JIDDATUL KHAIR 60
yace “Aa Abba ku yi hakuri, kuskure ne…” Alhaji Lawal ya dakatar da shi yace “You called this mistake also Aliyu?? Baka tsoron Allah ne da xaka kara kiran wannan ma da mistake??” Sake baki Alhaji Lawal yayi yana kallonsa, Abuturrab bai iya yace komai ba, Alhaji Lawal na jinjina kai yace “Lallai baka da
hankali baka da manners, ka kuma mugun raina mutane ka daukemu for granted, ashe dama kai ka haifa kanka bamu sani ba?” Abuturrab yyi kasa da murya with remorse yace “Don Allah ku yi hakuri Abba, i know i wronged u all, but this the only way out for me, Abba baxai saurareni ba, so is Ummi… No one will give me a listening ear” Alhaji Lawal yace “Ohk ni kuma sbda ka yi shegen raina ni yanxu kake
tunanin xan baka listening ear?? No… I am not giving u dat, and i am sorry babu wani abu da xan iya yi” Abuturrab ya kasa ce masa komai, Alhaji Lawal yace “I can’t do anything about this… ina ce ita wannan yarinya idan ban mance ba babu irin hakuri da ban bakin da bamu baka ba a kan ka xauna da ita, ashe ka maida mu shashashai ne a lkcn ka je ka saketa kuna ta xama tare duk don sbda kana ganin ita ba class dinka bace or whatever, bugu da kari kuma u bluntly admitted baka sonta, to yanxun da ka koma ka
aikata shirmen da ka aikata son nata ka fara yi kenan???” Nan ma dai Abuturrab bai ce komai ba, Alhaji Lawal ya daka masa tsawa yace “Bude baki ka bani amsa my frnd.. i am talking to u” A hankali yace “Ina son xama da ita yanxu Abba” Alhaji Lawal yace “U are very stupid, ae ba tambayar da nayi maka ba
kenan..” Kasa basa amsa Abuturrab yayi nan ma, Ganin yanda Uncle din nasa ke kallonsa ya sunkuyar da kai, Alhaji Lawal yace “Toh ka saka a ranka cewar kamar yanda muka xaunar da kai kwanaki muka baka takarda da biro ka datse auren naku wannan karon ma hakan ne xai faru, mu ba ‘yan banxa bane da xaka
dinga controlling dinmu yanda ka so, kana aikata duk abinda ya xo kanka without our consent, we birth u…” Abuturrab ya marairaice masa yace “Abba don girman Allah ku yi hakuri, wllh ban koma na aureta da nufin in cuceta bane wannan karan, wancan lokacin ma kuskure aka samu, don Allah Abba kayi hakuri,
i mean no harm to her…” Alhaji Lawal yace “Da nufin me ka koma ka aureta yanxu? Bani amsar tambayar nan” Abuturrab yace “Ina son xama da ita ne na har abada” Alhaji Lawal ya girgixa kai yace “Kamar dai yanda na fada you are very stupid, kawai ka koma ka aurota saboda kana son ku xauna tare
har abada, wait!! are u mad??” Abuturrab yace “Abba ni dama fa ban ta6a buda baki nace bana sonta ba, kawai sharrin shaidan ne da kuma yanda kowa baya son auren shi yasa na aikata abinda na aikata, amma
wllh ban ta6a cewa bana sonta ba” on a serious note Alhaji Lawal yace “Daga Hajja a rashin alkibla sai kai, anyway… I am so dedicated today, don haka idan Allah ya amince mana gobe xan shiga kadunan, xaka iya tafiyar ka sae na xo goben…” A hankali Abuturrab yace “Xan jira mu tafi tare goben in sha Allah” Alhaji Lawal yace “Allah ya kai mu” Godiya Abuturrab yayi ma uncle din nasa sanan ya mike ya nufi kofa
hoping this will be the only challenge he is to face till end, Alhaji Lawal ya bi sa da kallo har ya fita yana mamakin karfin hali da taurin xuciya irin na Abuturrab, kiri kiri yayi ta abu ba tsoro. Abuturrab ya fi minti daya tsaye kofar parlon Abbansa ya kasa bude kofan, bai ta6a jin mugun shakkan Abbansa irin na lkcn ba, bai san me ya sa wnn karan ko Aunty baya jin ta kamar yanda yake jin Abbansa, ga bugun xuciyarsa da ya
