NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE
NOOR ALBI COMPLETE HAUSA NOVEL BY MAMUHGEE
PAGE 1
Bismillahir-rahmanir Raheem
Kokarin komawa ta zauna Kan kujerar robar Dake gaban wheelchair dinda mahaifinta yake zaune akai tayi bayan ta aje cup din data Gama basa magani abaki Kan qaramin table din Dake gurin ta dago idanuwanta ahankali cikin nutsuwa ta kallesa batareda tace komaiba ta tsawon mintina biyu kafin ta Dan motsa Bakinta cikin wata nutsuwar ta sakar Masa murmushinda yake narkarda zuciyarsa da tsananin tausayinta da qaunarta Dan kuwa yanajin radadi da zafin dukkanin murmushinta Wanda yariga yasan ba komai cikinsa face damuwa, kadaici,maraici da rashin uwa dakuma rashin uba dukda shi uban gashi a raye Amma tamkar baya raye yake Dan baida wani abun dayake iya yimata bayan nuna Mata zallar qaunarta daga zaune sai kwance.
Ganin irin kallon dayake matane Wanda koyaushe yake nuna gazawarsa amatsayi na uba
Ita Kuma Bata taba yimasa kallon ya Gaza din sbd tasan hakan qaddararsu ce su duka tun daga kan mahaifiyarta da Bata Raye har Momy wadda take ganin itace tafi cutatuwa ato kowane bangare na rayuwarsu.
Sauke idanuwanta tayi daga kallonsa tareda Kai hannu ta zari tissue Mai Dan yawa tahau goge Masa gefen rigarsa da ruwan maganin masu kala suka zuba ta sauke siririn numfashi ahankali ta bude Baki ta furta”
Abba!!
Kadaina kallon kanka da yanayinka amatsayin ka cancanta hakan sbd abunda yafaru,
Kadaina kallon kanka amatsayin Wanda ya lalata rayuwar yarsa yakasa Mata komai bayan Kaine komai nawa,
Nice rabon haihuwata da zuwana duniya ya tarwatsa kwanciyar hankalin rayuwark……
Rintse idanuwa da yayi cikin Jin dacin zancenta yayi daidai da dafata da akai da hannuwa biyu a kafadarta Dan hanata qarasa zancen.
Ahankali ta sauke ajiyar zuciya batareda ta dagoba
ta Dan sake sauke numfashi Mai sanyi da rashin sauti kafin ta waiwayo da kyakkyawar fuskarta
idanuwanta basu sauka Kan Yar uwarta Kuma Antynta data dafata sai akan Momy suka fara sauka wadda ke tsaye bayan Anty SA’ADAH din kyakkyawar fuskarta ta Kamar yanda tasanta tun tashinta a daure Babu sakewa Babu fushi sai yanayinta dake sake nuni da har lokacin kallon Rabon daya lalata rayuwarta data yarta take Mata.
Ahankali ta dauke kallonta daga kanta tana Mai Dan Sunkuyar da kanta ahankali tareda miqewa tsaye daga gurin ta raba gefen Anty Sa’adah ta koma bayanta ta tsaya cikin tattausan muryanta batareda tasake kallon momynba cike da biyayya tace”
Barka da safiya Momy.
Kamar yanda tasani tun tasowarta harzuwa shekarunta na yanzu datake dasu Momy Bata taba amsa gaisuwartaba wanda hakan sabone agareta Kuma baya damunta Kamar yanda ko so daya Bata taba tsallake ranar gashetaba Dan kuwa Bata taba ganin laifi ko Jin haushin momynba,
Kallon uwa Kuma mariqiya take Mata tareda wani girmanta Mai tsanani datake gani.
Qarasowa cikin palon gabaki daya momyn tayi cikin tafiyar nutsuwa ta Isa Kan kujerar dake gurin ta zauna sai alokacin ta kallesa dakyau murya natse tace”
Barka da safiya!
Shiru sukayi dukkaninsu sbd sanin ba wani iya mgn Abban keyiba musamman da kwana biyun jikin nasa ke Dan sake rikicewa duk da tsawon shekaru masu yawa daya debo daga zaunen da kwancen.
Saida yamata kallon mintuna kamar yanda yasaba yimata kullum kafin ya iya daga kansa ahankali cikin wani irin yanayi na sanyi da jikin dayake Dan ji.
Numfashi Mai sanyi ta sauke ahankali kafin ta dauke kallonta daga kansa cikin sanyin murya tace”
Dr Abbakar yakira akan Yana hanyar qarasowa kana tunanin hakan zai…..
Dakatawa tayi da maganar Tareda yin shiru kafin ta Dan waiwaya ahankali ta kalli inda Sa’adah ke tsaye batareda tace komaiba
Suna ganin hakan suka nufa kofa itace agaba jikinta na qara bayyanarda sanyinta Amma taurin zuciyarta na sake boye hakan.
