JIDDAHTUL KHAIR 26
Tace “Yana jin hausa, kuma dogo ne kaman ka, sannan yace min sunansa Yousuf” Ya xare glass din idonsa yana kallonta, can yace “Ohk har hira ku ka yi kenan” Tace “Aa bamu yi hira ba” Bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da tafiya ta bi bayansa gabanta na faduwa, ticket din da Abuturrab ya yankar mata sai da ya tabbatar the person next to her is a female, exactly abinda tayi daxu daga kano xuwa Lagos shi tayi daga Lagos xuwa Abuja, Bayan jirgin ya sauka Abuja ta fita tana kare ma jirgin kallo tana fatan babu abinda xai kaddara mata sake shiga jirgi, har suka isa gidan Abuturrab wajajen la’asar jikinta a sanyaye yake, duk yana lura da ita bai ce komai ba, xaunawa tayi kan kujeran parlon tana bin parlon da kallo, yana kallonta yace “Yanxun ma kinyi aman a jirgi kenan?” Ta gyada masa kai kamar xata yi kuka, hararanta yyi ya wuce bedroom dinsa don yin alwala ya wuce masallaci dake layin, Har ya dawo tana nan yanda ya barta yace “Bakya sallah ne?” Mikewa tayi tace “Ban san inda xanyi alwala ba” Ya nuna mata dakin dake parlon, ta nufi dakin, ya bi ta da kallo sannan ya wuce dakinsa. Bayan ta idar ta fito parlor ta xauna tana sake kare ma parlon kallo, a haka bacci ya dauketa bayan ta jinginar da kanta jikin kujeran da take xaune, wajen karfe biyar da rabi aka kwankwasa kofar parlon, hakan ne ya farkar da ita, jin an kara kwankwasawa ta mike ta nufi kofar ta murda key din ta bude kofar, komawa baya tayi tana kallon warce ke tsaye bakin kofar kamar yanda take kallonta ita ma, dai dai nan Abuturrab ya shigo parlon, Jiddah ta juya tana Kallonsa….
[/indeed-social-locker]