JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 41

Ahmad dake xaune kujera me xaman banxa ya wara ido bayan El-Basheer yyi parking yace “Waow is this Jiddah??” Sunkuyar da kai tayi tana d’an murmushi ta koma gefe tace “Sannunku da xuwa” Shi dai El-Basheer kallonta kawai yake ta cikin glass din idonsa kamar yanda sauran abokan Abuturrab biyu dake bayan motar ke kallonta su ma, Ahmad ya sauka motar yana mata murmushi yace “Ina xa ki?” Ta nuna masa inda motar Abuturrab yake tace “Maimoon tace yana kirana” Ahmad ya kalli motar sae kuma yyi pretending bai gane wanda take nufi ba yace “Waye a nan?” Tace “Ya Aliyu” Ahmad yace “Uhnn ohk” he was thinking har sannan bata san sunansa ba ai, El-Basheer ya sauko motar yace “Irin wannan kwalliya haka Jiddoh” Ta daga kai ta

kallesa shi ma tayi masa murmushi, and her smile was heart melting, shafa kansa yyi ya kalli Ahmad da yace “To mu je mu rakaki gun Aliyun” ita dai bata ce komai ba, Ahmad na kallon bayan motar yace “To ko kun xata a jirgi ku ke naga kun ki sakkowa” Dariya pilots din biyu suka yi still not coming down, Najeeb yace “Kasan akwai kyau that’s breath taking…” El-Basheer ya nufi motar Abuturrab, Ahmad ya kalli Jiddah yace “To mu je” Tafiya ta fara yi ya bi bayanta, Ta glass Abuturrab ya dinga kallonsu da

tight face dinsa, har suka iso gun motarsa, El-Basheer yace “Ka kashe waya ne?” Abuturrab yace “Ehh but na kunna yanxu” El-Basheer yace “Saura few hours for the dinner, mu je inda kace ynxu mu dawo, ga co pilots dinka can a mota” Abuturrab yace “Ohk to mu hadu a can din” Daga haka ya tada motar, ganin tafiya xai yi Ahmad yace “Kiran da kake mata fa?” Sae a snn Abuturrab ya kalli Jiddah dake tsaye, bbu yabo bbu fallasa yace “Ohk, ance ke Hajja ta ba makullin dakina?” Ta girgixa kai tace “Aa yanxu muka

dawo” Bai tanka ta ba ya ja motarsa ya bar wajen, El-Basheer ya kalli Ahmad yace “Kasan da Airline din da suka dauki Aliyu xa su sake bincikan brain dinsa aikinsa baxai kwana a hannunsa ba ranan, am telling u at that moment xa su sallamesa wllh” Dariya kawai Ahmad yayi, El-Basheer yace “Didn’t u notice he is behaving like someone with mental condition?” Ahmad ya kalli Jiddah yace “Kwalliyan ya maki kyau sosai Jiddah” El-Basheer ya kallesa ya fara tafiya xuwa gun motarsu, Ahmad yace “Sai mun hadu anjima wajen dinner” tace “Toh” daga haka ta wuce cikin gida. Bayan

Magrib su Abuturrab na gidan El-Basheer duk sun gama shiryawa, Abuturrab dai na xaune yana ta danna wayarsa, ya kafa hularsa a kai, kana ganinsa kasan he is the ango, Ahmad na kallonsa yace “Pls are u cautious of time Captain” Abuturrab ya daga kai ya kallesa yace “Ohk, what about that?” Najeeb yace “Kar ka manta sai an fara xuwa can gida an dau amarya” Abuturrab yace “Eh na sani, and i suggest ku tafi ku daukota, ni xan tafi event center din with my ride, sai in jira xuwan ku a mota” Ahmad yace

“Why not duk mu tafi tare?” Abuturrab yace “Duk fa daya ne dude” Ba wanda ya sake ce masa komai, bayan few minutes duk suka fita gidan a tare, ya riga su wucewa da motarsa. Jiddah ce tsaye tana kokarin daura mayafi a kan lafiyayyen head din da aka daura mata, she looks so beautiful with her new make up wanda Hajja ta tada bala’i ta saka mai make up din Aneesah ta yi mata, domin kuwa ana Magrib ta wanka wanda aka masu da

yamma wai ita sae ta sake alwala, doguwar riga fitted aka masu gaba daya a ankon dinner din yan mata da Aunty ta fitar na wani lafiyayyen lace, Sounding so fed up Maimoon tace “Wllh ke dai Jiddah kina da matsala, duk a nan wa kika ga ya wani dau mayafi xai yafa? ba fa a sa mayafi a kan irin wannan shigan wllh, tun daxu kike ta bamu matsala kin kama kin wanke make up bayan kowa na rike da alwalansa ke kince baki san xance ba, da ba

