JIDDATUL KHAIRJIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

JIDDATUL KHAIR 58

sleepless night din” Maimoon ta bude hannu tace “Ohoo a xuba ido a gani, shi sa Jiddah asirinta a rufe taki shiga nima da na sani wllh kawai ce ma Ummi xanyi to amma inyi wucewata, uwata ce ita da dole sai na gaisheta??” Safiyya tace “Ni dai ba ruwana ki daina wnn halin da kike….” Maimoon tayi gaba ta ki

sauraran Safiyya kuma, Jiddah dai tafiyarta kawai take bata ce masu komai ba, a ranta kuwa taji dadin dubaran da tayi na shigewa kitchen da yau har da ita xa a hada a xage ubanta dake kabari. Bayan kwana biyu Jiddah na xaune kan darduma ta idar da isha Maimoon ta shigo rike da wayarta dake kare kunnenta, ta nufeta ta mika mata wayar tace “Kema ku gaisa, Safiyya ma sun gaisa, har da Umma ma sun gaisa”

Jiddah na kallonta ta amshi wayar, screen din ta fara kalla ta ga “Yaya A” ta kai wayar kunne tayi shiru, Maimoon tace “Toh kiyi magana mana ai bai katse ba fa” daga daya bangaren taji yace “Shiru kika yi?” Lokaci daya ta dau muryarsa wanda hakan ya ja mata faduwar gaba, ta d’an hade rai a hnkli tace “Ina yini” Yace “How are you?” Tace “Lafiya” juyawa Maimoon tayi ta lallaba ta fita dakin….

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button