JIDDAHTUL KHAIR 26
Har karfe daya da wani abu na dare Jiddah bata yi bacci ba, abu bai ta6a tsaya mata rai irin abubuwan da Abuturrab ya gaya mata ba, gashi har sannan ko digon hawaye bata yi ba, amma abun ya ki barin xuciyarta, da yake a kasan darduma ta kwanta kuma bai bi ta kanta ba yyi kwanciyarsa saman gado, ta mike xaune a hankali ta daura kanta bisa gwiwanta, sai a sannan hawaye ya shiga sauka idonta, gaba daya taji da ma ta hakura da aurenta da Iliya, taji ta gwammace gwara ta koma gidansu komin abinda xae faru, taji gwara ta gudu kawai, daga kai tayi hawaye na sauka idonta ta kallesa, duk da wutan dakin a kashe yake, tana ganinsa kwance saman gado. Da safe bayan ya gama shirinsa haka ya fita ba tare da yace mata komai ba, tun bayan da ta gaishesa bata ma san ko ya amsa ba har ya fita bata kalli inda yake ba ita ma, sae dai bata ga ya dau jakar laptop dinsa ba. Bayan fitarsa da minti kusan talatin ta mike ta dau Hijab dinta ta saka ta bude kofar dakin ta fita, a reception din hotel din ta gansa xaune da shayi a kan table din gabansa idonsa a kan screen din wayarsa, sosai gabanta ya fadi tayi still a inda take, dago kai yyi suka hada ido, tana ganin haka ta nufi kofar fita da sauri, da ido ya fara bin ta da mamaki, lkci daya kuma ya mike ya bi bayanta, fita tayi compound din hotel din, ya fara kalle kalle sbda baya son attention, luckily babu mutane haraban hotel din, hakan ya kara masa kwarin gwiwan bin ta ya fixgota ta fashe masa da kuka tace “Ni ka kyaleni in yi wucewata, wllh baxan xauna a nan ba wajen Baabarmu xan koma” Bai saurareta ba ya ciro makullin motarsa a aljihu ya ja ta xuwa parking space da motarsa yake ya bude back seat, turata ciki yyi ya kulle motar, sannan ya jingina jikin motar ya rungume hannunsa yana imagining… assuming baya xaune downstairs tafiyar xata yi da gaske, Jiddah ta dinga rusa kuka cikin motar, ya fi minti 7 a tsaye kafin ya bude motar ya shiga ya kulle, can gefe ta koma tana shessheka taki kallonsa, yana kallonta fuskarsa a daure yace “Ina xa ki tafi kika ce?” Cikin rawar murya tace “Gidanmu mana” Yace “Auren xa ki je a maki da mashayin saurayin naki?” Tace “Ehh” da mamaki yake kallonta, tace “Ni kawai ka mayar da ni, na yarda xan auresa din” Dauke kansa yayi bai ce komai ba, bayan few seconds ya kalleta yace “Toh ba kaduna muke ba yanxu, nan kano ne, ki jira idan mun koma kaduna sai in mayar da ke gidan naku da kaina ba sai kin tafi ke kadai ba, kin ji?” idonta ta fara gogewa tace “Yaushe xa mu koma kadunan?” Yace “Aiki nake yi a nan, sai ranan alhamis” Wani hawayen ya taru idonta, yana kallonta yace “Kin ji abinda nace?” Hawayen ya xubo mata tace “Har sai alhamis kuma?” Yace “Jibi ne alhamis din ai” Ta sunkuyar da kanta tana goge hawayenta, shi dai kallonta kawai yake ko kiftawa babu, a hankali tace “Toh” Bai kuma cewa komai ba, ya juya ya bude motar ya sauka yana dubanta yace “Sauko” Ba musu ta sauko daga motar tana wani kumbure kumbure, yana kallonta yace “Wani man kike shafawa?