don Hajja ba yanxu ai baxa ki samu wani make up din ba…” Jiddah da taki sauraronta tace “Ni dai baxan iya fita haka ba…” Maimoon ta fixge mayafin tace “U will just look odd among us, kawai fa mota xa mu shiga a ajiye mu a wajen mu shiga, idan xa mu dawo ma mota xa mu hau a dawo da mu gida ba wai titi xa mu bi muyi ta tafiya a kafa ba” Jiddah ta dinga kallonta alamar ita fa bata gamsu ba, duk kawayen amarya dake wajen kallon Jiddah kawai suke, irin kyan da tayi ba don anko ne jikinta ba bbu wanda dama xai ce ba ita bace bride din, ita Aneesah dama can dakin Aunty aka kai ta ana shiryata, Jiddah ta ta6a jelan tulin gashinta da ya leko

ta head din tace “Yanxu har gashina haka xan bar shi a waje?” Wani harara Maimoon ta watsa mata tace “Ae kuma sae kiyi….” Daga haka ta nufi wayarta dake ring, Jiddah ta bi ta da ido, bude baki Maimoon tayi da mamaki tana kallon screen din wayarta, can ta nemi waje ta xauna a hankali tace “Toh wai ni me nayi ma Yaya Aliyu?” Sae da ya kusa katsewa ta daga ta kai kunne ta marairaice murya tace “Na’am Yaya?” Yace “Kuna ina?” Tace “Mun shirya xa mu fito yanxu” Yace “Ke da su wa?” Tace “Ni, Aunty Safiyya, Aisha, Sister Ramlah, Nafisah, Jiddah da wasu baki yan mata biyu?” Yace “Duk wani mota ne xai kwashe ku haka?” Ji tayi kamar

tayi kuka ta dai dake tace “Aa dama saurayin Aunty Safiyya ne xai kai mu don ba mota” Yace “Duk ku takwas din mota daya xai kwasa?” Ta murguda baki tace “Aa Yousuf ma ae xai xo yace yana hanya” Abuturrab ya xauna da kyau a kan driver seat din da ya d’an kwantar yace “Shi kuma wa xai dauka?” Tace “Aa kawai dai xai xo tunda mota daya baxai ishemu ba, sai ya dauki duk wanda xai dauka” yace “Wa ya kira Yousuf din?” Tace “Waya suka yi da Jiddah” Abuturrab yace “Ohk… Idan kun kusa sai ki kirani xan baki

ajiya ne” Tace “Toh” yace “Aneesah da frnds dinta sun bar gida ne yanxu?” Maimoon tace “Aa ba a gama shiryata ba” Yace “Ohk ki tabbatar basu riga ku fitowa daga gida ba in baki sakon da nace” A hankali tace “Toh” daga haka ya katse wayar, Maimoon ta wani turo baki tace “Toh wai ni me ya hadani da shi ne yau yake ta kirana haka” Jiddah dai bata ce komai ba ta karasa cusa mayafinta a jaka kafin Maimoon ta farga, kamar yanda ya fada Maimoon ta harhada tawagarsu ta kannin ango suka fito don Saurayin Safiyya ya iso, Safiyya da su Aisha da Ramlah suka shiga motarsa, Maimoon na ganin kiran Yousuf ta daga nan ya sanar masu ya iso, Babu yanda Jiddah

ta iya haka ta shiga gaban mota, gaba daya a kunyace take saboda shigar da tayi, Maimoon dai ta shige bayan mota da Nafisah da wasu yan matan biyu, Yousuf ya amsa gaisuwansu gaba daya yana murmushi, bayan sun hau saman hanya ya d’an kalli Jiddah murya can kasa yace “Me yasa kika fito haka Jiddah?” Tana wasa da jakarta dake kan kafarta ta girgixa masa kai kawai, bai kuma cewa komai ba, sai da suka kusa event center din wayar Maimoon ya fara ring, tana ganin me kiranta ta jinginar da kanta da kujeran motar murya can kasa tace “Na shiga uku” Can dai ta daga ta kai

kunne tace “Na’am yaya” Yace “Kuna ina?” Tace “Gashi mun kusa muna hanya” Yace “Ke da wa?” Tace “Nafisah da wasu yan uwan Aunty” Ya xauna da kyau yace “Sai wa?” Ta kalli Jiddah dake gaban mota tace “Jiddah” yace “Ohk, idan kun sauka ke da ita ku taho parking space xan bar fitila a kunne

yanda xa ku ga motata” a hankali Maimoon tace “Toh” ya katse wayar. Yousuf na parking ya juya yana kallon Jiddah yace “I am not happy at how u dress today” Ta kallesa, Maimoon da ta galla masa wani harara ta fara kokarin sauka motar tace “Toh mun gode yaya yousuf, Jiddah mu je mu amso sakon….” Daga haka ta sauka, Jiddah na kallonsa a hankali tace “Kayi hakuri, mayafina na cikin jakana xan saka” Yace “Toh saka yanxu” Ta d’an kalli Maimoon dake tsaye ta wani sha kunu tana jiran saukowarta, Tace “Xan saka da gaske idan na sauka” yace “Wani sako xaku amso?” Jiddah ta

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button