JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 27

“Idan kace inyi sai inyi in dai xa a siya” Da mamaki ya d’an kalleta kafin ya maida dubansa kan titi yace “Xa kiyi kenan idan nace kiyi” Tace “Ehh, sai in yi har da wainar flawa da dankali” Yace “Toh bari mu je a samar maki waje a bakin titin ko?” murmushi ya ga tayi tace “Toh” Ji yayi kamar ya fixgota ya rankwasheta, tace “Toh amma kudin xa su taru har in je makkan kuwa?” Yace “Wannan ke xan tambaya ai, babarku ta tara kudin ya isheta har taje makka?” Shiru tayi tana kallonsa, can tace “Toh ai abinci muke ci da kudin sana’ar, wannan kuma baxan siya abinci da kudin ba tunda akwai abinci a gida koh” Shafa millionaires belt dinsa yyi still wondering if yarinyar nan xata ta6a wayewa, though ya ma yi mamakin yanda har ta fara iya dressing ko don kayan da ya siya mata sunyi correlating da mahadinsu ne, sannan bai ga tana irin kwalliyan nan na masu talla ba, a ja gira a shafa barbada kumatu, a shafa gazal, babu wanda xai kalleta yace she is local or even an illiterate sai ya ji xancen dake fita daga bakinta, mamaki ma yayi yanda ta bude baki take creating conversation da kanta yau, muryarta yaji tana cewa “Idan kudin ya taru da yawa kai ma sai in biya maka tunda ka taimakeni koh?” Ya d’an kalleta da sauri sannan yace “Haba?” Tace “Ehh, ko kuma in biya ma Umma” Murmushin gefen baki yayi yace “Ashe na taimake ki?” Tayi shiru tana kallonsa, sai kuma ta gyada masa kai a hankali, Bai kuma cewa komai ba, kuma bai kalleta ba, jin tayi shiru bayan kusan minti goma sha biyar, breaking the silence yace “Bayan awaran da dankali babu wani sana’ar da xa ki yi?” Ya d’an kalleta da yaji bata amsa masa ba, bacci yaga tana yi, xuwa lkcn sun fara fita outskirt din garin kano, ya kai hannu a hankali ya kwantar mata da kujeran motar, snn ya kara Ac din motar, har suka shigo garin kaduna bayan magrib bacci take, amma ta farka yyi sau biyar a hanya, mai gadi na bude masa gate yayi parking a parking space, ya sauka motar yana stretching kansa, coz he is very tired bayan tukin jirgi ga na mota, jingina yayi da motar ya rungume hannunsa, har ya mance rabonsa da workout, tun sanda burden din Jiddah ya hau kansa, xagawa yyi ya bude side dinta ya

bubbuga motar slowly, a hankali ta bude ido ta fara kalle kallen inda suke, yace “Sakko” sauka ta fara yi daga motar ya koma gefe tana fitowa ya kulle motarsa. Bayan sun shiga gidan xata wuce dakinta yace “Ki tabbatar kinyi sallah” Wanka jiddah tayi sannan ta dauro alwala bayan ta idar da sllh ta saka kayan baccinta ta kwanta. Karfe tara ya shigo dakin da abinci, tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai, kawai ya ajiye ledan ya fita. Washegari da ya kasance ranan juma’ah Jiddah na idar da sallan asuba ta sauko kasa ta hada shayi ta dumama abincin da ya kawo mata jiya da daddare ta wanke tukunyar da ta bata ta koma dakinta, duk kafin ya shigo gidan daga masallaci, don sai ya gama azkar dinsa yake shigowa gida, bata mance warning din da yayi mata ba, ganin har karfe sha biyu Abuturrab dake xaune parlor bai ga ta sakko ba, lkci lkci kuma ya ke kallon sama, daga karshe ya mike ya haura stairs din sannan ya bude kofar dakinta, bacci ya sameta tana yi, yayi knocking kofar da karfi wanda hakan ya farkar da ita ta mike xaune da sauri, ya wani daure fuska yace “Baki da hankali har yanxu bacci kike?” Tace “Aa nayi wanka na gyara dakin” Ganin hararan da yake mata ta dauke kanta, yace “Ohk kin fi so ki kwanta daki kullum in fita in siyo maki abinci in kawo maki anjima kice ai bani da kudi?” Buda baki tayi tana kallonsa tace “Ni yaushe nace baka da kudi?” Ya rungume hannunsa yace “Jiya a mota” Tace “Aa ni fa kudin jirgi nace baka da shi tunda ya kai miliyan daya, kuma kace min Abbanka ne ya biya ai ko??” Yace “Ehh abincin da kike ci ma ai duk shi yake siyowa in kawo maki ko” Tayi shiru tana kallonsa, can tace “Toh me yasa baka son kayi sana’a, kaga Umar yana fita kasuwa kullum, don kawunsa na da shaguna uku a kasuwan bacci…” Kallonta yake ko kiftawa baya yi, tace “Kai ma xa ka iya ce a neman maka waje a kasuwa tunda Abba na da kudi ae” Ya shafa fine beard dinsa yace “Haka ne kuma, amma ya aka yi kika san bana sana’an komai” Ta sakko da kafafuwanta daga saman gadon tace “Naga to ko da yaushe kana gida, idan baka son ka xauna a gidan kuma sai ka tafi kano, to ko sana’a kake xuwa yi a kanon?” Ya girgixa kai da sauri yace “Can ma kawai xama nake a gida, ai ba a bani sana’an da xan yi ba” Tayi shiru, sai kuma ta kallesa tace “Amma lkcn da kake xuwa hayin rigasa a ina kake samo wannan kudin da kake bani in ba Babarmu?” Yace “Abbana ke bani” Tace “Toh, shkkn” Yace “Yanxu kasuwan xan fara xuwa nima kenan” Tace “Eh ka gaya ma Abbanka ya bude maka shago” Yace “Sai ni dake mu dinga xama a ciki ko?” Kallonsa tayi ta fashe da dariya sosai dimples dinta na lotsawa, ya dinga kallonta, second time da yake ganin dariyarta kenan, tayi me isarta tace “Dama mata na xuwa kasuwa?” Ya rungume hannunsa yana kallon large eyeballs dinta yace “Tunda xa su iya xaman gefen titi su siyar da awara da dankali me xai hana??”

Toh Chamo dai tace banyi addu’ar Allah yayi min katangan rodi with some set of readers ba, duk da dai ra’ayinsu suke 6a6atu a kai nd they are entitled to der opinion, but oh God do not allow me to be seeing der comments so that i can write happily till end without mind spoilage Ameeeeenn ???? to those of u reading my book for free know that u owe me dari biyar kacal ehe… ????

[/indeed-social-locker]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button