JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 51

doing?” Tace “Alhmdlh” Hajja tace “To ki tsaya ku gaisa a tsanake idan kun gama sai ki taho min da jakata kin ji” Daga haka tayi wucewarta, Jiddah ta d’an kallesa, Murmushi yayi yace “Ya karatu?” Tace “Lafiya lau” yana kallon kafafuwanta yace “Ina takalmanki” Tace “Aa ta kofar kitchen na fito ne” Yace “To muje ciki”

Tana gaba yana biye da ita suka wuce parlor din gidan, Abuturrab na xaune parlor Hajja na tsaye sai basa labari take, shi kam ko kallonta baya yi banda danna wayarsa da yake, Jiddah ta shigo parlon tare da El-Basheer, Hajja ta kallesu tace “Har kun gama gaisawa?” Jiddah dai bata ce komai ba tayi hanyar dakin Hajja da jakarta bayan ta saci kallon Abuturrab, Hajja ta bi bayanta murya can kasa tana cewa “Ki daina abu kamar er kauye ‘yar nan, kamata yyi ki buda baki kuyi tadi da shi sosai, ba wai ki ta sunkuyar da kai

kina murmushi ba, ubansa fa shine sarkin Bauchi gaba daya, kuma ni na haifi uban, na ya6a da hankalinki ne shi sa nake ta cusa masa ke, amma naga ke kuma kina abu kamar wawa, haba kar kyanki ya tashi a banxa mana er nan” El-Basheer na kallon Abuturrab da ya ki dago kai yace “Na kira ka daxu wayarka a kashe” Abuturrab ya kallesa yace “Ohk kilan na kashe then, ya hanya” El-Basheer yace “Wannan mata ta fiye fitina wllh, i have to drive her all the way from kano, and in sha Allah gobe xan koma Bauchi”

Abuturrab ya mike yace “Toh muje can gidana, tafiya xan yi nima” El-Basheer ya d’an buda ido yace “Ae ban gaisa da su Ummi da Aunty ba” Abuturrab yace “Duk basa nan, if u are going mu tafi yanxu don ni tafiya xanyi, gobe idan xaka koma Bauchin sai kaxo kayi masu sallama da safe” El-Basheer ya d’an shafa kansa yace “Ohk, i can even still come back at night in gaisa da su” Abuturrab yace “Eh xai ma fi” Daga haka suka fita parlon, a hanya Abuturrab yayi masu take away din abinci, El-Basheer na kallonsa da

mamaki yace “Aneesah bata yi girki bane?” Abuturrab yace “Ehh bata jin dadi” El-Basheer yace “Toh Allah ya sauwake” Abuturrab yace “Ameen” sai da suka kusa gidan Abuturrab ya fara xullumin condition din da xai je ya tarar da gidan nasa with El-Basheer. Amma ga mamakinsa yana bude kofar parlor yaji wani kamshin turaren wuta me dadi ya doki hancinsa, ga sanyin Ac da ya cika parlon, suka shiga ciki tare da El-Basheer, the parlor was more than clean, banda kyalli babu abinda kayan kallon parlon suke, bin ko ina

Abuturrab ya dinga yi da kallo yana mamakin anya gidan nasa ne kuwa wannan, El-Basheer ya xauna yana sauke wani numfashi yace “Gidan Amare daban yake, so cool” Daga sama Aneesah ta sauko da atamfa riga da skirt da ya kamata ta kashe dauri, fuskarta kuma tayi light make up, tayi kyau sosai kamar a sace a gudu, da murmushi ta karaso cikin parlon tace “Sannunku da xuwa, bako muka yi captain” El-Basheer yace “Fatan mun same ku lafiya amarya?” Tana ci gaba da murmushi tace “Alhmdlh, u are welcome” karasawa

tayi kusa da captain ta xauna gefensa tace “Welcome my captain” Yana gyara xama yace “Yauwa thank you” Murmushi bai gushe a fuskarta ba ta mike ta wuce kitchen, sai gata ta dawo da ruwan gora biyu da drink sai cups, ajiye masu tayi tace “Ga ruwan sanyi” El-Basheer yace “Thank you Aneesah” Ta xauna one sitter tana kallon captain dake ta danna wayarsa, El-Basheer ya dau ruwa ya fara sha, tace “A kawo abinci yanxu?” Sai da captain ya daga kai ya kalleta jin abinda tace, tayi fari da ido tace “Eh, ko sai anjima” El-

