JIDDATUL KHAIRJIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

JIDDATUL KHAIR 57

ta kulle dakin ta koma nata dakin ta xauna gefen gado, ita fa duk ta rasa takamaiman tunanin da xata yi, ta rasa ma’anar abinda ta gani. Washegari da safe ganin har kusan takwas Jiddah bata fito ba Ramlah ta tafi dakinta, kwance ta ganta tana bacci, Ramlah ta karasa ta kai hannu kafarta, bude ido Jiddah tayi ta mike xaune da sauri, Ramlah tace “Baxa ki Islamiyya bane yau Jiddah? Karfe takwas fa yanxu” Jiddah dai

ta kasa barin ta hada ido da ita, a hankali tace “Um ciwon kai nake, sai gobe” Ramlah tace “Toh Allah ya kai mu” juyawa tayi ta nufi kofa Jiddah ta bi ta da kallo, komawa tayi a hankali ta kwanta ta lumshe ido.

Sanin Ahmad na hanya Ramlah tayi duk ayyukan gidan don taga alamar Jiddah ba fitowa xata yi ba, kwashe duk shopping din da Abuturrab yayi ma Jiddah tayi ta kai wani spare room ta ajiye don bata san wanda xata ce ya kawo ba idan Ahmad ya tambaya. Karfe goma saura Ahmad ya shigo gidan daga Abuja, bayan Ramlah tayi welcoming dinsa ta kawo masa breakfast suna xaune parlor yace “Jiddah ta je

weekend gidan Umma halan?” Ramlah tace “Aa tana daki yanxu ma haka” Yace “Islamiyyar fa?” Tace “She said she is having headache, bari in ce mata ka dawo” Daga haka ta mike ta wuce dakin Jiddah, kwance ta ganta kan gado duk da tayi wanka ta shirya, Ramlah sae kallonta take ganin kamar duk a tsorace take, Ramlah tace “Na xata bacci ma kike ai, baki karya ba fa, kuma Doctor ya dawo” Jiddah ta mike xaune taki yarda suyi eye contact da Ramlah tace “Xan fito yanxu” Ramlah ta juya ta fita, Jiddah ta

sauka kan gadon ta dau Hijab dinta, sai da gabanta ya fadi jin kamshin da yake, ta ajiye ta bude press ta dau wani sannan ta nufi kofa ta fita, xaunawa kasan carpet tayi ta gaishe da Ahmad ya amsa yace “Ya ciwon kan?” Ta d’an yi murmushi tace “Yayi sauki yanxu, na sha magani” Yace “Maa sha Allah, kun gama exams din?” Ta girgixa kai tace “Aa ranan Wednesday in sha Allah” Yace “Toh Allah ya taimaka” ta amsa da Ameen, sannan ta mike ta wuce kitchen, Ramlah dae sae bin ta da ido take, tea kawai Jiddah ta hada

ta koma daki. Karfe sha biyu saura Ramlah ta shigo dakin Jiddah, Jiddah na xaune saman darduma tana karatun qur’ani, Ta kai ayan karshe ta rufe Qur’anin ta d’an kalli Ramlah, ganin ta da mayafi tace “Fita xa ku yi?” Ramlah tace “Ehh yana kiranki, kayayyakin ki Kuma na daya dakin fa na ajiye maki a ciki” Jiddah tace “Aa ai ba nawa bane ni kadai” Mikewa tayi tunda dama da akwai Hijab a jikinta ta bi bayan Ramlah, Ahmad na xaune parlor rike da car key dinsa yana kallonta yace “Are you going out with us now Jiddah?

Xan kai Captain airport” Jin sunan da ya kira sai da gaban Jiddah ya fadi sosai without thinking twice tace “Aa karatu nake” Ramlah dai na tsaye bayan kujera tana kallonta, Ahmad yace “Tafiya xai yi fa, kuma xai dau watanni bai dawo ba, kawai airport xa mu kai sa muyi sallama da shi mu dawo” Shiru tayi jin abinda Ahmad yace, yana ci gaba da kallonta yace “Kije ki shirya mu tafi, ba komai ai, beside we are not staying long” Bata kuma masa musu ba ta juya a hankali ta koma daki, Ramlah ta bi ta da kallo, Ahmad yana

murmushi yace “Why are u looking at her that way Baby?” Ramlah ta d’an yi murmushi bata ce masa komai ba, Hijab kawai Jiddah ta canxa ta dau nikab dinta dake a goge ta saka hakan kadai ne xai iya sa ta bi su kai Abuturrab airport, jakarta ta dauka ta rataye a shoulder sannan ta fito parlor, Dariya Ahmad yyi ganinta yace “Tohh yau kuma nikab xa a sa kenan” Jiddah dai bata ce masa komai ba tayi murmushi daga cikin nikab din, a haka duk suka fita gidan, back seat ta shiga… hira Ahmad da Ramlah ke yi har suka iso

