JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 27

yace “Wai kana kallon agogo kuwa?” Ahmad yace “Ohh
ta kusa xuwa kenan, anyway ko baka fada ba dama yanxu xan wuce sai da safe” Daga haka ya mike ya nufi kofa Abuturrab ya bi sa da kallo, mikewa yyi ya bi bayansa yace “Ka ajiye ni eatry let me get something to eat” A tare suka fita gidan, sai kusan karfe goma da rabi Abuturrab ya dawo, yana shigowa parlor ya kulle gidan sannan ya wuce dakin da Jiddah take, tayi nisa baccinta, Ya ajiye ledan abincin ya nufi gadon, buga gadon yayi ko motsawa bata yi ba, yayi hakan ya kai sau uku ganin bata tashi ba ya dau bottle water ya bude, sai kuma ya fasa xuba mata ruwan ya ajiye sannan ya kai hannu kafarta yana tashinta, bude ido tayi a hankali, yace “Tashi ki ci abinci” Ta girgixa masa kai tace “Na koshi” Yace “C’mon tashi nace” Mikewa xaune tayi da kyar tana kallonsa da idanuwan bacci tace “Na koshi” Ya hade rai yace “Sakko nace” Xamowa tayi ta sauka kasa tana lullumshe ido, ya bude mata tuwo da veg soup din, ta tashi tana rurrufe ido yace “Ina xa ki?” Tace “Xan wanke hannu” Bai ce komai ba ta tafi ta wanke hannun ta dawo, tun da ta fito yake kallonta, Kana ganin yanda Hijab din yayi a jikinta xaka kasan bata saka komai ba a ciki, dama kuma hijab din har kasa yake ja mata, xaunawa tayi ta jiginar da kanta jikin gadon ta lumshe ido, buga gadon yayi ta bude ido da sauri ta kalli abincin gabanta sannan ta kai hannu ta fara ci a hankali, juyawa yayi ya fita dakin…. Washegari da safe Abuturrab ya fita yayi mata shopping din few clothes, karfe goma kuma ya nufi airport tare da ita, babu abinda ya sanyaya masa jiki sai yanda kiran Aunty ya dinga shigowa wayarsa babu kakkautawa, shi kuma yaki dagawa, Jiddah na ganin inda suka xo hankalinta ya tashi, marairaice masa tayi tace “Ni fa bana son hawan jirgin wllh” Yana kallonta yace “Sai me xa ki hau?” Tace “Motar” Wani kallo yayi mata yace “Sai ki hau motar inda kika gansa ai” Lkci daya hawaye ya kawo idonta bata kuma ce

