JIDDAHTUL KHAIR 26
[indeed-social-locker sm_list=’fb’ sm_template=’ism_template_6′ sm_list_align=’horizontal’ sm_display_counts=’true’ sm_display_full_name=’true’ unlock_type=1 locker_template=2 sm_d_text=’
This content is locked
Share This Page To Unlock The Content!
‘ enable_timeout_lk=1 sm_timeout_locker=40 delay_lk=1 sm_delay_lk=4 reset_locker=1 locker_reset_after=1 locker_reset_type=’days’ ism_overlock=’default’ ]
ya jira har sai da jirgin ya tafi can sararin samaniya suka kai cruising altitude, duk da seat belt sign that is still on… hakan bai hana shi cire nasa seat belt din ba sannan ya cire mata nata, And he led her to the lavatory, wata cabin crew ta nufosu tana kallonsa tace “Is she alright?” Yace “Sure she will be” yana tsaye har jiddah ta fito daga lavatory din tana sauke numfashi, banda jiri babu abinda take gani, ga kanta dake juya mata, yace “How are you feeling now?” Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yace “Toh mu je” Tafiya ta fara yi ya bi bayanta, har xuwa wajen seat din nasu, ta xauna sannan shi ma ya xauna, kamar ya lura she is so uncomfortable from d clouds she is seeing via the porthole that she is sitting beside, rufe wajen yyi yana kallonta, hakan da yayi ya taimaketa sosai kuwa, bayan some minutes da take off dinsu aka kawo masu
snacks with drinks, kallonta yayi suka hada ido, bayan an ajiye masu ya dau nasa ya fara ci, ganin bata ci komai ba har ya gama cin abinda xai ci ya kalleta yace “Ain’t you eating?” Tayi shiru bata ce komai ba, bai kuma yi mata magana ba, har ta fara bacci, seeing how uncomfortable she is sleeping yasa ya bata access to his shoulder, a haka kuma ta dinga bacci har aka fadi nan da mintuna nawa xa su shiga lagos, shi ya saka mata seat belt din nata bayan an bada umarnin yin hakan, dalilin da yasa ta tashi daga baccin da take kenan, jiddah bata san lkcn da ta rikesa ba ta rufe fuskarta a jikinsa da xa su yi landing, Cikin kuka take gaya masa amai take ji, ya dago kanta yace “Hold it for a while…” ya bude porthole din da ya rufe yana nuna mata, juyawa tayi ganinsu a kasa jirgin na gudu ta ji hankalinta ya d’an kwanta, amma har lkcn xuciyarta bai daina bugawa ba, shi dai kallonta kawai yake, can ta kallesa, d’an murmushi yyi yace “Ya sunanki?” Ta sauke idonta tace “Jiddah” yace “Jiddah!!” Ta gyada masa kai, yace “Wannan ne farkon hawanki jirgi Jiddah?” Ta gyada masa kai, bai san lokacin da yyi murmushi ba yace “I see, to mun kawo lafiya, hope ur next flight won’t be as
frightening as this?” Ita dai bata ce komai ba,
yace “Ke kadai kika xo lagos?” Ta girgixa masa kai tace “Aa ni da yayana” yace “Wow, yana ina?” Ta buda masa hannu alamar bata sani ba, yace “Ba tare ku ka
shigo jirgin ba?” Tace “Toh ni ban sake ganinsa ba” yana waige waigen business class din yace “Ohk, sunana Yousuf…. Yousuf Umar” yana fadin haka ya ciro wayarsa yace “Sa min digit dinki so i can say hi some other time Jiddah” Tayi shiru tana kallon wayar tasa me kyau kirar samsung, can tace “Ni ae bani da waya” da mamaki yace “Baki da waya?” Ta gyada masa kai yace “Ban yrda ba” tace “Wllh, wanda yayana ya bani yana gida” ganin how she is speaking innocently yasa ya yrda, ya ciro Complimentary card dinsa ya mika mata yace “Toh ki min alkawarin xa ki kirani ga number na nan” ta dinga kallon katin dake dauke da number sa kafin tace “Alkawari fa kace” yace “Eh Jiddah” jan fingers dinta ta fara yi bata ce komai ba ya bude jakarta ya sa mata katin dai dai nan kuma jirgin ya tsaya cak, yace “Hakan na nufin kin dau alkawarin” Ta xaro ido tace “Kamar yaya” yace “A yarenmu yanda kika yi da fingers dinki yana nufin kin dau alkawarin” Ta xaro ido tana kallonsa, ya sakar mata murmushi, Cabin crew din da ta gwada mata yanda xata saka seat belt dinta daxu ce ta iso inda take tana murmushi tace “Captain Aliyu yace in taho da ke Hajiya” Jiddah ta kalli Yousuf Cabin crew din ta basu waje ta koma can ta tsaya tana jiran Jiddah, Yousuf yace “yayanki ne yayi tukin jirgin kenan?” Da mamaki take kallonsa tace “Tukin jirgi fa kace? Aa baxai iya ba” yana murmushi yace “Toh tashi ki je… ina jiran kiranki” shi ya rigata mikewa ya dau briefcase dinsa ya fara tafiya ta bi sa da ido snn ta mike ta nufi cabin crew din da tayi mata jagora har Cockpit inda Abuturrab