BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 20

FARUQ POV.

Mama ta sauke ajiyar zuciya tana jinjina lamarin Rafi’a.

“Faruq ka saka mata ido, duk abun da take tana yi saboda ta bata maka rai ne, kuma komai na rayuwar duniya jarabawa ne, ko da arziki ne Allah ya baka ya ga yadda zaka iya rike su, balle kuma talauci, da muguwar mata”

“Wallahi Wani lokacin Rafi’a tana bani mamaki, ita kamar bata san Allah ke yi ba? Shi zai yi ma kansa arziki ne? Sai ta rika abu kamar ba yar’uwa ba?”

Aisha ta dana da nata. Sai Faruq ya kalleta.

“Wani lokacin ina jin kamar na sake ta na huta, sai dai idan na tuna irin wahalar da mahaifinta yai da ni a karatuna kuma ya dauki yarsa ya aura min duk da a lokacin bana da komai, sai na kamar idan na sake ta ban kyauta masa ba”

[indeed-social-locker sm_list=’fb’ sm_template=’ism_template_9′ sm_list_align=’horizontal’ sm_display_counts=’true’ sm_display_full_name=’true’ unlock_type=2 locker_template=8 sm_d_text=’

This content is locked

Share This Page To Unlock The Content!

‘ enable_timeout_lk=1 sm_timeout_locker=1200 reset_locker=1 locker_reset_after=1 locker_reset_type=’days’ ism_overlock=’default’ ]

“Haka ne, wani abu dole a daga mata kafa saboda mahaifinta, domin mutumen kwarai ne, kuma na tabbatar da yana raye Rafi’a ba zata maka wani abun ba, kasan Umma daman ba son auren take ba tun farko shiyasa komai tai bata ganin laifinta, amman kai hakuri Inshallah sauki yana tafe”

Ya ja wani dogon numfashi ya sauke.

“Ni da har na yanke shawarar na bi Yusufa mu tafi nijar gurin ginar zinarina nan”

“Nijar kuma?”

Cewar Mama ciki damuwa.

“Eh kin ga masu zuwa suna samowa ba laifi, kuma ba kasan inda rabonka yake ba, amman zama haka ba zai yi Mama, hausawa sun ce idan hagu ta ki sai a koma dama”

Mama ta girza kai.

“Wallahi bana son tafiyar nan nesa Faruq, da dai ka hakura mu ga abun da Allah zai yi”

“Mama duk inda rabonka yake sai ka tararda shi, ko kuma ya nemeka, kuma abun da Allah ya rubutawa bawa ko a ina yake zai same shi, na san dai ba zai wuce ki ce kina jin tsoron hanya ba ko abunda zai faru da ni, kawai ki min addu’a”

“To Allah ya zaba mana abun da yafi zama alheri, idan tafiyar Alheri ce Allah ya shige maka gaba”

“Ameen idan Allah yasa naje ko na siyen fili na samu ai na samu”

“Haka ne, amman kudin motar zuwa can fa?”

“Har cin abinci da komai zan iya kashe 20k haka Yusufa ya fada min, kuma yace ana kwana uku kamin a samu isa, wannan kudin da ban biya haya ba zan iya cire na mota ciki sai kuma sauran kuma na siya ma Rafi’a abinci na bar mata kamin mu tafi kuma mu ga abun da Allah zai yi”

“Toh Allah ya shige maka gaba”

“Ameen”

Ya fada yana mikewa tsaye sai kanwarsa ta kalleshi.

“Ya Faruq ance fa rame ake shiga, ko. Kwanan baya na ji ance rame ya rusga da wasu”

Murmushi yai.

“Allah shi ke tsarewa ai, ku dai kui ta mana addu’a”

“Toh Allah ya tsare, yasa arzikinka na can”

“Ameen ya Rabb”

Ya amsa sannan yai musu sallama ya fice, ko da ya isa gida har ta gota, a bude ya samu kofar gidan, sai ya shiga da sallama ya maida kofar ya rufe sannan ya shiga falon, sai ya same ta tana waya sai dai ganinsa yasa ta sauke wayar ta kalleshi.

“Sannu da zuwa”

“Yauwa, ya gidan?”

“Alhamdulillah”

Sai ta tashi ta nufi inda abincinsa yake ta dauko masa ta aje masa tare da ruwa.

“Ina Sultan?”

“Yayi bachi”

Ta amsa sannan ta zauna kusa da kujerar da yake zaune, kallonta yake har ta zauna din, gaba daya yau ta canja, daman can fara fes amman haskenta and yau ya karu sai wani sheki take tana ta kamshin hummura mai tsada. Dauke kansa yai ya maida dubansa gurin abincin data aje masa yana hade yawu, rabon da wata mu’amalar aure ta shiga tsakaninsu har ya manta, domin bata yarda idan ma ya neme ta, idan ya matsa sai tace ga ciki ba zata iya ba, shi kuma baya son yi mata da karfi hakan yasa ya dauke mata kai ta wannan bangaren ba dan baya bukata ba sai dan ba zai iya ja’inja da ita ba.