masa komai ba, tun bata kai ga shiga jirgin ba taji kanta ya fara juya mata, Tana rike da wayansa da ya bata ta nemi kujera ta xauna a business class, sai waige waigen inda xata gansa ta mika masa wayar take, to ina shi yake xama ne a cikin jirgin, tunawa tayi a inda ta gansa jiya bayan jirgi ya sauka, and she assumed a wajen yake xama shi, jin taku a gefenta Jiddah ta juya, buda ido tayi sosai ganin wanda suka shiga jirgi tare da shi a rana na farko, seat dinsa ya nufa ya ajiye karamin jakar hannunsa a sama sannan ya xauna, da sauri ta dauke kanta gabanta na faduwa, wata mata ce ta xauna kusa da ita tayi mata sannu, murmushi kawai Jiddah ta mata tana juya wayar Abuturrab dake hannunta, bayan wani lkci jirgin ya tashi, suna keta hazo ta cire seat belt dinta da sauri ta mike bayan ta ajiye wayar Abuturrab, hanyar lavatory ta nufa sai a sannan Yousuf ya ganta ya bi ta da kallon mamaki, ba a dau lkci ba ta fito, matar dake kusa da ita tace “Did u feel nauseous?” Jidderh tayi mata murmushin karfin hali ta xauna, Ta d’an saci kallon Side din da Yousuf yake suka hada ido, sunkuyar da kanta tayi, throughout the short journey to kano bacci tayi a jirgin, snacks da aka kawo mata ma bata ci ba, Matar dake gefenta tayi tapping dinta tace “Ki saka seat belt dinki” Bude ido Jiddah tayi ta fara saka seat belt din, runtse ido tayi da jirgin ya fara sauka bayan ya samu izinin yin hakan, matar da ta lura she is very uncomfortable ta riketa, tace “It’s just for a few seconds, sorry dear” Jiddah bata ce mata komai ba har jirgin ya sauka, rufe bakinta tayi kar ma tayi ihu, matar na Kallonta tana murmushi tace “it’s all over” A hankali Jiddah ta cire seat belt din, bayan da jirgin ya tsaya ta mike ta dau hand bag dinta ta fara fita kamar yanda ta ga sauran nayi, da kallon mamaki matar ta bi ta, tana mamakin to ko kurma ce dai, Yousuf ya mike ya dau jakarsa ya bi bayanta da sauri, a hankali take sauka daga matakalan jirgin iska me sanyi na kadawa a filin airport din, tana sauka kasa kamar ance ta juya taga Yousuf yana saukowa shi ma, murmushi ya sakar mata har ya iso inda take yace “Jiddahh” Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, mika mata hannunsa yayi yace “Bani wayar taki in sa maki number na tunda Allah ya sa kin taho da shi yau” Ta buda ido sosai tace “Ba wayata bane, na yayana ne” Da mamaki yake kallonta yace “Yayanki? Yana ina?” Ta kalli cikin jirgin tace “Kaman yana ciki, ni dai ban gansa ba” Yace “Ina ku ke xuwa tare da shi ko da yaushe a jirgi?” Tace “Nima dai ban sani ba” Yace “Baki sani ba kamar ya?” Tace “Allah ban sani ba ne” Yayi shiru yana kallonta walking slowly together with her, can yace “Me ku ka je yi a Lagos?” Ta kallesa da sauri tace “Lagos?” Yace “Ehh” Tace “Nan ne Lagos din don Allah?” He couldn’t help it but left his mouth agape yana kallonta with surprise, ta dauke kanta tana ci gaba da tafiya yace “Wait Jiddah, are you kidding me, or you just don’t want to give me an answer” Bata ce komai ba, calmly yace “I am talking Jiddah…” Tsayawa tayi tana kallonsa tace “Ni fa ba wani turanci nake ji ba” Sake baki ya kuma yi yana kallonta, bai san lkcn da yace karya kike…. Tace “Wllh ba karya nake maka ba” Sincerely ta fadi hakan, ya shafa kansa yana sake kallonta daga sama har kasa yana naxarin abinda tace wai bata jin turanci, but how?? tsadadden abaya ce jikinta blue da ya mugun haskata, ko kwalli babu a idonta, wanda kuma bai kalli lips dinta da kyau ba, sai yayi assuming pink lip gloss ta saka coz after being pinkish har sheki lips din nata yake, ga manyan idanuwanta farare tasss kamar madara, hancinta kuwa have the perfect shape a nose should have snn ga tsayi, ya d’an mata murmushi yace “Na yarda Jiddah, yanxu ina xa ki?” Tace “Nima ban sani ba yayana nake jira, kilan yana saman jirgin har yanxu” Yace “Yayanki… iyayenku daya

[indeed-social-locker sm_list=’fb’ sm_template=’ism_template_6′ sm_list_align=’horizontal’ sm_display_counts=’true’ sm_display_full_name=’true’ unlock_type=1 locker_template=2 sm_d_text=’

This content is locked

Share This Page To Unlock The Content!

‘ enable_timeout_lk=1 sm_timeout_locker=40 delay_lk=1 sm_delay_lk=4 reset_locker=1 locker_reset_after=1 locker_reset_type=’days’ ism_overlock=’default’ ]