yake xaune tare da Co-pilot dinsa wani black American suna secure Cockpit checklist, da mamaki Abuturrab ke kallon Crew din don ce mata yayi tayi leading dinta outside d plane, hannu black American din da ya kafe jiddah da ido ya mika mata yana murmushi yace “Hello….” Kallon Abuturrab Jiddah tayi, lkci daya taga ya mata wani shegen kallo, amma calmly yace “Juya ki tafi ki jirani ina xuwa…” Juyawa tayi da sauri ta bar wajen, Yana ma American din murmushi yace “We don’t do that captain, and she doesn’t even understand English” Pilot din na kallonsa yace “Ohh, is she ur sister?” Abuturrab yace “My friend’s wife….” Jiddah na sauka jirgin ta dinga kalle kalle ganin jiragai da yawa, mamaki ta dinga yi wai yau ita ce ta hau jirgi, Crew din daxu ce ta sakko suka bar wajen tare, sai bayan kusan minti ashirin Abuturrab suka sauko daga jirgin da Co-pilot dinsa. Kallonsa Jiddah ta dinga yi ganin ya kuma canxa kaya, daxu da fararen kaya ta gansa kamar uniform da hula a cikin jirgi, yana isa inda take ba tare da ya kalleta ba ya wuceta, ta bi sa da kallo, juyawa yyi ganin bata taso ba yace “Ko in daga ki ne?” Mikewa tayi a hankali ta bi bayansa, hotel din da ya ke sauka a lagos not too far from Murtala Muhammad Airport ya nufa tare da ita cikin taxi, Tana biye da shi bayan sun sauka taxi din sun shiga hotel din, bin sa take kamar xata shige jikinsa ganin mata
kusan tsirara suna yawo
hankali kwance, garin kallon wata da ta gani da wando iya cinya ta kusa fadawa kansa, ya juyo yana kallonta, kamar xata yi kuka tace “Ina ne nan ka kawo ni?” Ci gaba yyi da tafiyarsa ta bi bayansa, har ya amshi makullin daki a reception tana makale da, shi dai bai sake ce mata komai
ba suka shiga dakin da ya amsa, bayan ya kulle kofar kamar xata yi kuka tace “Su basa jin kunya ne?” Juyawa yayi ya kalleta pretending not to know what she is talking about yace “Su wa?” Ta sunkuyar da kanta, yace “Tambayarki nake su wa?” Still ta ki cewa komai, ya ajiye wayoyinsa yace “Ke me ya aike ki kallonsu?” Bai jira cewarta ba ya fita dakin ta bi sa da kallo, a hankali ta karasa ta xauna gefen gado tana bin katon dakin da kallo, ya ma fi wanda suke ciki a kano kyau sosai, Ba a dau lkci ba ya dawo dakin, fried rice with chicken, jollof rice with beef and plantain, sai pepper soup da ruwa with drinks…. abubuwan da ya bude kenan tsakar dakin ya xauna kan carpet yana nannade hannun shirt din jikinsa, ita dai kallonsa kawai take, sai da ya fara cin fried rice din sannan ya daga kai ya kalleta yace “Idan xa ki ci ki sakko” A hankali ta girgixa masa kai, ya hade rai yace “Sakko….” Bata sake cewa komai ba ta mike ta dawo ta xauna daya side din carpet din, abincinsa kawai yake ci, ganin haka ta dau spoon dake nannade cikin tissue ta saka cikin jollof rice din ta fara ci, ya gama cin abinda xai ci ya mike ya shiga bandaki ya wanke bakinsa sannan ya fito ya kwanta, ta d’an saci kallonsa ta dau sauran naman kazan da ya rage ta daura kan abincinta, hada ido suka yi lkci daya ta daburce ya mike xaune yace “Maida shi, ai nace baxa ki sake cin kaza ba” Da sauri ta mayar da kaxan kan abincin da ya rage, ya koma ya kwanta, bayan ta gama cin abincin ta gyara wajen ta hade takeaways din cikin leda, ruwan da drink ta ajiye su gefe daya, sannan ta mike tana kallonsa taga idonsa a rufe, can gefen gadon ta tafi ta xauna a kasa. Karfe biyu saura Abuturrab ya koma Airport tare da Jiddah, don he will be piloting to Abuja, hankalinta ya tashi ganin jirgi xa su kara shiga tana kallonsa kamar xata yi kuka tace “Don Allah mu hau mota, wllh bana son jirgin nan” Lkci daya hawaye ya kawo idonta, yace “Baki so saboda me?” Tana goge idonta tace “Amai nake yi, kuma ina ganin jiri, don Allah kar mu shiga tsoro nake ji” Yace “Daxu kin yi amai kenan?” Ta gyada masa kai yace “A ina kika yi aman?” Tace “Wani mutumi ne da ya xauna kusa da ni ya kai ni bandaki” Abuturrab ya juya da sauri yana kallonta yace “Ya kai ki bandaki??” Ta gyada masa kai, maimaitawa ya sake yi, ta kuma gyada masa kai, yace “Sai aka yi yaya?” Tace “Ya jirani nayi aman sannan muka dawo, da jirgin xai sauko kasa ma shine ya kamani wllh tsoro nake ji” Sake baki yayi yana kallonta yace “Ya kamaki a ina?” Tayi shiru bata ce komai ba, ya rungume hannunsa yace “Ya mutumin yake???”