JIDDAHTUL KHAIR 37

kallon Abuturrab bayan ya shigo dakin, ya ajiye mata flask din gefenta yace “Ga flask dinki ya fashe sai ki fadi nawa kika siya a biyaki….” Da farko Hajja bude baki tayi tana kallonsa, sai kuma ta dauka da sauri ta jijjiga, lkci daya ta sake flask din ta mike sai kuma ta fashe da kuka tace “A Masar fa mijin Nafisa ya siya min flask din, waye yayi min wannan aika aikan??” Abuturrab yace “Ni ne, kuma shi yasa nace ki fadi nawa yake” Tace “Toh Allah ya isa wllh, don kaf dukiyarka baxasu siya min
flask din ba tunda a Masar aka siye sa ba a kasar nan ba, sannan me ya kai flask dina hannunka bayan wancan matar na ba ta juyo min ruwan xafi?” Yace “In dai kin tambayi nawa aka siya sai ki gaya min” Daga haka ya juya ya fice daga dakin, ta fashe da kuka tace “Allah ka dai ga wannan xaluncin da aka min, a ina xa a samo flask irin wannan yanxu a kasar nan” Komawa gefe Jiddah tayi da sauri bayan Abuturrab ya fito don tana labe bakin kofar, ta bi sa sa kallo har ya wuce sannan ta shiga dakin gabanta na faduwa, a fusace Hajja tace “Ke garin yaya flask dina yaje hannun wancan mutumin da ya tsaneni?” Jiddah ta sunkuyar da kanta tace “Dauka yayi Hajja” Hajja tace “Toh yaje shi, ni ba yafewa nayi ba, kuma bari
Usman ya dawo tunda shi na haifa” Ita dai Jiddah bata ce komai ba. Bayan magrib Umma ta ajiye ma Ummi duk abinda Hajja ta ba su Jiddah da Maimoon na kayan lefe, Ummi tace “Ki bar masu kawai tunda ita ta basu” Umma tace “Aa maida masu da kayansu yaya, a ina aka ta6a haka” Ummi tace “Wai ba ni nace ki bar masu ba??” Umma tace “Toh Allah ya kyauta bari in je in ma Hajja sallama” Daga haka Umma ta fita bangarenta, a corridor suka hadu da Aunty xata sakko parlor, Aunty tace “Aa Hajiya Ramlah ashe kun shigo, mun wuni lafiya?” Umma tace “Alhmdlh” Aunty tace “Tun shekaranjiya nake ta ce ma Ummi ta kiraku an gama hada lefe wllh…” Umma tace “Ai kam kaya maa sha Allah, Allah ya sanya alkhairi” Aunty tace “Toh ai ni na xata kin xo kenan sai mun dawo daga kai lefen, kin san gobe ne xa a kai fa da safe” Umma tace “Aa sai kun dawo Hafsah, ni ba wani dadi nake ji ba, Allah ya
kai ku lafiya ya dawo da ku lfya” Aunty tace “Ehh tun da ma da ni xa aje shkkn kawai, Allah ya kara lafiya…” Umma dai ta wuce dakin Hajja, Aunty kuma ta sauka parlor, Ummi na kallon Jiddah dake parlonta ita kadai, su Maimoon kuma na daki wajen Ramlah tace “Kwashi kayan ki kai mota Jiddah” Jiddah ta mike ta dau ledojin kayan da Hajja ta basu ta fita, Aunty dake xaune parlor da wata bakuwa da tayi, Abuturrab ma na parlorn don kudi ta kirasa xai tura ma bakuwar wai na zoben gwal guda biyu da xa a sa ma Aneesah a lefen, ta bi Jiddah da kallo tana kare ma ledojin hannunta kallo, shi ma Abuturrab kallonta yake, Jiddah ta gaisheta ta nufi kofa ta fita, mikewa Aunty tayi tace ma bakuwarta tana xuwa sannan ta fita da sauri, shi dai Abuturrab bai ce mata komai ba, a compound ta tsayar da
