JIDDATUL KHAIR 60
Jiddah ce ta fara dauke idonta ta ci gaba da wankin da take a hankali, har ya wuceta sannan ta bi sa da kallo ta durkusa tana ci gaba da daurayan hijabs dinta, bayan minti goma ta gama ta shanya su sannan ta dauraye hannunta ta wuce cikin gidan, Xaune ta gansa a parlon yana danna wayarsa, su Maimoon na
daki Umma ma na bedroom dinta, Huraira kuma na kitchen tana girkin lunch, ta karasa cikin parlon tana kallonsa a hankali tace “Sannu da xuwa…” Kallonta shi ma yake yace “Kema sannu” Xata tafi dakin Umma taji yace “I will be back later” Ta juya tana kallonsa, mikewa yayi ya nufi kofa ita dai tana tsaye
har ya fita parlon. A hankali ta nufi dakin Umma ta yi sallama sannan ta bude, Umma na xaune tana waya, Jiddah ta xauna saman carpet ta jira har ta gama ta ajiye wayar, Umma na kallonta tace “Ya aka yi Jiddah?” Tace “Aa dama xan tambayeki sanda xa ayi awaran da kika ce ne” Umma tace “Au kinga ma na mance ni, duk sanda kika shirya ba matsala ki xo ki amshi kudin ingredients din, ke da Huraira ko
Maimoon ku tafi kasuwa” Jiddah tace “Toh Umma” Daga haka ta mike ta fita daga dakin. Abuturrab na
isa gidansa ya sauka daga d’an sahun da ya kawo sa, sai a sannan ya tuna ba shi da currency din kasar a tare da shi, ya nufi gun Mai gadinsa da ya taso yana welcoming dinsa da fara’a, yace “Ka basa dari biyar idan kana da shi” Mai gadin ya taho gun Mai adaidaitan da sauri xai basa kudin Abuturrab ya shiga cikin
gidan, the compound looks so neat saboda yayi employing masu shara da gyaran flowers da ba su ruwa, yana isa entrance din shiga parlon ya murda kofar gently ya shiga ciki, kida ne ke tashi an kure sa har kusan karshe a parlon, ya dinga bin parlon that looks very untidy and unkept da kallo, ga plates sun fi
kala biyar a kan carpet da duk ya baci da shinkafa da kwallin lemo, kayan kallon da suka yi uban k’ura ya dinga kallo, ya kalli dining area can ma duk plates da cups ne da breads ko kulle ledan ba ayi ba, calmly yake tafiya ya nufi stairs, shi ma duk yana jin yana taka k’ura kasan tiles din, bangarensa ya tafi ya bude
kofa, sun fi su bakwai xaune parlonsa nan din ma dai plates ne da kwalaye na ciye ciyen da aka yi, suna ta labari ga kida na tashi a parlon ma amma bai kai na parlor ba, Duk suka juya jin an bude kofa, Aneesah dake xaune kan carpet sanye da zani da ves a jikinta ta mike da mugun mamaki tana kallonsa tace “My Captain saukan yaushe babu notice? Mun fa yi waya jiya baka ce min kana tasowa ba” Bai sake kallonta
ba balle ta sa ran amsa ya bude kofar bedroom dinsa, Safara’u dake parlon ita ma da daurin kirjin ta mike da sauri tana cewa “In ji dai bai gan ni ba??” Bata jira an bata amsa ba ta fice da sauri daga parlon, Kawayen Aneesah duk biyar din su ma suka mike suka bi bayanta suka bar Aneesah tana xaxxare ido tana bin parlon da yayi kaca kaca da kallo, gashi takasa bin sa cikin bedroom din, Abuturrab ya fi minti
biyu tsaye yana bin bedroom din nasa da kallo, kaya ne ta ko ina a xube tun daga kan gado har kasan tiles da carpet, bayan kaya har da takalma, ga farin bedsheet din saman gadon har ya fara fita hayyacinsa duk ya yamutse, sababbin jakunkuna na kayan sa wa har uku ya gani jere a dakin su ma duk a wangale, tun da yake bai ta6a sanin bedroom na iya xama haka ba sai ranan, wannan ya wuce untidy ko
unkept, har wani tsami tsami mara dadi yaji bedroom din ke yi, ga kofar bandaki a hangame, ya lumshe ido ya juya ya bude kofar ya fita, har sannan Aneesah na tsaye sai wuwwurga idanuwa take, bai kalli direction dinta ba ya fice, wani dakin daban ya tafi ya bude ya ga Safara’u xaune saman gado wanda shi ma din duk a yamutse yake, har lkcn daurin kirji tayi, ganin sun hada ido ya gaisheta, bai jira amsa dogon
