JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 46

kunya kawai” Ita dai Jiddah bata ce komai ba ta bi bayanta tana tafiya a hankali, Driver na ta xaune mota yana jiran ranan fitowar Hajja, Hajja ta bude bayan motar tana kallon Jiddah tace “Toh shiga, halan ta kitsa maki karya da gaskiya ne, naga ranki kamar ba dadi” Ita dai Jiddah tayi murmushin karfin hali ta shiga motar, Hajja ma ta shiga ta kulle tace “Ae laifin wa enda suka bar ki a wajenta ne, kowa fa yasan matar bata da mutunci, nan da nan take maka mutum kotu ko ta kaisa gidan yan sanda ayi ta bala’i shi yasa

kowa ke shakkarta a pamily, da akwai wani lkci da ta kira ma Hafsah yan sanda a kan ta xagi yar uwarta Hauwa, aka yi ta dauki ba dadi ana bala’i daga karshe dai Allah ya yayyafa ma abun ruwan sanyi, to idan tana ji da bala’i nima ai A ce, kawai nayi sanyi ne tunda naga su Masar basa haka, ni kuma sai inje in kai masu wani halin daban? Aa shi sa na daina wllh” Jiddah dai bata ce mata komai ba har driver ya kama

hanyar gidan Aliyu. Suna isa gidan xai yi parking a kofar gida Hajja tace “Kai ya haka, baka san waye mai gidan ba, jikana ne fa, ni na haifi ubansa, ka danna masu han kawai a bude maka ka shiga” Yana danna horn mai gadi ya leko, Hajja sai kallon Mai gadin take ganin yaki bude gate din ya karaso gun motar tace “Ji wani yakunanne don Allah, kace masa kakar mai gidan ce kai Bala” Drivern ya sauke glass ya sanar ma mai gadin, yana hada ido da Hajja da ta wani sha kunu ya koma ya bude gate din, Hajja tace “Fitsara suke

ma mutane idan sun samu waje wllh, banda haka shi xai ce bai ga kamanni ba, kawai neman magana malam” Driver ya ja motar xuwa cikin gidan, Kai kana ganin Jiddah xaka xata wani mugun waje aka taho da ita, gaba daya taki sakewa, driver na parking Hajja ta sauka, kafin tace komai Jiddah ta sauka ita ma, Hajja tace “o,o Na shiga uku, yanda kike yi da fuskar nan taki wani ba sai yayi xaton sato ki nayi ba er nan, a gaskiya Ramlah da kyar taga annabi, ni yanxu ta ya xan sa abinda ta kitsa maki kike ta daure fuska haka

fisabilillahi, matar nan fa ta fita hanyata a kasar nan wllh” Jiddah ta kirkiri murmushi tace “Bata ce min komai ba Hajja” Hajja tace “To ni ba ruwana, ta ji da munafurcinta” Daga haka ta fara tafiya xuwa main entrance din gidan Jiddah ta bi bayanta, da sauri Hajja ta juyo tana kallon driver tace “Ka tafi kawai kai, Aliyun sai ya maida mu gida idan muka shirya” Amsa gaisuwar da mai gadin gidan ke yi mata tayi tace “Mai gidan na ciki?” Mai gadin yace “Ehh Baaba yana ciki” Hajja tace “To madallah” Daga haka ta yi gaba Jiddah na biye da ita, murda kofar Hajja tayi bayan ta murda ta ji sa a kulle, ta kalli Jiddah tace “Toh ko

meye na garkame kofa da rana tsaka haka” Bata rufe baki ba aka bude kofar, daga sama har kasa yake kallonsu, sai kuma ya koma gefe still looking at Jiddah, Hajja ta shige parlon abunta, Jiddah dai sunkuyar da kanta tayi taki yarda ta kallesa, ya gama kare mata kallo sannan ya juya ya koma parlon yana kallon Hajja yace “Sannu da xuwa Hajjaj, daga ina haka?” Hajja ta rike ha6a tace “Ohh ikon Allah, aure me seta mutum, yaushe rabon xancen kirki ya hadani da kai Aliyu, yau wai kai ne ke min sannu da xuwa fuska a sake haka” Ya shafa kansa yana murmushi yace “Daga ina ku ke?” Tace “Daga gida wllh, na dai ce bari in xo gidan amarya yau” Ta gefen ido ya kalli Jiddah da taki xaunawa ta tsaya daga bayan kujera, muryar

Hajja yaji tace “To ina amaryar?” Ya dauke kai yace “Tana sama” xata sakko yanxu, yana fadin haka ya xauna yana tambayarta mutanen gida, Hajja ta kalli Jiddah, girgixa kai tayi tace “Ban san haka er nan take ba sai yau da nace ta rakani, ashe ita ma duk kanwar ja ce, Duk Ramlah ta xugeta tunda muka kamo hanya take min wasu abubuwa me nuni da cewa bata son biyoni, ni ai na xata kirkin gaske gareta wllh, to banda haka meye xa ki makale jikin kujera kamar na kawo ki gidan yankan kai? Ni da na sani da Nafisah na taho duk da halinta ko Aisha” Jiddah ta karaso parlon ta xauna kasan carpet a sanyaye, mikewa