“Rafi’a ina ta shawara da kuma neman zabin Allah”

Ta kalleshi da sauri a tunaninta ko zai fada mata cewar daya faga cikin aikin da yake Applying ne wani ya fito.

“Na me? Aikin ka samu ne?”

“Aa, ina shawarar zuwa nijar ne?”

Wani irin yatsine fuska tai kamar wanda tai arba da abun kyama.

“Nijar fa kace? Ba dai gurin ginar zinari ba ko?”

“Can mana”

“No nonono, Wallahi ba zan yarda ba, so kake ka ja min abun magana a gari? Ace mijina ya tafi gurin ginar zinari? Talaucin har ya kai nan? Aa Wallahi ba zaka je ba”

“Shi zuwa ginar zinari zunubi ne? Wace irin magana ce wannan nan?”

“Kana tafiya za a ce talauci ya matsa mana har ka bar gari ka tafi nema nijar, ka ja min abun magana, kawaye na mazajensu daga masu aiki a kamfani sai banki sai ma’aikatun gobnati, ni kam ba zan iya ba Wallahi”

“To sai na fasa saboda ke nan? Ni na riga na yanke shawara, kuma na zo na fada miki ne saboda na baki hakkinki”

“To Wallahi ba zan yarda ka je ba, Wallahi sai dai ka sake ni ka tafi na san ba mu tare”

Dubanta yai irin duba na mamaki.

“Rafi’a me kike son ki zama? Ke kin isa ki yi ma kanki arziki ne, da abu kadan zaki fara cewa talauci?”

Sai ta mike tsaye domin ya fahimci da gaske take.

“Wallahi Faruq, na rantse da Allah ba zaka tafi nijar ginar zinari da aurena ba, sai dai idan tafiya ce zaka yi ta har abada, wanda babu dawowa, wai kai baka da zuciya ne? Baka san Annabi ya faku ba, na gaji da abun kunya Faruq, na gaji, aurena dole ne? Ni kadai ce mace a duniya nan ne? Ba zan iya ba, ga danka nan yayi wayo amman ka kasa saka shi makaranta, wannan da zan haifa ma na san dan taure zaka yanka min”

“Sai ki saki kanki ai, ba saki ba? Ba zan saki ba kuma sai na tafi nijar din ki mutu, ina hakuri ne dake kawai saboda Mama da kuma mahaifinki”

Ya fada yana mikewa tsaye, sai ta sa gabansa.

“Wato ka fito gurin bakar tsohuwa ta kitsa maka abun da take so a kai…”

Bata karasa ba ya wanke mata fuska da mari sai da ta fadi zaune. Ta fashe da kuka.

“Faruq ni ka mara?”

“Har abun da yafi mari zaki samu, matukar iskancinki da rainon wayo ya kai ki ga taba mahaifiyata, ai ko da ba ta hada komai dake ta cancanci girmamawa saboda tana sarakuwarki balle tana a matsayin kanwar mahaifinki”

“Ita bata san da zumuncin bane ta barka kana ta cutar da ni? Ba zan iya ba, na ce bana so ka sauwake min mana”

Har yayi kamar Ya bude baki yace na sakeki sai kuma wata zuciyar ta hana shi. Be sake kulata ba ya shiga bedroom din, bakin gado ya zauna yana kallon Sultan dake ta bachi ya kai hannu ya shafa shi, makomar dansa yake zubawa idan har ya sake ta rayuwarsa zata zama abun tausayi, domin zaman zai zame masa a tsakanin gida biyu, gidan mahaifinsa da kuma inda Mahaifiyarsa. Tsabar bacin rai da tunani be ci abincin ba ya kwanta kusa da dansa, Baturiya kuma ta kwana a falo.
Washe gari waina ya siyo musu abun kari kasancewar aljihunsa da dan nauyi irin na masu nema yau da gobe, bata gaishe ba tun da garin Allah ya waye, sai dai hakan be hana shi ce mata zai fita ba, da harara ta bishi babu Allah ya tsare balle addu’ar alheri.

“Allah yasa kai hadari ka mutu..”

Ta fada bayan ta ji karar rufe gidan, sannan ta tashi ta bude wainar ta zubawa Sultan, ita kuma ta nufi wayarta ta dauka ta kira Fahat, ringing biyu ya dauka.

“Fee’at”

Sai ga murmushi a fuskarta kamar ba ita ba, bata kula da Sultan ba ta cigaba da wayarta tana masa kalaman soyayya kamar yadda shi ma yake mata. Sun kusa awa daya suna abu daya sannan sukai sallama tana masa kiss a wayar, duk abun da take Sultan na kallonta sai dai ita bata lura da hakan ba. Fitowa tai waje ta fara gyara gidan domin Ramlee ta fada mata karfi goma za su hadu. Ko da tara tai Baturiya ta gama komai har ta shiga ta yi wanka. Sai da ta shirya sannan ta kai Sulta makota ta dawo gidan ta kara daukar wasu kayan matan ta sha daman Ramlee ta nuna mata wadanda zata sha idan tana kusan tafiya.
Tara da rabi kiran Ramlee ya shigo wayarta, jiki na rawa ta dauka kamar ba ita ce ta gama jin tsoro ba a jiya.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button