JIDDATUL KHAIR 46
mamaki ya dinga kallonta babu ko kiftawa, can ya shafa kansa yace “Wani abincin xa ku ci Hajja?” Hajja tace “Ni ko tuwo aka samu a ban Aliyu” Yace “Ohk” sannan ya juya ya fita, Hajja tace “Ikon Allah, yanxu Aliyu ne ke nan nan da ni kamar wanda nayi ma wani abun arxiki, wllh ni tunda muke bai ta6a girmama ni ya mutunta ni irin yau ba, ohh Allah mai iko” Jiddah dai bata ce mata komai ba. Aliyu ya nufi bangarensa ya shiga parlor ya tadda Aneesah xaune tana shan lemon fata, idan ta sha sai ta jefar da fatan akan
farantin da aka dauro lemukan a kai, yana mata wani irin kallo yace “Aneesah na sha gaya maki idan xaki ci abu plss ki daina ci min a parlor i detest that…” Ta kallesa daga sama har kasa tace “Naga dai ba ni na shigo da lemun ba kai ka kawo abunka ko” Yace “For heaven sake ya xa ki maida min parlor wajen cin abinci, what’s d essence of d dinning area downstairs” Bata kuma basa amsa ba ta dau wani lemun tana sha a hankali tana jefar da kwallon kan faranti, gajeran wando ne jikinta da yar vess, yace “Tuwo grandma dita ke son ki girka mata ynxu” Ta sauke kafarta daga saman kujeran tace “Tuwo?” Yace “Ehh” wani dariya tayi tace “Yanxu kai ka ta6a ganin ko indomie na girka a gidan nan balle tuwo, wllh Aliyu ban san haka
kake da takura ba sai da muka yi aure, kullum sai ka samu matsalar da xaka billo da shi idan ka dawo weekend, kace can datti, nan datti, can wari nan wari?? sannan ma tsaya tukun, ni ka gaya min xaka yi baki a gidan nan? To kaga baka sanar da ni ba, don da ka sanar dani akwai wata kawata chef sai in gayyato ta ta min girki in biyata, amma waye xai maka wannan wahala da tsakar ranar nan, beside ba naga tare da Me siyar da doya da dankali ta xo ba, ai ita ta sa6a wahala sai ta tashi ta shiga kitchen din ta girka masu in yunwa suke ji, don wllh wllh baxan iya ba, in ma ji da gajiyar wankin bayin da kasa nayi daxu mana”
Kallonta ya dinga yi kafin ya juya ya fita daga parlon ta bi sa da wani shegen harara tana dauko wayarta dake ring, d’an xaro ido tayi ta katse wayar sannan ta saka shi a flight mode. Eatry Abuturrab ya tafi ya siyo take away din tuwo da gasasshiyar kaza, Hajja ta dinga washe baki bayan ya shigo masu da ledan tace “Allah maka albarka Aliyu, sannu kaji, matar taka bata yi girki bane?” Yace “Bata yi ba” Hajja tace “Toh Allah ya kyauta, haka fa Hafsah ta dinga yi ma Usman bata son girki” Abuturrab ya kalli Jiddah dake
kwance ta juya masu baya nan ko takaici ne duk ya bi ya isheta tayi fashin makaranta, xaunawa yayi a dakin Hajja tayi ta jan sa da hira yana responding har aka kira la’asar, Jiddah ta sauka kan gadon ta shige bandaki ya bi ta da ido, Hajja ta kyabe baki murya can kasa tace “Uwar rikon ce fa ta kitsa mata karya da gaskiya, kaga ko yar cin cin din da alkaki ta ki ci wllh… Tun daxu sai nukurci take, taki sakewa” Abuturrab yace “Kyaleta, a nan xaku kwana” Hajja ta gyara xama tace “Atoh dai” mikewa yayi ya fita don xuwa yayi alwala ya wuce masallaci. Har kusan isha Jiddah bata ga alamar Hajja xata ce su tashi su tafi ba, ga wani
abincin Abuturrab ya kawo, bayan ta idar da sallah tana xaune kan darduma a hankali tace “Hajja wai baxa mu wuce ba?” Hajja tace “Ke ba fa gidan 6are na xo ba, bari kiji in gaya maki, ni wllh bansan bakin hali gareki ba sai yau, gidan jikana ne nan fa, babu ruwanki da sanda xa mu wuce, ke dai iyakarki ba rakiya ba, xan kawoki inda xa a cuceki ne? Ni fa na rainesa yana karami, idan ban xo gidansa ba ina xanje, kuma a nan xan kwana wllh don xuwa gobe da safe nake son ganin iyakar xabiyar matarsa da ta xo ta gaishe mu a tsattsaye har yanxu bata sake shigowa ba, dadin abun kuma jikana ya saurareni gashi muna ta hiran