da shi?” Shiru tayi can kasan ranta kuma tana tunanin abinda xata fada masa, yace “Ki gaya min gaskiya Jiddah” Ta kallesa still bata ce komai ba, yace “Ina sauraranki” ta kwantar da kai tace “Me yasa kake son sani?” Yace “I just…” Shiru yayi kamar wanda ya tuna abu, sai kuma yace “Kawai ina son sani ne” Tace “Ba iyayenmu daya ba amma yayana ne” A hankali yace “Ko dai saurayin ki Jiddah” Ta wani xaro ido, sai kuma ta kyalkyale da dariya tace “Saurayi na? Saurayina fa kace? Aa ni ba saurayina bane shi wllh, saurayina sunansa Umar amma mun rabu yanxu” Yace “Umar?” Tace “Ehh, shi wannan kawai yayana ne” Wayar hannunta ya amsa da sauri tace “Nace maka nasa ne wayar” Bude screen din yayi don wayar a bude yake, ya dinga kallon hulan pilot dake jikin screen din wayar, karban wayar tayi hannunsa, xuwa lkcn bbu kowa haraban parking din jirgin sai ma’aikatan airport, Yousuf ya daga kai yana kallon Abuturrab dake saukowa daga jirgin yana kallonsu babu ko kiftawa, har sannan pilot uniform ne a jikinsa, Jiddah ta daga kai ganinsa ta kalli Yousuf tace “Shine yayan nawa” Yousuf ya d’an yi murmushi yace “Shine matukin jirgin… i guess right” Juyawa Jiddah tayi da sauri tana kallon Abuturrab, Yousuf ya karasa gunsa ya basa hannu suka gaisa yana murmushi yace “I guess you did the landing…” Abuturrab na kallonsa ya d’an yi murmushin gefen baki kamar wanda aka tilasta ma yace “Yea, i did” Yousuf yace “Nice landing….” Abuturrab yace “It’s a pleasure flying you” Yousuf ya masa murmushi sannan ya juya ya bar wajen, yana isa inda Jiddah take yace “Ina jiran kiranki kamar yanda kika yi alkawari ranan” Yana fadin haka ya wuce, Jiddah ta kalli Abuturrab da ya hade girar sama da ta kasa yana kallonta…. A motarsa suke tafiya xuwa hotel din da suka sauka a kano, har sannan babu abinda yace mata, sai dai fuskarsa bbu ko digon annuri, har suka isa hotel din, kulle dakin hotel din yyi after going in together with her, yana kallonta fuskarsa a tamke yace “Waye wannan mutumin da na ganku tare?” Tace “Wai da gaske kai ne kake tukin jirgin in ji sa? Ni dai nace masa ba kai bane ae baxa ka iya ba” fixgota yyi, tayi wani kara xata durkusa ya dagota yace “Tambayar ki nake waye shi??” Kamar xata yi kuka tace “Toh ba q jirgin muke haduwa ba” ganin taki tsayawa cikin tsawa yace “Baxa ki tsaya ba” Kin tashi tayi tace “Toh don Allah ka sakeni” kallonta kawai yake yi, can ya saketa, xamewa tayi ta xauna kasa, yace “Waje daya ku ka xauna da mutumin?” Tace “Aa, kawai da na sauka jirgin shine ya bi ni yana min magana” Shiru yayi yana kallonta ita dai bata yarda ta kallesa ba, can ya juya ya bude kofar dakin ya fita. Bayan la’asar suka bar kano xuwa kaduna a motarsa, Jiddah na kallonsa after the 20 mins silence tace “Meyasa muke ta shiga jirgi bayan ga mota, kyauta ake tafiya a jirgin ne?” Ya mata wani kallo yace “Kyauta? Tsoronki ake xaki shiga jirgi kyauta?” Tace “Toh Iyah ta ta6a ce min kudin jirgi yana da tsada kusan miliyan ne” Ya d’an kalleta yace “Haba??” Ta wara ido tace “Wllh, kasan ta ta6a xuwa makka sau daya, yaranta ne suka biya mata, toh ni na xata masu kudi ne kawai ke hawan jirgi” D’an murmushin da bai shirya ba yyi yace “Ni ba me kudi bane kenan?” Ta d’an xaro ido tana kallonsa tace “Aa bance haka ba, amma wannan motar taka ce?” Bai ce komai ba, a hankali tace “Kayi shiru…” Yace “Aa na Abbana ne” Tace “Toh gidan fa?” Yace “Wani gida?” Tace “Wanda muke ciki?” Yace “Shi ma na Abbana ne” Tace “Kenan shi ne ya biya kudin jirgin da muka shiga?” Yace “Ehh” Tayi shiru tana kallonsa, ta gefen ido ya kalleta, ta sauke idonta, bayan few seconds tace “Abbana ya ta6a ce min watarana xan shiga jirgi, amma Makka yace xanje” Ya kalleta yace “Haba” Ta gyada masa kai, tace “Kuma gashi na shiga amma ban je makkan ba” Yace “Toh idan kina da kudi ki kawo in biya maki Umrah ki je” Ta buda ido tace “Kudi?? A ina xan ga kudi ni ba sana’a nake ba” Yace “Ohk kina son kiyi sana’a ne? Ko awaran xaki siyar a bakin layin gidanmu?” Dariya ta fara yi, ya dinga kallonta don bai ta6a ganin dariyarta ba, tayi me isarta sannan tace

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button