gaisuwan da take jere masa ba bayan ta jawo zanin gado ta yafa, yace “Alhmdlh mun gode Allah” Daga haka ya fice ya kulle mata kofa, wani dakin ya bude ya ga kawayen Aneesah sun yi dai dai a dakin ya kullo kofar ba tare da ya amsa gaisuwansu ba, bai sake bude wani dakin ba ya sauka downstairs ya fice daga gidan gaba daya, Abuturrab ya fi minti goma tsaye a kofar gida gashi babu cash a jikinsa babu Atm
card, luggages dinsa kuma bai dauko daga airport ba, wayarsa ya ciro daga karshe ya shiga kiran layin Maimoon, tana dagawa bayan sun gaisa yace “Give the phone to ur frnd” Maimoon ta mika ma Jiddah dake gefenta waya, Jiddah ta amsa tana duba me kiran kafin ta kai kunne, Maimoon ta fita daga dakin, Jiddah tace “Ina ji” Yace “Did u tell them i am back?” Ta girgixa kai tace “Aa” Yace “Ohk, kina da cash
wajen ki?” Ta d’an yi shiru, sai kuma tace “Aa sai a account, wanda Ya Ahmad ke sa min saboda makaranta” Calmly yace “Ohk ki bar wayar a wajenki…” Bai jira tace komai ba ya katse wayar ya karasa bakin titi, ya samu adaidaita ya koma gidan Umma, bai bari ya shiga can cikin layin ba ya sake kiran
Number Maimoon, Jiddah ta daga, yace “Ki kawo min Atm card dinki waje yanxu” A hankali tace “Toh” ya katse wayar, ta mike ta dau jakarta ta cire atm card din ta mayar ta ajiye sannan ta dau gogaggen
Hijab dinta ta saka ta bude kofa a hankali ta leka parlor bata ga kowa a parlon ba hakan ya sa ta fito da sauri ta nufi kofar fita, har ta isa gate tana waigen entrance din gidan, tana fitowa kofar gida ta dinga kalle kallen inda xata gansa, daga nesan ya hangota ya sauka daga kan adaidaitan, hakan ya sa ta gansa,
ta karasa inda yake tana tafiya a hankali, idonsa na kanta har ta iso, ya sauke idonsa ya amshi Atm card din yace “Pin?” Ta gaya masa, yace “Thank you” daga haka ya shiga adaidaitan yace su tafi, ita kuma ta juya ta koma cikin gida. Abuturrab na cire kudin ya tafi yyi lodge a hotel, yana shiga dakin da aka bass ya kashe wayarsa, bayan ya huta yayi ordering abinci, Ana la’asar kuma ya fita xuwa airport don daukan
luggages dinsa ya dawo hotel din a taxi, ya shiga da kayan ciki, bai sake fitowa hotel din ba sai da aka kira magrib ya fito yin sallah, bayan sun idar ya siya fruits ya koma cikin hotel din…. Washegari Asabar karfe tara ya kunna wayarsa ya shiga kiran Ramlah, tana dagawa da fara’arta tace “Yaya ka dawo ne?” Yace
“Ahmad na gari?” Tace “Aa bai shigo ba satin nan, yace sai next week” yace “Ohk xan xo in amshi makullin motarsa yanxu” tace “Toh yaya sae ka xo” katse wayar yayi da yake ya shirya ya dau cash din da ya ciro jiya ya sa a aljihunsa sannan ya fita ya kulle dakin, a adaidaita ya isa gidan Ramlah, bayan ya
sallamesa ya shiga ciki yana amsa gaisuwan mai gadi, ya wuce parking space, yana tsaye a nan ya shiga kiran Ramlah, bayan ta daga yace “Ki fito min da makullin parking space” tace “Yaya baxa ka shigo ba?”
Yace “Ehh” tace “To bari in fito” ba a dau lkci ba ta fito rike da makullin motar, tana murmushi ta nufi parking space din ta risina ta basa tace “Ya hanya yaya?” Yace “Alhmdlh, ba sae kin ce masa na dawo ba” tace “Toh Yaya” bude motar yyi ya shiga yyi warming dinsa ita dai tana tsaye tana kallon sa, har daga karshe ta daga masa hannu ya fita da motar ita kuma ta koma cikin gida… Abuturrab ne xaune kansa a
kasa yana sauraron uncle dinsa, Alhaji Lawal dake ta kallonsa da kyau yace “To ko dai kana shan wani abu ne wanda mu bamu sani ba Aliyu?” Shi dai bai ce komai ba, Alhaji Lawal yace “Dago ka kalleni ina maka magana” Ba musu Abuturrab ya dago kansa yana kallon Uncle din nasa, Alhaji Lawal yace “Tell me what exactly is wrong with u? Do we deserve being taking for granted Aliyu?” Abuturrab ya girgixa kai