” Ba tare da ta kallesa ba tace “Wanda ka siya min mana” Bai ce komai ba, bayan few seconds yace “Toh kar ki kara shafawa” ta kallesa yace “Mu tafi ciki” Ba musu ta fara tafiya ya bi bayanta, ba komai ya sa ya tambayeta ba sai ganin yanda ta kara haske, which he don’t like, ko kadan baya son idan mace ta doso waje ayi noticing dinta, haske kuma na daya daga abinda yake sa ayi noticing mace a waje, ita kam Allah ya hore mata wannan, juyawa tayi ta kallesa suka hada ido ta ci gaba da tafiya yana biye da ita, har suka shiga reception din sannan taji yace “Tafi ki shirya ina jiranki, minti ashirin na baki” Bata ce komai ba ta wuce sama ya bi ta da kallon gefen ido, kallon agogon wrist dinsa dake nuna karfe takwas da rabi yayi, he will be piloting around 10:30, shi kuma bai son xama daki tare da ita shi ya sa ya sakko ya xauna reception din. Karfe tara dai dai Jiddah ta sakko, tun da ya kalleta sau daya ya dauke kansa… Abaya ce baki a jikinta, i need not to say yanda kayan ya haskata, sai karamin jaka da takalmin kafarta same color, ta iso table din da yake xaune, lkci daya kamshin turaren da ta saka ya baxa wajen, ya fi minti biyu bai ce komai ba, can dai ya kalleta yace “Baki xo da Hijab bane?” Ta girgixa masa kai kawai, Bai kuma ce mata komai ba, ta xauna d’an nesa da shi, sai a snn yace “Me xaki ci?” Tayi shiru bata ce komai ba, chips and egg ya sa aka kawo mata sai shayi, ya sa ta tafi sama tayi breakfast din, ta mike ta wuce, ya bi ta da kallo, lkci lkci yake duba agogon hannunsa dake nuna after 9, tashi yyi ya wuce sama, ya tarar ta gama, jakarsa ya dauka yace “Kina bata min lkci Malama” Tashi tayi ta bi sa suka fita ya kulle dakin, tana biye da shi har suka iso gun motarsa, ya ajiye jakar a back seat ya
shiga maxaunin driver ya tada motar, xagawa tayi a hankali ta bude front seat din ta shiga ta xauna, warming din motar yayi suka fita haraban hotel din ya dau hanyar Airport. Abuturrab ya samu discount wajen yankar mata ticket din Business class, wanda hakan yasa take cikin boarding group na farko, duk wanda ya ga jiddah a lkcn xai xata ba farkon boarding din plane dinta bane, she is so calm, but deep inside her she is so so Afraid, bata ta6a tunanin haka jirgi yake da girma ba, snn bata ta6a mafarkin xata ga jirgi ido da ido ba balle har ta shiga wataran, kuma tunda ta shiga jirgin ta xauna idonta ke kasa, sai ka lura da ita sosai xaka gane a tsorace take, daya daga flight crew member ce ta nufota tana murmushi da ladabi tace “Ina kwana Hajiya…” Jiddah ta daga kai ta kalleta a hankali tace “Ina kwana” Cabin crew din na murmushi ta xauna kujeran gefenta tana kallonta ta buda mata ido sannan ta shiga fastening Seat belt dinta, wanda da alama Abuturrab ne ya sa ta gwada mata yanda zata saka seat belt din, Jiddah dai kallonta kawai take har ta gama sakawa, Flight crew din tace “Toh saka naki haka” Ba musu jiddah tayi yanda taga tayi, matar tayi murmushi ta yi unfasten din nata ta mike tace “Toh ki cire, sai jirgi xai tashi xa ki saka, Allah ya sauke mu lafiya” Jiddah ta cire, matar ta kuma sakar mata murmushi ta juya ta wuce, jiddah ta bi ta da kallo don kayan jikinta yayi mata kyau sosai ba kadan ba, ba su fi ashirin a Business class din ba, kowa kuma harkan gabansa yake, tunda wani mutumi ya xauna gefenta ta xama so uncomfortable, ga kamshinsa da ya cika wajen, shi dai bai kalleta ba sai operating din wayarsa da yake yi attentively, bayan minti ashirin duk passengers din sauran class din suka gama boarding plane din, Nan aka fara announcing ayi fastening Seat belt, ganin kowa na saka nasa ita ma ta fara kokarin saka nata, amma sai ta kasa sakawa sai fama da belt din take, sai a sannan mutumin dake gefenta ya kalleta ta gefen ido, ganin ta rasa yanda xata saka, ya kai hannunsa ya saka mata, bata iya ta kallesa ba kuma bata ce komai ba, a haka jirgin ya fara tafiya, dukar da kanta da yaga tayi na kusan minti 5 yasa ya sake kallonta yace “Are you okay?” Da sauri ta dago, dai dai nan jirgin ya daga, ta rufe bakinta hankalinta a tashe tace “Amai nake ji wllh” da mamaki yake kallonta yace “Amai?? Ohk hold it for a while” Ita dai hannunta na bakinta tana gyada masa kai, he gets she might be prone to motion sickness…