BAKAR INUWA 24

Episode 24
…………Kusan tare tawagar ango da tasu Bappi ta iso tare da forma president. Sai wasu gwamnoni masu sauka dama wanda sukaci zaɓe. Dama wasu tuni sun iso, dan a kaf jihohin ƙasar NAYA arba’in da ɗaya babu gwamnan da baizo ɗaurin auren nan ba da sarakunan gargajiya. Sai waɗanda lalura ta hana kuwa, suma sun bada wakilai. Hakama masu ƙananun muƙamai irin members na majalisa dama na jihohi da cabinets na tsohon shugaban ƙasa dana gwamnoni, attajirai da manyan malamai, kai harma da jama’ar gari da aba’a gayyata ba. Dan a cewarsu dole suzo su kashe kwarkwatar ido, ɗurin auren shugaban ƙasa guda ba wasa ba.
Tsabar cikar da garin yayi sallar juma’a wasu har akan tituna, motoci kam har an rasa wajen fakin. Badan jami’an tsaro dake zagaye da garin ba ma da ba’asan yaya zata kaya ba.
Ango yayi shar cikin wata muguwar ɗanyar shadda da zaman neman addin kuɗin da aka sayeta ma ɓata lokacine. Takalma da agogon hanunsa zuwa hula kuwa dole a kirasu na musamman. Yayi fayau dashi saboda ƴar ramar campaign da har yanzu bai gama cikowa ba.. Ga gyaran fuskar da ya sha da tsagar kan gashin girarsa na tabon ciwo sun sake ƙawata fuskar tashi. Ƙamshi yake na musamman, ga securitys zagaye da shi, kai kace zasu iya karesa daga cika aiken mala’ikan mutuwa ne (????????).
A kusa da kakansa Bappi yay salla a sahun farko, ɗayan gefen haggunsa Mal. Dauda ne hakimi a gefensa. Sai can ɓangaren shugaban ƙasa mai sauka tare da mai-martaba da sarkin Dillo. A yau sarkin musulmi ne ya jagoranci sallar juma’a. Bayan idar da salla aka gudanar da ɗaurin aure kamar yanda shari’a ta yarda. Jikin Mal. Dauda sai rawa yake, dan harga ALLAH a firgice yake ganinsa tsakkiyar manyan mutane da bai taɓa tunani gani ba koda a mafarki. Daya sani ya bari ƙanin nasa ya karɓi auren kamar yanda Inna tace. Amma sai ya bijire dan kar wasu su zata ba shine mahifin Raudha ba. Ko wani yayima Sabilun alkairi saɓanin shi daya cancanta.
A hankali shugaban ƙasa Ramadhan ya lumshe idanunsa lokacin da ake sanar da ƙulluwar auren nasa kamar haka. (Alƙawarin ALLAH ya cika. Domin kuwa Aminatu Dauda Haladu ta zama mata ga Ramadhan B. Hameed Taura. akan sadaki mai daraja. ALLAH ya bada zaman lafiya da zuri’a mai albarka).
Annan take waje ya ɗauki gungunin faɗin amin, yayinda irin su Alhaji Yaro glass ke faɗin (Ba amin ba) a zukatansu. Gefe kuma daga can wajen masallaci aka shiga busa algaitu daga sarakuna domin girmamawa ga shugaban ƙasa. Yayinda maroƙa suka shiga kirari da yabo ga ango kuma shugaban ƙasar NAYA.
Wani irin iska ce mai shiga jiki da sanyi tamkar na tsakkiyar hunturu suka shiga ratsa Ramadhan batare da yasan dalili ba. Tabbas bayajin sonta, yayi biyayya ne kawai ga iyayensa. Shiyyasa ya rasa dalilin yanayin daya shiga a yanzun. Dan lokacin aurensa da Amnah tsintar kansa yay kawai da zumuɗin ganinta a lokacin da aka shafa fatihan aurensu. Saɓanin yanzu da yake jin tamkar an sake aza masa wani nauyine bisa kansa bayan wanda yake ɗauke da shi. Ya shiga sauke ajiyar zuciya a hankali lokacin da Bappi ya rungumesa yana musu addu’ar zaman lafiya da fatan alkairi.
★★★
A can gidan su Raudha ma taƙe yake da mutane har wani baya iya jin zancen wani. Amarya na maƙure jikin Asabe dan zazzaɓi ne mai zafi a jikinta har amai tayi ɗazun saboda takura mata taci abinci da Hajiyar birni tayi. Kwalliya kam sai da hajiyar birnin da Aunty Hannun sukai tamkar zasu halakata dan bala’i sannan ta amince akai mata.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta fito tamkar tauraruwa cikin taurari. Tayi ƙyau harta gaji, musamman da sarƙan gold ɗin wuyanta tai mata wani irin masifar ƙyau da haska fatarta. Duk yanda akaso ta fita tsakar gida ƙi tayi, dan har aka fara guɗe-guɗe a cikin gidan na jin an ɗaura auren bata leƙo ba, sai ma fashewa da tai da kuka mai ban tausayi, dan tasan tata ta kare. Wannan auren tamkar mabuɗin buɗe hanyartane na zuwa lahira ita da wanda ta aura ɗin.
Tana daga kwance tanajin labarin taron mutanen da aka tara wajen ɗaurin auren nata. Sai taji komai ya kuma kwance mata a ƙwaƙwalwa.