Jiddah ta amshi ledojin hannunta tana duba abubuwan ciki, kwace dayan ledan tayi da karfi tace “Ubanki ne ya siya kayayyakin da aka baki ki kai mota??” Jiddah dai tayi shiru tana kallonta, Aunty tace “Baxa ki daina kallona cikin ido ba sai na tsole idanuwan?” Sunkuyar da kai Jiddah tayi, Aunty ta juya kamar xata tashi sama ta koma cikin gida, Abuturrab na kallon Aunty bayan ta xauna a parlor ta ajiye ledojin da ta amso a gefenta yace “Aunty da baki amsa ba ai ni nace xan siya duk abinda babu a ciki” Aunty tace “Rufe min baki, kai xaka gaya min abinda xanyi da wanda baxan yi ba, duk wanda bai rike girmansa ba xai ga rashin girma a gidan nan wllh, a kan me xa a debe ma yarinya kaya wannan ai karanta ne wllh,
wannan abun kunya har ina kawai a bude lefen yarinya a yashe mata kaya??” Umma da ta shigo parlon tare da Ummi ta kalli Aunty amma bata ce mata komai ba suka fita parlon tare da Ummi Aunty tace “A gaida gida” a compound suka ga Jiddah a tsaye, Umma tace “Ina kayan? Kin kai mota?” A hankali Jiddah tace “Aunty ta karba” Juyawa Umma tayi ta koma parlon, Ummi ta bi ta da kallo sai kuma ta bi bayanta, Umma na kallon Aunty tace “Kayan da kika amsa xa ki bani Hafsah” Aunty tace “Wllh baxan bada ba Hajiya Ramlah, wannan ai ba girmanku bane daukan kayan yarinya, wannan ai karanta ne, ku idan aka ma ‘ya yanku haka xa ku ji dadi??” Ummi ta kalli Abuturrab tace “Aliyu” ya daga kai ya kalleta, tace “So nake ka kwashe akwatunan nan gaba daya ka kai su gidan Ramlah da daddaren nan” Aunty
tayi wani shewa tana tafe hannu tace “Gidan Ramlah? To ai naga ba Ramlah bace ta hada lefen, don haka xan ga me kwasan akwatuna ya fita da su gidan nan yau….” Shi dai Abuturrab kallon Ummi ya dinga yi ya kasa cewa komai, Hajja ta fito rike da fasasshen flask dinta tace “Me ke faruwa na ganku cirko cirko a tsaye?” Aunty na kallon bakuwarta tace “Xa a tura maki kudin na biyun ki tafi gida kawai Salaha” Daga haka ta bar parlon kamar xata tashi sama, Salahan ta mike ta fita parlon, Ummi na kallon Abuturrab strictly tace “Kaji abinda na gaya maka?” Yayi kasa da murya yace “Ummi duk bai kai haka ba, don Allah…” Wani tsawa tayi masa tace “I said take away the boxes to Ramlah’s home” Hajja tace “Naga ikon
Allah, na tambayi me ke faruwa an min shiru” Ummi tace “Cewa nayi ya kwashe akwatunan ya mayar gidan Ramlah daga can xa a kai su” Hajja tace “Atohh a kira mai gadi ya fitar da su xuwa motar mana me ake jira” Kallonta Abuturrab yyi fuska daure, Ummi tace “Ya fita ya kira mai gadin da kansa, idan ba haka ba wllh wllh baxa a kai kayan nan ba, kuma kudin da aka kai sai dai a yafe shi….” mikewa Abuturrab yyi yana kallonta, Ummi ta juya ta bar parlon Umma na biye da ita. Hajja ta nufi kofa don kirawo mai gadi tana cewa “Aa bai kai haka ba Hauwa ni da kaina sai in je in kira mai gadin a fito da akwatunan” Abuturrab ya koma ya xauna ya rike kansa ya rasa tunanin da xai yi, mikewa yayi ya nufi bangaren Aunty….