yaushe gamo da shi don haka sai Allah ya kai mu gobe xan nuna mata ni er banxa ce” Jiddah ta ji kamar ta fashe da kuka, lkci daya hawaye ya kawo idonta ta mike ta koma can karshen gado ta xauna, Hajja ta kwashi take away din da suka ci abinci ta fita xuwa kitchen, Sai a sannan Jiddah ta fashe da kuka ta hade kanta da gwiwa, bayan kusan minti goma Hajja ta shigo dakin tana hura hanci tace “Tirrrrrr, ashe kazama Aliyu ya auro? Ke kinga kitchen dinta duk wari kuwa? Wllh da nasan haka kitchen din yake ni baxan ma fara shan ruwan gidan nan ba sai dai a fita a siyo min a waje, a garin yaya mace xata bar kitchen dinta
haka ni Dije? Wllh sai da tsoro ya kamani, yaushe Aliyu shi ma ya lalace da son kazanta? A yanda na san sa a da fa har tunani muke ko aljanun tsafta ne suka auresa, to naga duk ya lalace ya xuba ido kitchen dinsa ya ru6e duk wari” Jiddah dai bata ko kalleta ba, Hajja ta xauna tayi shiru alamar dai tunanin kitchen din take kuma abun ya dameta, can tace “Tirrrr” Sai kuma tace “Huhuhu kazama ce wllh, kwanukan duk wari naji suke, ni kamar har da kiyashi naga suna yawo a kitchen din, ga dai kitchen har kitchen” Sai kuma ta
kalli Jiddah murya can kasa tace “Wllh ban san ta ina xanyi wanke wanken bane kar inje in jika kitchen din abu ya kara lalacewa ai da nayi, amma ke tunda naga duk kun saba ki daure domin bama tsafta hakkinsa kije kiyi wanke wanken nan, wllh babu kyan gani kinji na rantse, to ko dai ba mace ya auro ba” Jiddah tace “Hajja bata sa ni in mata wanke wanke ba fa” Hajja ta kara yin kasa da murya ta marairaice tace “Na sani
er nan, duk don a fita hakkin tsafta ne, wllh da Masar ne kitchen din nan ya tashi aiki, sai ma a iya rushesa kawai, domin Allah ki tashi ki je ki gyara, ai ba don yar iskar xa muyi ba, kawai don Allah, don tsafta xa mu yi” Jiddah ta dinga kallon Hajja, Hajja ta mike tace “To ai Shikenan bari in kwashi kwanukan in fita da su tsakar gida in wanke don a gaskiya idan xa su kwana a haka ni baxan kwana gidan nan ba ba ruwana,
baxan ci amanar tsafta ba a gaskiya” Ganin da gaske fita xata yi Jiddah ta mike tace “Toh naji xanyi” Hajja ta koma ta xauna tana huci, Jiddah ta fita dakin, babu kowa parlon ta shiga kitchen din, tafi minti uku a tsaye tana tunanin ta inda xata fara, sai yamutse fuska take, can dai ta fara hada kayan wanke wanken waje daya.. Har karfe tara Jiddah na kitchen din, lkci daya kitchen din ya dawo fess duk ta gyara ko ina ta goge, tana wanke wajen sink din aka dauke wuta, lkci daya kuma taga kamar an kunna hasken waya a
parlor, ko gama dauraye wajen bata yi ba ta kashe tap din xata fito kitchen din da sauri, ta kusa cin karo da shi, ta ki tsayawa xata bi ta gefensa ya rikota, kwace hannunta take son yi, ya ja ta xuwa kitchen din ya kulle kofar ya jinginar da ita jiki, ta buda ido sosai tace “Meye haka” ya kife wayarsa saman cabinet din
kitchen ta daina ganin hasken komai, a tsorace tace “Wai meye haka” yace “Me ya hanaki cin abincin da na kawo maku??” Xuciyarta na bugawa tace “Ni wllh na ci kadan, ai nace mata na koshi ne, amma kuma na ci ai…” Gaba daya ta daburce, yace “To ni dodonki ne da kika ce baxa ki kwana a gidana ba” Ta dake tace “Toh ai ba dole sai na kwana a gidanka ba, ko ya xa ayi in kwana a gidan wanda ban sani….”
xaro ido Jiddah tayi jin goshinsa a nata tana juyo breathing dinsa, sai kuma ta rufe ido a tsorace tana turasa da duk karfinta tana son kwace kanta amma ko gezau, bata ankara ba sai ganin abun tayi kamar a mafarki, and he gave her a perfect french kiss da ya gigitata ya rikitata, ba don rikon da yayi mata ba da tuni ta kai kasa dama.