Basheer yace “Aa kawo min ni dai, Captain sai ya ci take away din da yayi” Ta mike ta dau ledan take away din ta wuce kitchen tana cewa “Shi ma baxai ci ba, ga dai abinci nayi” Captain ya bi ta da kallo, manyan warmers kusan biyar ta kawo parlon ta dire kan carpet, ta koma ta dauko plates, da serving spoon ta ajiye masu tana murmushi tace “Bismillah” daga haka ta wuce sama, El-Basheer ya sauka kasan carpet yana bude warmers din, Abuturrab ma sae kallon warmers din yake, wani lafiyayyen fried rice ne a warmer daya, dayan kuma wainar shinkafa sai tiriri yake, ga hadadden miyar taushe dake ta kamshi, wani warmer kuma peppered chicken ne that looks so enticing, last warmer din pepper soup din kayan ciki shi ma sai kamshi yake, kallon foods din kawai Abuturrab yake, tuni El-Basheer ya fara diban abubuwan da xai diba, Abuturrab ya ci gaba da danna wayarsa, sai kuma ya mike ya wuce kitchen, ko ina fess a kitchen din babu kayan wanke wanke, ya fara dube duben inda xai ga take away din da ta dauke a parlor bai gani ba, hakan ya sa ya bude kofar kitchen yaga a bola ta jefar, ya fi second biyar yana kallon ledan abincin kafin ya

gyada kai ya kulle kofar ya fice daga kitchen din, ya dawo parlor ya xauna, El-Basheer yace “Kai baxa ka diba abincin ba?” Ya girgixa kai yace “Na ci abinci a can gida ai” Yace “Ohkk” Abuturrab da El-Basheer suna tare parlon har kusan magrib, ita dai Aneesah na sama, duk da yunwan da Abuturrab ke ji amma ya ki cin abincin, ana kiran magrib suka yi alwala a toilet din downstairs, Abuturrab yyi mamakin ganin toilet din ma fess, ana idar da sallah bayan sun fito masallaci El-Basheer yace ma Abuturrab xai koma can gida don su gaisa da su Ummi tunda gobe da safe xai koma, Abuturrab yace “Toh bari in dauko makullin

motar” yana shiga ciki ya dauko makullin motarsa ya fito suka wuce can gidan, El-Basheer ya nufi bangaren Ummi don gaisheta, shi kuma ya tafi dakin Hajja, Hajja na gyara labulayenta Jiddah kuma na durkushe tana sa turaren wuta a garwashin da Mai aiki ta kawo ma Hajja a kasko, Hajja na ganinsa tace “Aliyu wllh bauchi da naje baka ga wata yar yarinya da na maka sha’awa ba, duka duka yarinyar bata wuce Jiddan nan ba, amma abinda yasa ban ce masu komai ba saboda ban san irin tsaftar yarinyar ba, kaga

yanxu shi Bashir warce nake sa ran hadashi da ita nasan tsaftarta, to ita wancan gaskiya ban sani ba” Abuturrab dai bai ce mata komai ba, Hajja tace “Duk kwanan nan da kai nake kwana a raina nake tashi, saboda nasan kana cikin jarabawar auren mata kazama, amma in sha Allahu ka sha kurumin ka ina nan ina maka fafatuka, yanda na samar ma Bashir yar kirki me tsafta kai ma haka xan samo maka, Shi kansa Kabiru

yyi farin cikin wannan xabin da nayi ma Bashir, uwarsa kuma babu abinda xance da ita sae dai ta ci kanta ni ba ta ita nake ba… Yanxu Usman nake jira ya dawo inji ynda xa a yi, ko shi ne xai xama waliyyin yarinyar to… Bashir kuma yace min shi dai a shirye yake ko gobe ne a daura, amma ae ba gaggawa ake ba ina

laifin ma nan da sati uku” Abuturrab yace “A ina kika samar masa matar?” Hajja ta wani kallesa tace “Aa wannan kuma ba ruwan ka ae, wllh Kabiru yace min ya amince indai Bashir din na so, ae karfin xuwa na Bauchin kenan…” Abuturrab ya shafa kansa ya ki cewa komai, can ya kalleta yace “Toh ban ci abinci ba, yunwa nake ji” Hajja tace “Aa ba ma ga yunwa ba a gidan nan, ga dai abinci kaca kaca ka wani ce yunwa,

bari wannan yarinyar Nafisah ta shigo ta xubo maka, naga lafiyayyen girki aka yi a gidan, ae Hauwa dama Allah ya hore mata iya sarrafa hatsi” Yace “Sae Nafisa ce xata ban abinci?” Hajja tace “Aa nima sae in je in xubo maka, meye a ciki” yace “To ita warcan baxata iya xuba min ba” Hajja ta kalli Jiddah dake duke da

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button