JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 45

ladabi tace “Ina yini” murmushi ya sakar mata yace “Lafiya lau Jiddah, how are you doing?” Tace “Alhmdlh” yace “Daga ina kike haka?” Tace “Gida” Yace “That’s cool…” Bata ko kalli Abuturrab da ya bi ta da kallon gefen ido ba tayi hanyar dakin Hajja, shi ma El-Basheer din da kallo ya bi ta, da sallama ta bude kofar dakin Hajja, Hajja ta amsa ta washe baki ganinta tana cewa “Sannu da xuwa Jiddah” Aisha dake xaune dakin ta bi Jiddah da wani kallo, Jiddah ta tsugunna ta ajiye warmer din hannunta tana kallon Hajja tace “Ina yini Hajja?” Hajja tace “Lafiya lau, shinkafa ta baki ki kawo ko me?” Jiddah ta girgixa kai tace “Aa tuwo ne” Hajja tace “Atoh da kyau, dama shi nake marmari” Mikewa Aisha tayi ta fita daga dakin, Hajja tace “Dama ba wani amfani take min ba, yar kazar da Bashir ya kawo min take ma ni kuma na boye kayana karkashin gado, tunda ba uwarta bace ta

siyo min, shi wan nata Salem tun saukana daga Masar har yau ban gansa ba ance yana Benue, to ni ina ruwana kuma” Ita dai Jiddah bata ce komai ba, Hajja tace “Yanxun nan Bashir din ya fita ai da kun gaisa wllh” Jiddah tace “Ai mun gaisa” Hajja tace “Haba” Gyada mata kai Jiddah tayi, Hajja tace “A ina kika gansa?” jiddah tace “A parlor” Hajja tayi kasa da murya tace “Shi da wa?” Jiddah tace “Ya Aliyu” Hajja ta wani kyabe baki tace “Ashe bai tafi ba kenan, in gaya maki ni dai babu xagin da bai min ba daxu, amma ban biyesa ba don ba shine gabana ba wllh, ni tunda naje Masar na koyi xama da ko wani fitsararre, iyakar hakuri da kauda kai na koyo kam ba laifi a Masar” Jiddah ta d’an yi murmushi kawai, Hajja tace “Toh

ba ruwana dai da wannan, yanxu ki tashi ki tafi bangaren warcan matar da ku ke ce ma Ummi, kiyi sallama sai ki durkusa ki gaishesu da ladabi gaba daya sannan kice don Allah Maman Bauchi kike nema, Idan aka nuna maki ita aka ce gata sai kice mata dama Hajja ce tace in kira ki, Shkkn sai ki taso abun ki ki fito kinji?” Jiddah tace “Toh” Hajja tace “Toh tashi kije” Mikewa tayi ta fita dakin, suka hada ido da Abuturrab a parlor ta

dauke kanta tayi hanyar bangaren Ummi, El-Basheer ya shafa kansa yace “Kasan mene Captain” Abuturrab ya kallesa yace “Idan magana ce da ya shafi koma waye na cikin gidan nan I’m not interested Yarima” El-Basheer yace “A kan Jiddah ne maganar” Mikewa Abuturrab yayi ya wuce dinning area, El-Basheer ya bi sa da kallo yana murmushi… Duk yanda Hajja tace haka Jiddah tayi, Ummi na murmushi ta nuna Mummy tace “Gata nan” Jiddah ta kalleta sannan ta sunkuyar da kanta, Mummy tace “Ki ce mata gani nan xuwa” Jiddah tace “Toh” sannan ta mike ta fita parlon, muryar Aunty ta ji a main parlor tana cewa “Har gashi xa ayi isha baka tafi ba ka bar yar mutane ita daya a gida Aliyu, Wai me yasa bakwa gaya masa gaskiya Bashir” El-Basheer yace “No nayi masa magana Aunty, har ce masa nayi ya tashi in rakasa yace aa yana jiran wani abu ne, ina ta xuba ido in ga me yake

jira” Abuturrab na kallon Aunty daga dinning area da yake xaune yace “Yanxu xan wuce, dama gidan akwai wasu coursemates dinta ne amma nasan may be sun tafi yanxu, i will be on my way” Jiddah dai tayi sum sum ta shige dakin Hajja kafin Aunty ta ganta gabanta na faduwa. Tana shiga dakin Hajja ba a dau lkci ba sai ga Mummy ta shigo ta nemi waje ta xauna tana kallon Hajja tace “Ga ni” Hajja na Murmushi tace “Toh xancen da muka yi daxu dake dai da yamma… kin tuna?” Mummy ta d’an yi shiru, sai kuma tace “Na tuna” Hajja tayi dariya tace “Toh shine, ai dama na maki