Kai tsaye dakin anty Sa’adah din Sa’adahn ta jata suka shiga ta nuna Mata bakin gado da ido tana cewa”
Zauna anan Ina zuwa.
Fita tayi ta nufa kicin ta duba abincin da akai Karin safiya dashi taga sauran doyar Dake cikin kular da alama ba’aciba
Ta dauka plate ta zuba Mata farar doyar tareda soyayyar jar miyar dataji albasa ta bude Dan qaramin fridge dinsu daya Dan tsufa Amma Yana aiki ta dauko Mata pure water daya masu sanyi ta nufo dakin ta qarasa har gefenta ta zauna ahankali tareda Kiran sunanta cikin tattausan lafazin dake nuni da irin tsananin son datakewa Yar uwar tata Wanda bayan Momy data haifeta Babu Wanda takeso kamarta.
LAYLAH Takira sunanta cikin kulawa da sautin Mai Dan girma Kai tsaye tace”
Ahakan Zaki zama likitan kina skipping lokacin cin abinci?
Cinye ki tashi kije ki gyara palon Abba kafin baqinsa suzo.
Kamar yanda yake dabiarta dagowa tayi ta kalli Anty Sa’adah din kadan tareda Dan yaqen guntun murmushi tana daukan plate din tafara cin abincinta a natse.
Qura Mata ido anty Sa’adah tayi tana qarewa kyakkyawar fuskarta zuwa yanayin sanyi da nutsuwarta kallo,
Duk yanda kakai qarshe da sanin halin mutum da yanayinsa bazaka taba iya gane halinda zuciyar ZAINAB LAYLAH take cikiba,
Yarinyace Mai tsananin zurfin ciki da wata irin juriya da tawakkali,
Bata bayyanarda fushi ko bacin Rai,
Batada hayaniyar da zaka Kuma gane farin cikinta
Abu daya ke bayyanarda halinda zuciyarta ke ciki ko yanayinta shine murmushinta Wanda shine abinda ke bayyanarda zallar ‘dacin datake ciki.
Mahaifinta yayi auren sirri da Yar uwar dangin nesa sosai ta Babban amininsa da baida tamkarsa sun taso tare sun girma tare tarin Arziki,suna da daukaka ya rage kusancinsu sbd nisa da aminin nasa yai Masa bawai Dan sun rabu ba haryanxu suna tare matuqar Aminin nasa Yana qasar,
Yayi auren sirri ne da Yar uwar dangi ta Aminin nasa batareda sanin matarsaba wadda dukkanin yardarta,soyayyarta,kaunarta da gatanta suna kansa sbd tsananin yardarta dashi dari bisa dari,
Bata taba zarginsaba ko kawo tunanin zai iya cin amanarta ko ha’intarta takowane bangare musamman sbd sunada ‘yarsu daya tak dasuke tsananin so da kauna Sa’adah.,
Saida ya shekara shida da auren ZAINAB cikin sirri Da tsananin so da kauna Mai qarfi da baya iya rabuwa da ita kafin Allah yabata cikin dayayi sanadiyar fitowar auren.
Batada labarin aurensa saidai tasamu labarin hadarin daya samu Mai tsananin gaske akan hanyarsa takai Matar asibiti tana nakuda a jahar daba tasuba,
Akaron farko da wani babban alamari ya jijjiga izzarta datake ganin tanada ita a zuviyar mijinta duk wata yardarta da soyayyarsa ta rushe tareda wani irin kunci daya cike zuciyarta tsawon shekarunda take dakonsa har yanzu,
Batasan auren mijintaba saidai gawar matarsa tagani da lafiyayyar jaririya da aka bar Mata wadda kallo daya takasa Mata sbd batason shedan ya ribaci zuciyarta ta cutatarda ‘dan kowa,
Bata taba son ‘yar ba wadda taci sunan mahaifiyarta Kuma sunanta wato ZAINAB
Bata taba sontaba kamar yanda Bata taba Jin qintaba,
Bata kallonta sbd kada ta cutatar da ita,
Ita ba jahila bace tasan Babu haqqi akan yarinyar na abundaya faru saidai Kuma takasa Hana zuciyarta yimata kallon Itace asalin dalilin tarwatsewar rayuwarsu duka sbd rabon haihuwartane yayi sanadin komai,
Tun accident din abban yarasa qafafunsa a zaune yake cikin kujera daga zaune sai kwance tsawon shekarunda sukaja masu tsayi sosai,
Bai taba ganin laifin momy ba Amma Kuma Bai taba daina rokontaba daga kwancen akan ta samu wani fili kadan a zuciyarta da zata saka Masa Laylah sbd batada kowa saishi shikuma Haka tasa qaddarar tazo baida wani Abu dazai iyayi Mata amatsayin uba,