JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 51

turaren wuta kusa da ita har sannan tace “To ke tashi ki xuba masa” Jiddah ta wani 6ata fuska, Hajja dae sae kallonta take, can ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido, Hajja ta rike ha6a a hankali tace “Sae naga kamar ta fara kiwiya ita ma, to ni dae fa kar ta sa inji kunya a kan abinda nake shirin yi, ko dai tana boye wasu halayyanta ne ban sani ba” Mikewa Abuturrab yyi ya fita daga dakin… Yana shiga kitchen

din ya kulle ta juya tana Kallonsa kamar dama tasan xae biyota, ya rungume hannunsa yace “Yanxu ma ki fita ta inda kika fita daxu” Ita dai bata ce komai ba ta ci gaba da dibar masa abincin a hankali, yace “Bude kofar ki fita nace” still taki kallonsa, tsawa yayi mata yace “Baki ji na ne” Ta kallesa kamar xata yi kuka tace “In fita in je ina?” Yace “Inda kika je daxu” Ganin ya nufota ta tafi ta bude kofar ta fita tana kallonsa

xuciyarta na bugawa, banda hasken wata babu wani haske a wajen, fitowa taga shi ma yayi bayan ya kashe fitilar kitchen din, bata san lkcn da ta tattare skirt dinta ba da xumar fallawa a guje yayi hanxarin cafkota da sauri, sannan ya kulle kofar kitchen din, iyakar tsorata ta tsorata a lkcn, ta marairaice masa tayi kasa da murya tace “Don girman Allah kayi hakuri ka sakeni… Wllh yanxu Umma xata fito mu wuce gida

kar ta fara nemana, tace min yanxu xa mu tafi” Yace “Toh ta nemeki din mana ina ruwana??” Kasa ce masa komai tayi amma scene din ranan a kitchen din gidansa ne ke dawo mata wanda hakan yayi mugun daga mata hankali, duk a tsorace take, ya daure fuska yace “Saboda nace ki daina gaisheni na lura har wani

nishadi kike duk sanda kika gani, kuma confidently kike wucewarki…” Tayi narai narai da ido tace “To amma ai kai kace in daina gaisheka, kuma abinda kace min ai shi nake yi” yace “Amma kuma ai murna kike don baki gaisheni?” Ta kasa ce masa komai gabanta na mugun faduwa, sai kuma ta fara kauda fuskarta saboda saukan breathing dinsa da take jiyowa don dab da ita yake, yace “Ohk ni kike dauke ma

fuska?” Ta fashe da kuka tace “Ni don girman Allah ka sakeni ana jirana, don Allah fa nace maka….” Tana ganin xai juyo da fuskarta saitin nasa ta rufe fuskar nata a jikinsa hankali tashe tace “Don Allah kayi hakuri bana so wllh” wrapping dinta yyi jikinsa yace “Xan sake ki amma sai kin bani amsar tambayar da xan maki yanxu” Banda bugawa babu abinda xuciyarta ke yi tana jiran jin tambayar tasa, ga kamshinsa me dadi da ya cika hancinta, duk taji ta kasa ci gaba da tsayuwa, xata xame kasa yace “Kee” a hankali tace “Na gaji don Allah ka bar ni in tsugunna” da bango ya hadata ta rufe idonta da sauri, sai kallon fuskarta yake a duhun, taji yace “Duk xaman da muka yi dake a gida daya ki lissafo min abubuwan da na maki na rashin

adalci…” A hankali ta bude ido tana kallonsa, yace “Ina sauraronki” Ta girgixa kai tace “Aa babu” ya dafa shoulders dinta yace “Karya kike” Tace “Ba karya nake ba, ban tuna abinda ka min na rashin adalci ba” Yace “To ina son ki tuna sai ki gaya min” Tayi shiru, shi dai kallonta kawai yake, murya can kasa tace “Amma me yasa kake ta6ani bayan kasan ni ba muharramarka bace, nasan kuma ka fini sanin hukuncin….” wani xaro ido tayi jin cold lips dinsa a wuyanta, da duk karfinta ta turasa shi kuma ya rungumeta gaba

daya, ai kam neck dinta ya sha kisses iri iri ba a cewa komai tun tana iya turasa har ta hakura ta kasa komai, switch din fitila da aka kunna a kitchen ya sa ya saketa da sauri, without looking at her ya bar wajen, xamewa tayi kasa ta hade kanta da gwiwa amma hawayen ma ta nemesa ta rasa sae sauke numfashi take… Tunda makullin motarsa na jikinsa gate kawai ya nufa ya fice ya shiga motarsa ya wuce

gida, ko kallon Aneesah dake xaune parlor duk ta cika turaren wuta bai yi ba ya haura sama yaki xuwa bangarensa ya bude wani daki ya shiga ya kulle kofar da key ya wuce bandaki direct…. Maimoon ta mike xaune ta kunna switch din dakin dake gefenta tana kallon Jiddah cikin muryan bacci tace “What happened Jiddah?” Ganin Jiddah taki bata amsa kuma taki dagowa ta sauka kan gadon ta nufi kofa ta fita xuwa dakin Umma….

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button