kofar gidan Abuturrab, Ahmad ya dau wayarsa ya shiga kiransa, ba a dau lkci ba ya daga, Ahmad yace “I am outside ka fito….” Abuturrab yace “Sai karfe biyu jirgin xai tashi xuwa lagos, I can’t sit all day at the airport, ka gane?” Ahmad yace “Ohk wai sai kun fara xuwa lagos dama?” Abuturrab yace “Yeaa, amma

ba mu xa mu yi piloting xuwa lagos din ba ai” Ahmad yace “But u should have told me that since” Abuturrab yace “Is there anything wrong idan kun shigo kun jira for just few hours?” Ahmad yace “Alright then” Daga haka ya katse wayar ya kalli Ramlah yace “Mu shiga ciki” Ramlah ta bude motar ta

sauka, tuni mood din jiddah ya canxa, amma bata jira ace ta sauka ba, kuma bata nuna hakan a fuskarta ba, ta bude motar ita ma ta sauka ta rufe, Kalle kallen layin ta fara yi, ganin karamin kiosk can farkon shigowa layin ta kalli Ahmad tace “Yaya xan d’an siyo abu a kantin can” Ya kalli inda ta nuna masa yace

“Me xa ki siya” Tace “Yanxu xan amso in dawo yaya” daga haka ta nufi kantin da sauri, su kuma suka shiga gidan, Aneesah tayi welcoming din Ramlah kamar xata hadiyeta don fara’a, tuni ta cikasu da lemo da kayan ciye ciye irinsu cake, cin cin, da alkaki da Chef Salma ke mata ta ajiye a gida sbda bak’i, Shi dai Abuturrab na xaune parlon yana danna wayarsa, bayan few minutes Ramlah ta kalli Ahmad tace “Bata shigo ba har yanxu fa Yaya” sae a sannan Abuturrab ya daga kansa, Ahmad ya mike ya nufi kofa,

Abuturrab na kallon Ramlah yace “Who?” Ramlah tace “Jiddah, tare muke, tace xata siya abu a kanti kuma har yanxu shiru” Bai kuma cewa komai ba, Aneesah ta wani ta6e baki ta koma kitchen tana kas kas da chewing gum a ranta kuwa cewa tayi gwara dai kam da bata shigo din ba don xata yi danasanin

shigowa, abinci ta fiddo a deep freezer don dumama masu, Bayan some minutes Ahmad ya dawo yace “Har gun mai kantin naje, ba abinda ta siya wajensa, kila tafiyarta tayi” Ramlah ta dinga kallonsa, sae kuma tace “Toh ba waya kuma balle a kirata” Shi dai Abuturrab danna wayarsa kawai yake amma duk yana jin su, Ahmad yace “Da akwai makulli wajenta ne?” Ramlah tace “Eh akwai spare key, tun ranan da

na bata da xan je gida” Ahmad yace “Ohk better” Aneesah ta fito daga kitchen tana washe baki tace “Na daura girki bari yayi sai in xubo maku Sis Ramlah” Ramlah tace “Ayya da ma baki yi bothering kanki ba Aunty, mun ci abinci daga gida kafin mu fito” Aneesah ta 6ata fuska tace “Aa wllh, ke da ko girkina baki ta6a ci ba, yau dai kam sae kin ci” Ramlah tayi murmushi tace “Toh shkkn Anty” Hira suke ta yi a parlon

banda Abuturrab dake danne dannen waya, bayan kusan minti ashirin da xuwansu Ahmad ya kalli Aneesah yace “Dauko min car key xanje laundry in amso kayana ynxu” Tana kallonsa da mamaki tace “Amma kace delivery xa ayi maka ai, and babu wani kayan da xaka bukata a ciki, ko ka manta ne” yace “Noo na tuna akwai wani rigan sanyi da xan dauka a ciki” Tace “Toh ka kira su kawo maka mana dole sai

kayi wahalan driving kuma” Mikewa yyi ya wuce sama, shi dai Ahmad idonsa na kan tv yana kallon wani program da ake yi, sai ga Abuturrab ya sakko da makullin motarsa, Ahmad yace “Mu je can din tare” Abuturrab ya kallesa yace “No, ba sai ka wani wahala ba kai da xaka kai ni airport, i will be back soon”

mikewa Ahmad yyi yace “Mu je can din, babu damuwa” Ta gefen ido Abuturrab ya kallesa, Aneesah tace “Haba doctor ga abinci can nace ya kusa nuna kuma kace xaka fita, don Allah ka tsaya ka ci, don Allah Dr” Abuturrab yace “Kaga dama kai ma baka ta6a cin abincin amarya ba, kawai ka tsaya ka ci… So u can rate her” Yana fadin haka ya amshe makullin motar Ahmad yace “Ba sai na tsaya warming mota ba, i will go with ur car, and i will be back in d next 20 mins” daga haka ya fice daga parlon, Aneesah kuwa sai

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button