alkawari xaki santa yau din nan” Mummy dai sai d’an Murmushi take tana kallon Jiddah dake xaune kasan carpet kasa kasa, Jiddah tace “Hajja ana jirana a waje” Hajja tace “Direba ko?” jiddah tace “Ehh” Hajja tace “To yi maxa tashi kije, kice da Ramlah na gode, Allah ya tashe mu lafiya” Jiddah ta mike tace “Ameen” Sallama tayi ma Mummy sannan ta fita dakin, Hajja tace “Toh ita ce dae Jiddar” Mummy tace “Maa sha Allah” Hajja tace “Aa ba haka xaki ce ba” Mummy tace “To ya xan ce” Hajja ta marairaice tace “Yau naga jaraba, sai kice ehh ai kuwa tayi Allah ya tabbatar da alkhairi Hajja, haka ake magana me ma’ana” Mummy tace “Gaskiya ne tayi kam, Allah ya tabbatar da alkhairi” Hajja tayi Murmushi tace “Yauwa ko ke

fa, in sha Allahu satin da xa a shiga xan xo bauchi gun kabiru” Mummy tace “Toh Allah ya kai mu, bari in je Hajja” Daga haka ta mike ta fita dakin, Hajja ta ta6e baki tace “Oho dai, kya ji da bak’in halinki… In dai jikana na so bbu ruwana da sarautarku ta karya can, yanxu fa sai tace ita a dole gimbiya take so ya aura don ita tana jikar sarkin Gombe, to ni ba ruwana bama haka, kowa mutum me daraja ne a wajenmu, kuma nasan Kabiru da Bashir baxa su watsa min duwatsu a ido ba…” Sai da Jiddah ta fara

xuwa tayi ma Ummi sallama sannan ta fito main parlor, har sannan Abuturrab na tare da El-Basheer, Tana kallon El-Basheer tace “Sai da safe” Yace “Ohkk ba nan xaki kwana ba dama” Tayi murmushi ta girgixa masa kai tace “Kawo ni aka yi” Abuturrab ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya mike ya fita daga parlon, El-Basheer yace “Driver kowa?” Ta gyada kai tace “Shi” El-Basheer yace “To mu je in rakaki” Bata ce komai ba ya mike

suka fita parlon a tare, kofar gida suka tadda Abuturrab tsaye jikin motarsa, Jiddah na kallon El-Basheer tace “Nagode, sai da safe” Ya sakar mata murmushi yace “Aiitt, Allah ya tashe mu lfya” Bude back seat tayi ta shiga driver ya tada motar suka bar layin, El-Basheer na kallon Abuturrab yace “Ya ne, are you ready to go home now” Abuturrab yace “Yeah, Sai da safe” Daga haka ya shiga motarsa ya tada ya bar layin. Abuturrab na isa gida ya fi minti goma xaune cikin mota a parking space kafin ya sauka ya shiga cikin gidan, kulle kofar parlor yayi yana bin parlon da kallo,

plates ne da suka ci cin cin, dubulan da su alkaki da frnds dinta da goran ruwa da lemo, ga bone din kaji a wani plate din a gefe, carpet din duk an marmasa cin cin da dubulan, haurawa sama yayi ya nufi bangarensa ya bude kofar parlon, nan ma dai ledojin souvenirs ne a tsakar parlon da souvenirs din a ciki, ya bude kofar bedroom dinsa, xaune ya ganta gaban mirror daure da towel tana ta shafe shafe, kamshin turare iri iri ya cika dakin, kallo daya tayi masa ta ci gaba da abinda take gently, yace “Aneesah what happened naga parlon downstairs so irritating sannan ga parlona duk wasu tarkacen ledoji, what’s d meaning of that?” Tace “Ohh

xan xo in kwashe souvenirs din but downstairs gaskiya sai gobe cause har yanxu jikina da gajiya sosai, baka ji bayana ba sai ciwo yake min wllh, I’m so stressed out” Calmly yace “No Aneesah, but u can’t leave my parlor that way, I won’t sleeo comfortable, ban sa6a ganin haka ba, Kuma ban ta6a kwana a haka ba” Tace “Captain ba wai fa nace baxanyi bane, xanyi amma gaskiya sai gobe, haba duk gajiyan bikin nan dake tare dani ka tsiro min aiki kuma da daddaren nan” Juyawa yayi ya fice daga dakin ya sauka downstairs, ya wuce kitchen ya dau sweeper da abun kwasar shara ya dawo parlon, sai da ya fara tattara duk plates din da robobin lemo ya kai

kitchen sannan ya dawo ya share carpet din tass, ya kai ya xubar… Xaunawa yyi a parlon for kusan minti ashirin kafin daga karshe ya mike ya kashe wutan parlon ya wuce sama, har sannan ledojin souvenirs din na nan yanda ya barsu, ya kwashesu gaba daya ya bude kofar balcony dake parlon ya watsar da su nan ya tabbatar babu komai xaune parlornsa bayan furnitures sannan ya kulle kofar balcony din ya wuce daki, a gaban madubin ya sameta still, dakin sai wani fitinannen kamshi yake, ta saka wasu tsinanannun kayan bacci, yyi mata kallo daya ya fara cire shirt dinsa ya wuce bandaki. Daure da towel ya fito, yana goge gashin kansa da

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button