★★★
An kammala ɗaura aure mutane suka fara kama gabansu. Wasu garuruwansu suke komawa, wasu Bingo. Kafin la’asar sai yazam tsirarun mutane suka rage sai tulin jami’an tsaro. Shi kansa angon ana idar da sallar la’asar jirgin helicopter yazo ya ɗaukesa. dan tawagar da yazo da ita ta abokansa da abokan kasuwanci tuni sun kama hanyar Bingo. Ibrahim babban abokinsa tun na ƙuruciya ne kaɗai anan tare da shi. Duk yanda Ibrahim ɗin yaso yaje yaga amarya tare da sauran abokai ayi hotuna Ramadhan bai bada fuska ba. Dole suka haƙura tunda sun san gobe idan ALLAH ya kaimu dole ne su ganta a wajen dinner da kuma rantsarwa ranar lahadi.
Ɗagawar jirgin ango babu jimawa jerrrun motoci talatin cif suka sake shigowa garin Hutawa. Sai na jami’an tsaro dake biye da su kai kace shugaba ƙasar akazo ɗauka, sai dai kuma ko basuzo ɗaukar shugaban ƙasa ba sunzo ɗaukar mata kuma amaryar shugaban ƙasa. (???????? wayaga Mino first lady. Lol)
A yanzun kam ma kukan Raudha ta kasa, dan anan ɗin ma babu wanda ya zaunar da ita yay mata faɗa balle nasihar aure ko lallashinta. Damuwarsu kawai karsu rasa motar zuwa kai amarya. Andai kira Mal. Dauda sunyi sallama. koda yazo shima ɗin sai ya ɓige da matsar ƙwalla yana jaddada mata inhar bata zauna lafiya gidan mijinta ba harya sakota tai masa baƙin cikin wannan NI’IMTACCIYAR INUWAR da ALLAH ya tsundumasa sai ya taine mata. Kuma babu shi babu ita. Ko kasheta kullum Ramadhan zai dingayi ana sake busa mata sabon numfashi baice ta nuna masa damuwarta koda a fuska ba.
Jikin Asabe ya ƙara sanyi da kalaman tsohon mijin nata da ayanzu takema kallon wanda baisan ciwon kansa ba. Yayinda tausayin ɗiyarta ya ƙara mamayeta. Sai dai babu yanda zatayi dan su Hajiyar birni sun hanata kowane irin ƙarfin iko na uwa, komai sun mamaye.
Zuwa ƙarfe biyar da wasu mintuna kowacce mota ta ɗauki iya adadin mutanen da zata iya. Yayinda suka fita cikin garin Hutawa a jere motar amarya a tsakkiya. Gaba da baya jami’an tsaro ne.
Wani irin sarƙewa numfashin Raudha ya shigayi alamar Asthma ɗinta zai tashi, dan kuka. ALLAH yasa Hajiya mama dake a motar tai saurin fahimta taja hand bag ɗin Raudha da sauri tana laluben inhaler ta. Da ƙyar ta samota aka shaƙama Raudhan. Sai da numfashinta ya dai-daita suka shiga sauke ajiyar zuciya ita da Hajiya Zuhrah dake tamkar ƙanwa ga Pa. uwa ga su Ramadhan. Dan kuwa Yafendo ce ta haifeta. Itace babbar ɗiyarta, sai dai tana Australia tare da mijinta dake matsayin ambasada a can. A yanzu ma biki ne da bikin rantsar da Ramadhan ya kawosu ƙasar. Komi na kammala kuma zasu juya.
Tuni tausayin Raudha ya sake mamayeta, dan tunda ta ganta ƴar ƙarama take mamakin yanda iyayenta suka amince suka mata aure (kusan su irin manyan nan wayayyu ƴaƴan sai sunci boko sun ƙoshi, wani lokacin ma ba bokon ke hanasu yin auren ba, ra’ayine kawai da tunanin za’a yanke musu jin daɗin rayuwar ƴammatanci ko samartaka. Shiyyasa suke ganin masu aurar da yara 17years zuwa 20 tamkar ganganci sukai????).
___________
*_BINGO CITY_*
Kamar yanda aka nuna ɗaurin auren shugaban ƙasa Ramadhan live a gidajen tv haka aka nuna tahowar amarya da isowarta bingo ma. Inda duk da ɗunbin mutanen nan dake cike da Taura house da wanda sukayo ma amarya rakiya hakan bai hana Anne da ke fama da tsufanta ba fitowa tarbar amarya ita da su yafendo. Fulani na zaune tare da su suka fito amma batako motsa ba. Dan tona irin baƙin cikin da suke ciki game da auren nan ita da Asmah da gimbiya Su’adah ɓata lokacine. Abinda kawai suka sani shine sun tanadama Raudha bama-baman bala’in da sai ta gudu gidansu da ƙafafunta. Dan shi kansa Ramadhan ɗin jiya ya sha masifarsu saboda yace suyi haƙuri shi bazai iya bijirema Pa da Bappi akan maganar auren nan ba.
Aiko sukai masa ca gimbiya Su’adah harda kuka wai Anne ta asirce mata shi bayajin maganarta baijin ta mahaifiyarta da ƴan uwanta. Shi dai bai sake ce musu komai ba, da ga ƙarshe ma kiran wayarsa da akaine tai bailing sa ya samu ya gudu musu. Har zuwa yanzu kuma basu sake ganinsa ba, dan koda ya baro Hutawa kai tsaye wajen meeting ɗin da zasuyi da shugabannin jam’iyya na jihohi ya wuce.