JIDDATUL KHAIR 31

ina ce ita ma mutum ce kamar kai, kamar ni, kamar kowa ma? To don me baxan kwatar mata right dinta ba, ko ka mance akan kwato mata right din nata yasa har naje na aureta? Sannan still a kan kwatar mata right din nata ne yasa na datse auren dake tsakaninmu, and duk wannan wa’axin da kake min ni na ta6a bude baki nace maka da aure tsakaninmu ne?? Ko kuma idan ma da auren gaya maka aka ce xanyi” Ahmad yyi murmushi yace “You are just confusing and disorganizing ur self, shi lamarin da ya shafi addini babu wayo a ciki dai, anyway Ummi is jet angry at you, gwara ko koma yanxu ka dau jiddah ka kai ta can gidan tunda dinner xa ayi yau, daga wajen dinner din sai ka wuce da ita gida, gobe Saturday ka kawota yini tunda baxa ka iya barinta a gidan ba, amma kasan me? Kawai ina ji a jikina xamanku tare da ita ya kusa xuwa karshe” Da ido Abuturrab ya bi Ahmad har ya fita. Motoci biyu ne lafiyayyu suka yi parking kofar gida, El-Basheer ya juya yana kallon warce ke xaune bayan mota ta sha glass yace “Toh ai sai ki sauka mun iso” Da mamaki tace “In sauka fa kace, a kan titin xan sauka d’an nan, motoci sun daina shiga get din gidan ne xan sauka a bakin titi” Yace “Toh ai babu wajen parking a ciki, ke baki ga mutane bane….” Tace “Toh ina ruwana da mutane, har yanxu dama Najeriyan bata canxa ba, mu ba haka ake yi a Masar ba wllh, idan ana biki ko wani shagali wllh dai daikun mutane ake gayyata da daddare, sai a tarfa ma kowa yar gurasar alkama a gefen faranti, a daura kofin madara a gefe,
idan da yar cinyar kaza a saka a gefe shi ma, Allah ba a taro irin haka kamar ana yunwa, shi Kabirun yasan haka mutane xa su cika gidan xai bada mota a kawoni nan salon in gantale? wllh mu bamu saba haka a Masar ba, a gaskiya idan baxai yiwu ba a juyar dani kawai a mayar dani Bauchi, daga baya kada Usman ya kullaceni sai in dawo inyi Allah ya sanya alkhairi, amma wllh baxan sauka bakin titi ba duk k’ura ta kare min abinda babu a Masar, ko shi Usman din bai san ina hanya ba ai Aliyu ya sani tunda na sanar masa ta waya…. Aa gaskiya ba dole Allah ya sanya alkhairi juya mu koma kawai… Mu ba haka ake a Masar ba, komai bisa tsari ake yin sa” Kashe motar El-Basheer yyi yace “Kinga Hajja idan xaki sauka ki sauka ni xan tafi gun daurin aure ne, ga ki ga gate kice baxa ki sauka ba” Bude baki tayi tana kallonsa, can tace “Aa toh gaskiya Najeriya ba wajen xuwa bane, tunda nake a masar ba a ta6a min rashin da’a irin wannan ba, sun san girma da mutuncin tsoho…” Tana kai wa nan ta ciro wayarta fuska
tsuke ta mika masa tace “Kira min Kabirun, ai shi na haifa ba kai ba” Bude motar El-Basheer yyi ya sauka yayi wucewarsa cikin gidan, ta bi sa da kallo baki bude, sai kuma ta sauko ita ma ta bi bayansa. Jiddah ce xaune bedroom din Umma kanta a kasa tana wasa da gefen hijab dinta, Umma tace “Jiddahh” dago kai tayi a hankali tana kallon Umma, Umma tace “Ina sauraronki, idan kika min karya kuma kar ki manta Allah na kallonki, kuma nasan kinsan makomar makaryaci” Lkci daya hawaye ya kawo idonta, Umma tace “Ina jin ki”
Those nulls reading my book for free and still commenting nonsense should know that i owe dem 500…. subhanallah!!! It’s their gut for me wllh. In ma ku biya in ma kar ku biya babu pardon tsakanin mu. My diehard fans kuma we move…. ????