JIDDATUL KHAIR 51
Abuturrab ya dauke kansa, Umma tace “A hado maka da abinci ne?” Girgixa kai yayi yace “Aa” Jiddah na ba Huraira sakon Umma ta fito ta wuce dakinsu, Huraira ta fito da ruwan ta ajiye ma Abuturrab, knocking aka yi bakin kofa Huraira ta karasa bakin kofar ganin driver ne ta kalli Umma tace “Umma Musan ya dawo” Umma tace “Ohk to ya jirani” Huraira ta koma ta gaya ma drivern abinda Umma tace, Abuturrab ya dau bottle water ya bude yana kallon Umma yace “Umma fita xa ki yi?” Umma tace “Ehh yanxu kuwa” Tana
[indeed-social-locker sm_list=’fb’ sm_template=’ism_template_9′ sm_list_align=’horizontal’ sm_display_counts=’true’ sm_display_full_name=’true’ unlock_type=2 locker_template=8 sm_d_text=’
This content is locked
Share This Page To Unlock The Content!
‘ enable_timeout_lk=1 sm_timeout_locker=1200 reset_locker=1 locker_reset_after=1 locker_reset_type=’days’ ism_overlock=’default’ ]
fadin haka ta mike ta wuce dakinta ta dau hijab da purse dinta, tana fitowa parlon shi dai bin ta kawai yake da kallo, ta xauna saman kujera ta kira Huraira, Huraira na xuwa tace “Kira min Jiddah” kallonta kawai Abuturrab yake, Huraira ta wuce daki sai ga ta sun fito tare da Jiddah, Umma tace “Dauko Hijab dinki ki
rakani” Jiddah tace “Toh” sannan ta juya, Abuturrab dai sai kallon small mum din tasa yake, banda danna wayarta babu abinda take, Can ya shafa kansa a hankali yace “Umma ina xa ku?” Tace “Kwana biyu banje na gaida Yaya ba, can xanje yanxu” Yace “Nima can, xan tafi na dai fara xuwa nan in gaisheki ne” Umma
tace “Allah sarki, ai ka kyauta” Yace “Toh in ajiye ku can din?” Umma tace “Idan ka ajiye mu wa xai maido mu, gwara mu tafi da driver ko awa nawa xanyi xai jira in gama sannan ya maido mu gida” Abuturrab yace “Ae xan kai har bayan isha a can, duk sanda xa ku dawo sai in dawo da ku sannan in wuce gidana” Umma tace “Toh ai shkkn idan ba takura” Umma ta mike ta wuce kitchen don juye pepper soup din da tayi ma
Ummi, Jiddah ta fito daki sanye da hijab din da ta xo da shi, hada ido suka yi da shi, ta juya da sauri ta wuce kitchen, babu 6ata lkci Umma ta fito kitchen Jiddah na biye da ita rike da warmer din pepper soup, Abuturrab ya mike yace “Ina jira a mota Umma” Umma tace “Eh yanxu xa mu fito” Umma ta gama ba
Huraira instructions din da xata bata sannan suka fito parlon da Jiddah, driver dake tsaye parking space Umma ta nufa tace “Musa kawai kayi tafiyarka na samu ma wanda xai ajiye ni can gidan” cike da ladabi Musa yace “Toh shkkn Hajiya, Allah ya tsare” Umma tace “Ameen, sai gobe kenan” Daga haka ta nufi gate Jiddah na biye da ita a baya being very careful kar ta 6ata hijab dinta da abinda ke cikin warmer din
hannunta, back seat Umma ta bude ta shiga, Jiddah ta shiga bayan ita ma ta kulle motar, Umma na kallonsa tace “Idan ka samu wajen siyar da fruits a hanya” Yace “Ohk” daga haka ya tada motar ya bar layin. Dai dai wajen masu siyar da fruits yayi parking kamar yanda Umma ta umarcesa, Umma ta ciro kudi ta mika masa tace “Apples kawai sai grapes” Ya kalli kudin ya sauka motar yace “Akwai kudi a jikina” daga haka ya kulle motar ya tafi gun masu fruits din, bayan some minutes ya dawo, ya bude back seat yana
mika ma Umma ledan amma Jiddah yake kallo, Umma ta kallesa tace “To ita kake ba ledan ko ni Aliyu? idan ita ce sai ka xaga ta can mana” Tana fadin haka ta amshe ledan xata rufo door din motar, shi dai bai ce komai ba ya koma driver seat, Jiddah dai na makale at the far end of d car don bata ma son su hada ido mistakenly ta madubi. A kofar gidansu yayi parking, Umma ta sauka, Jiddah ma ta sauka rike da