Abuturrab yyi ya wuce sama, Hajja ta kalli Jiddah tace “Ba fa baren waje muka xo ba ki saki jikin ki, jikana ne ni na haifi ubansa, ke ma kuma ai kin san sa, kar ki bari matar tayi mana dariya tace mun xo muna ta dari dari a gidan, ki sake jikinki duk abinda kike so kiyi babu wani shakka, wllh bbu me hanaki kin ji” Jiddah tayi murmushin karfin hali, tana son cewa Hajja xata wuce Islamiyya amma ta kasa, don bata san me xai biyo baya ba, Hajja tace “Yanxu tashi ki tafi kitchen ki kwaso mana ruwa da lemo, ki duba robobin garanta ki dau faranti ki debo mana duk abinda kika gani ki kawo” Jiddah ta kasa mata musu amma bata tashi ba, Hajja tace “To tashi mana” Mikewa tayi rai ba dadi ta nufi kitchen din, ta fi minti daya tana kare ma kitchen din kallo, kitchen din na nan yanda yake banda kayan kitchen da aka cika masu tsada, ta dinga kallon wajen wanke wanke dake cike da dirty plates, ta kalli wajen gas taga duk yayi baki alamar ba a gogewa, bin kasan kitchen din tayi da kallon mamaki ganin how untidy it is, daukan plate tayi ta tana kare ma plate din kallo, kawai taje ta dauraye snn ta karasa store ta bude robobin da ta gani ta diba duk

abubuwan ciki, wani tray ta dauka ta daura ruwan gora biyu da cups snn ta fito kitchen din, xaune taga Aneesah a parlor tana kallon Hajja dake ta xuba, Aneesah ta dinga kallon Jiddah da wani irin mamaki, don bata ma san da ita aka xo ba, Hajja tace “Yauwa, kinga kinyi dubara, sannu” Jiddah ta ajiye tray din hannunta ta d’an kalli Aneesah da mood dinta ya sauya lkci daya tace “Ina yini” Aneesah ta hau danna wayarta, Hajja tace “Gaisheki fa take Nanisa kike ko?” Aneesah ta daga kai tace “Ohk, sannu, lfya lau”

Jiddah ta mike ta xauna saman kujera tana kallon Tv dake aiki, mikewa Aneesah tayi tace “Na gaisheki Hajja, ina d’an yin abu ne a sama” Daga haka ta wuce Hajja ta bi ta da kallo, ta rike ha6a murya can kasa tace “Tabdi” Jiddah dai kallon tv kawai take, Hajja tayi kasa da murya tace “Kaji min shegiya, ta sanki ne ta maki wannan walakancin ni ya su?” Saukowar Aliyu yasa Hajja tayi shiru, ta kallesa tace “Amma ba a nan parlon xa a yashe mu ba kamar marasu makabuli ko Aliyu” Yace “Mu je sama” Mikewa Hajja tayi ta kalli Jiddah tace “kwaso mana kayan flawan da lemon” Jiddah ta dau tray din ta mike suka hada ido da

Abuturrab da sauri ta dauke idonta, Tuni Hajja tayi hanyar stairs Abuturrab ya bi bayanta, sai sannan Jiddah ta fara tafiya ta wani hade rai. Dakin da Jiddah ta xauna a lkcn da take gidan ya shigar da su, Hajja tace “Ba shakka, ko mutum xai yi sati a nan babu wanda xai san abinda yake ciki abunsa” Jiddah ta ajiye tray din ta xauna kasan carpet, Hajja ta cire mayafinta ta linke ta bude press ta ajiye, katon jakarta kuma ta rataye sa a bag rack, sai kallonta Jiddaj take da mamaki, ta juyo tace “Ki cire wannan Hijabin ki sha iska abun ki, ai nan ba bakon waje bane, gidan Aliyu ne fa” Jiddah tayi gathering courage tace “Hajja ni fa

makaranta xan wuce yanxu dama, tunda akwai sauran lkci” Hajja ta kalli Abuturrab tace “Kaga jaraba ko, Ramlah ce ta koya mata haka fa kafin mu fito, to ko dai Ramlan nan kanwar uwar Jiddan ce bamu da labari??” Abuturrab dake kallon Jiddah, calmly yace “Baxa ki je ba” Hajja tace “Atoh dai, su makarantar basu san uxuri bane” Wani kallo Jiddah ta masa ta gefen ido lkci daya ta dauke kanta ta daure fuska, Da

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button