xata sa da turarruka da mai, tana rufe jakar ya shigo dakin, kasa dago kanta tayi ya rufe kofar, bata yarda ta kallesa ba ta mike ta dau kayan nata ta shiga bandaki, sai da ta gama sakawa sannan ta fito ta mayar da turare da cream din cikin jaka ta tafi kan darduma ta xauna, yana xaune can gefen gado ya kalleta yace “Tashi ki kwanta” sunkuyar da kanta tayi, sai kuma ta mike ta tafi can karshen gadon ta kwanta, ba a dau lkci ba kuma bacci ya dauketa, karfe daya nayi ya kashe laptop dinsa ya ajiye sannan ya dau pillow ya ajiye a kasa ya kwanta. Da asuba ana idar da sllh Abuturrab yyi wanka ya shirya, tun ana sllh Jiddah ta tashi amma bata juya ba balle ya san idonta biyu, tana jinsa yana shiryawa har ya gama, kallonta yayi ya buga gadon yace “Ke baki sallan asuba ne dama?” Mikewa xaune tayi ba tare da ta yarda ta kallesa ba ta wuce bandaki, kwance ta gansa da ta fito idonsa a lumshe ta tada sllh bayan ta idar ta kwanta kan darduma, karfe bakwai da few minutes Abuturrab ya tashi, tashinta yyi ta mike xaune da sauri, yace “Anjima idan anyi knocking ki bude kofa ki karbi abinda aka kawo, apart from that ban ce ko bakin kofar ki je ba, kin ji me nace maki??” A hankali tace “Toh” Sai da ya fara kunna TV dake dakin ya kai tashar hausa sannan ya dau jakarsa ya nufi kofa ta bi sa da kallo har xai fita ya juyo, da sauri ta dauke idonta daga kallonsa, yace “Saura ki bude kofar a haka baki sa hijab ba idan aka kwankwasa” bai jira cewarta ba ya fita dakin ya kulle kofar, mikewa tayi ta hau saman gado ta ci gaba da baccinta. Karfe takwas taji an kwankwasa kofa, mikewa tayi har ta nufi kofar haka ta dawo da sauri ta dau hijab da ta daura kan riga da wandon jikinta na bacci, sannan ta nufi kofar ta bude, abinci aka kawo mata ta amsa tare da godiya ta juya ta koma cikin dakin, sai da tayi wanka ta shirya sannan ta yi breakfast din da aka kawo mata. Throughout ranan haka ta yini ita kadai dakin sai dai tayi kallo idan ta gaji tayi bacci, tana farkawa ta ci gaba da kallon, abincin lunch da aka kawo mata ma sai kusan la’asar ta ci, karfe biyar da rabi tana tsaye bakin window taji an bude kofar, da sauri ta juyo, shigowa dakin yyi, ya ajiye ledan hannunsa,duk da wayar da ta gani kare a kunnensa hakan bai hanata ce masa Ina yini ba, ya xauna gefen gado ya ci gaba da wayarsa, bayan ya gama ya tashi ya fita ta bi sa da kallo, sannan ta kalli ledan da ya ajiye. Sai bayan magrib ya shigo tana xaune saman darduma ta bi sa da kallo har ya xauna ya bude ledan da ya shigo da shi ya fara cin naman tsiren dake ciki, dauke idonta tayi bayan few minutes tace “Kace min gidanmu xaka kai ni, baka kaini ba shine xaka kawo ni nan, ni wllh ka maidani wajen Babarmu” Bai tanka ta ba, hakan bai hanata maimaita abinda ta fada ba, ya juya ya kalleta yace “In maida ke wajen Baabarku?” Tayi shiru bata ce komai ba, mikewa yayi ya koma gefen gadon ya xauna yana facing dinta yace “Tambayarki nake?” Ta sunkuyar da kanta tace “Ehh kai kaini wajenta” Yace “Ohkk… amma bari in tambaye ki” Ta dago idanuwanta ta kallesa yace “Kina tunanin xamana da ke ba burden da damuwa bane a gareni?? Ina nufin baki san cewar rayuwar ki tare da ni nauyi babba na daura ma kai na ba da rashin kwanciyar hankali? Do you think ko matata ba iyakar abinda xan mata nake maki ba? What’s so important about staying under same roof with you? Kina tunanin ni ajin ki ne da nake kula ki nake kula al’amuranki? Toh bari ki ji, ni din nan da kike gani ba ajin ki bane, ina taimakon ki ne saboda Allah ba don komai ba, gidan naku da kike cewa in mayar da ke an gaya maki baxan iya daukan ki in maida ke ba duk abinda xai faru dake ya faru? Toh bari ki ji, sau da yawa tausayi kan canxa mutum, banda haka bani da abinda xan yi dake a waje daya, and i mean it, ni ba ajinki bane” Yana fadin haka ya mike ya fice daga dakin, ta bi sa da ido kafin ta sunkuyar da kanta.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button