warmer din ta bi bayan Umma da sauri, Direct bangaren Ummi suka tafi, Jiddah dai na xaune kasa bayan sun gaisa da Ummi da ta fito daga daki, Ummi tace “Toh ki xauna kujera mana Jiddah” Murmushi kawai Jiddah tayi bata ce komai ba, Umma tace “Ko a gida ma kafin ta xauna a kujera sau daya tayi xamanta a carpet ya fi a kirga” Ummi tace “Ikon Allah, to ina su Maimoon?” Umma tace “Suna dawowa boko suka
tafi gidan Hajiya Zainab” Ummi tace “Haba, tana garin nan dama?” Umma tace “Aa last week ta shigo” Ummi tace “Allah sarki” Umma tace “Jiddah kuma ai nace maki tana gidan Ramlah ta fara karatu ko?” Ummi tace “Ehh haka kika ce, Allah ya bada ilimi me albarka da amfani” Umma tace “Ameen, Hajiya Hajja fa? Kwana biyu ba a je min ba” Ummi tayi murmushi tace “Shekaranjiya ta tada rigiman a kai ta gombe
wajen mai martaba, amma yau kuma wai sai naji suna hanya kilan ma sun kusa, mun yi magana da El-Basheer din da safe” Umma ta tabe baki tace “Toh Allah ya kyauta, meye amfanin tafiya me nisan da ko kwana uku baxa ayi ba” Dariya kawai Ummi tayi, aka bude kofar Abuturrab ya shigo da sallama, xaunawa
yayi ya gaida Umminsa, Ummi ta amsa tana kallonsa, Umma tace “Shi ya kawo mu, yaje can gida gaisheni shine yace bari ya ajiye mu tunda nan xa mu xo” Ummi tace “Maa sha Allah, Ina matar taka??” Yace “Tana gida” Ummi tace “Toh yayi kyau, shekaranjiya ma ai ina jin ta xo nan wajen Hafsah, amma ni dai ban ganta
ba su Nafisah ke gaya min” Abuturrab dai yyi shiru bai ce komai ba, Umma dai ta ta6e baki tana kallon Tv, Ya kalli Ummi yace “Ummi akwai abinci?” Umma ta wani kallesa tace “Amma da nayi maka magana a can gidan me ka ce min?” Murmushi kawai yayi, Ummi ta kalli Jiddah tace “Akwai abinci kitchen ki dibar masa
Jiddah” Sosai gaban Jiddah ya fadi ta kalli Ummi, Umma dai bata ce komai ba, Jiddah ta mike a hankali ta nufi kofa, Abuturrab na kallon Umminsa yace “Aunty na nan?” Ummi tace “Sai kaje ka duba” Bai ce komai ba, sai kuma ya mike yace “Bari in gaisheta in dawo yanxu” Daga haka ya nufi kofa daga Ummi har Umma suka bi sa da kallo, Umma tace “Mu je ciki akwai magana yaya” Ummi ta mike tace “Toh” a tare suka shiga
bedroom din Ummi… Abuturrab na fitowa bangaren Ummi kitchen ya nufa direct, Jiddah ta juya da sauri jin an shigo kitchen din, suna hada ido ta juya masa baya, kana ganinta kasan duk a tsorace take ta ma rasa me take yi, sai kuma ta tuna miyan ganyen xata xuba a bowl, tana cikin xubawa taji muryarsa yace
“Saboda nace ki daina gaisheni shi yasa idan kika gan ni sai ki min kallon banxa ki wuce right?” Kasa ce masa komai tayi amma banda bugawa babu abinda xuciyarta yake gashi taki juyowa, bude kitchen din aka yi ta juya da sauri, Mai aikin gidan ce ta shigo ganin Abuturrab ta koma xata fita, da sauri Jiddah ta ajiye bowl din miyar hannunta ta fice ta kofar da tagani a kitchen din wanda ke a bude, da mamaki ya bi
ta da kallo, har ta xagayo gaban compound din gidan waige waige take ko ya biyota amma bata ga haka ba, mai gadi ya bude gate sai ga mota ya shigo, ko parking din motar ba a yi ba, motar na tsaye tsakar
compound din aka bude back seat sae ga Hajja ta sauko da katon jakarta, Jiddah ta karasa gunta don amsan jakarta, Hajja sae kallonta take can tace “Wannan kafafuwa naki haka kamar a Masar, kinsan su ma haka kafafuwansu yake farare tass da yake larabawa ne, to ke kuma ba balarabiya ba sae dai ko sadaka
[/indeed-social-locker]
yalla” Jiddah dai tayi murmushi ta amshi jakar Hajja tace “Sannu da dawowa Hajja” Hajja tace “Yauwa wajen d’ana sarkin Bauchi naje, ai da ke nayi niyyar xuwa Usman ya hanani wai inyi ta kaina, banda haka da na kai ki kinga ikon Allah, to ina takalman naki kike yawo haka ke kuwa? Ita mace ae ba a santa da
yawo babu takalmi ba, barin ke da taki kafar kamar ta ‘yan Masar” El-Basheer ya sauko daga mota yana kallon Jiddah, Jiddah ta d’an kallesa tace “Ina yini?” Yayi murmushi yace “Lafiya lau Jiddah, how are you