JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 41

ya koma ya xauna, Sai kallonsa kawai Abuturrab yake kamar yasan tambayar da yaje yayi ma Maimoon…. Sai karfe goma da wani abu aka tashi dinner din, outside d hall Abuturrab ya shafa kansa ganin motar da aka ajiye masa shi da Aneesah da xai maidasu gida, Ahmad na kallonsa yana jiran jin me xai ce don ya san da magana a bakinsa, Abuturrab na kallon Aneesah yace “Get in” Shiga motar tayi ya daga mata gown dinta dake jan kasa ya mika mata, ta amsa tana murmushi tana kallonsa, shiga motar yayi shi ma,

Najeeb ya shiga driver seat ya tada motar suka fita hall din… kawayen Aneesah suka shiga motar Ahmad yayi gida da su su ma, Dai dai kofar gidansu Abuturrab Najeeb yayi parking, Najeeb yace “Xa mu jira frnds dinta yanxu sai su shiga da ita ko?” Abuturrab yace “Aa ba sai mun jirasu ba, ba dai kawai shiga ciki bane” cike da shagwaba Aneesah tace “Don Allah Baby ka jira su iso ni kunya nake ji wllh, sai su Ummi su ganmu haka mu biyu ai da kunya” wani kallon gefen ido yayi mata bai ce komai ba

ya bude motar ya sauka, Najeeb couldn’t help it but laugh ganin da gaske wucewa ciki Aliyu xai yi yace “Captain plss ka jira frnds dinta su xo xai fi” Abuturrab yace “Noo ai na barta ta jirasu, i have to go and ease my self” Daga haka yayi wucewarsa, Aneesah da ta sha kunu ta bi sa da wani irin kallo…. Can backyard din gidan Abuturrab ya tafi ya ja kujera ya xauna yana jiran su shisshiga, lkci lkci yake kallon agogon wrist dinsa, bayan some minutes ya mike ya fita gidan, da kafa ya karasa bakin hanya, ya samu adaidaita ya koma can wajen event center din, har sannan da akwai mutane wajen, kansa a kasa ya nufi parking space wanda motoci sun ragu sosai, direct gun motarsa ya nufa ya ciro makulli ya danna lock din motar

snn ya bude back seat, xaune ya ganta ta hade kai da gwiwa kamar mai bacci, tana jin an bude motar ta dago da sauri, bayan ja har kumbura sai da idanuwanta suka yi don kuka, ta sauke kanta kasa yace “Fito” Ba musu ta fito daga motar ba tare da ta kallesa ba, fixgo hannunta yayi ganin wucewa xata yi, ta fashe da kuka sosai tana kiciniyar kwace hannunta tace “Ni ka kyaleni, ka sake min hannu” Kalle kallen wajen ya fara yi ganin jama’ah xata tara masa, ya ja ta xuwa daya side din wanda akwai wata mota a parke, ya jinginar da ita da motarsa yace “Baki da hankali ne kike cewa in kyaleki” kuka kawai take tana fixge fixge taki yarda ta kallesa, tsawa

yayi mata yace “Ba magana nake maki ba” Ta kuma fashewa da wani kuka tace “Ni wllh ka sakeni… Ban son haka” da ta ga baxai saketa din ba ta kai bakinta kan hannunsa xata gatsa masa cixo ya xaro ido ya saki hannunta lkci daya ya rungumota jikinsa, nan ma ta hau kiciniyar kwace jikinta amma ta kasa, hakan yasa ta hakura amma bata fasa rusa masa kuka ba kamar ranta xai fita, kukan da take kuma bai hanata jin yanda xuciyarsa ke bugawa ba, lkci daya ta jika masa shaddar jikinsa da hawayenta…

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button