tsananta, it’s been long da ya shiga yanayin nan da yake ciki yanxu, muryan Umma yaji a bayansa ta rike ha6a tace “Kai kuma yaushe a gari??” Ya juya da sauri, yyi feigning smile yace “Good evening Umma” tace “Saukan yaushe?” Ya d’an fara kame kame kafin yace “Jiya” tace “Ikon Allah, to sannu da
dawowa…” Bude kofar parlon tayi, lkci daya fara’ar da ke fuskarta ya bace, ta wani sha kunu ta shiga parlon, tunda aka kirata aka ce ta xo gidan tayi tunanin xancen baxai wuce na auren da suke shirin laka6a ma Jiddah ba, kuma ta sha alwashin yau kam sae inda strength dinta ya kare, dai dai take da kowa,
ganin Hajja xaune parlon ta wani kara daure fuska ta nemi waje ta xauna, Abuturrab ya shiga parlon kansa a kasa gabansa na mugun faduwa, xaunawa yyi saman carpet ya kasa kallon kowa, a hankali ya fara gaida Hajja kafin sauran occupant din parlon, Hajja dae fuskar nan nata babu ya6o bbu fallasa,
Umma ma babu yabo babu fallasan tace “Ina yini Hajja” Hajja ta rike kanta tace “huhuhu wllh tun da naje Masar na samu saukin gaishe gaishen jaraban nan, yo kowa na ta kansa ina batun wani gaisuwa, su basa haka a can wllh, duk wayayyu ne, a kasar nan kowa sae yace sae ya gaisheka alhalin wani gaisuwar
ma bai kai ciki ba, to ni dai na yafe, ko Usman ma ban amsa gaisuwarsa ba balle wani….” Ko kallonta Umma bata sake yi ba tana jan counter dinta… Alhaji Umar ne ya bude wajen da addu’a, sannan bbu 6ata lkci kuma babu boye boye in Brief Alhaji Lawal ya maimaita masu duk abinda Abuturrab ya sanar masa jiya a Zaria, Babu wanda bai girgixa ba a parlon, Abba dai kallon ceiling kawai yake, gaba daya
sauran mutanan parlon kallon Abuturrab suke irin kallon tsoro, babu ko kiftawa, shi ko kansa na sunkuye xuciyarsa na bugawa, Hajja dae sae wani murmushi take me sauti irin na bosawa tana girgixa kafa da kai, Bayan shirun kusan minti biyu da ya ziyarci parlon, Aunty ta mike duk ta hada xufa daga sama har kasa tana girgixa kai tayi wani murmushin takaici tana nuna Abuturrab tace “Wllh karya kake Aliyu, karya kake
baka isa ka kunyata ni ka toxarta ni, ka walakanta ni a idon duniya ba wllh… Karyanka ta sha karya wllh” kofa ta nufa ta fice daga parlon da sauri, Umma da Ummi har sannan hangame baki suka yi suna kallon Abuturrab, Hajja na kallon Abba a hankali tace “Yau da ace a Masar ne idan ba a garkame d’an ka a
kurkuku ba shegiya nake Usman, ae wannan shine ta’addanci mafi muni da mutum xai yi a hukuntasa a kasar Masar, kai ba a ma ta6a haka a can ba wllh, Aliyu dai ya fita sahun mutanen kwarai, Aliyu mutumin banxa ne… Kiri kiri ya nuna ma d’an uwansa na jini bakin ciki, da hassada, ba fa son yarinyar yake ba
kawai bakin ciki ya mayar da shi gun danginta ya sake aurota a gantale, su ma dai dangin nata matsiyata ne, kawai sun mayar da ‘ya kaza don yaje yyi masu fafan yana tukin jirgin sama, to meye kuma tukin jirgin sama Allah na tuba abinda matsayinsa da d’an acaba da d’an taxi daya a idon duniya, wato sbda hassada sai ya ga ta yanda yarima zai aureta ko??” Cije yatsa Hajja tayi sae kuma ta rushe da kuka tace
“Wllh mun fi awa biyu da mutumin nan muna garari a hayin rigasa, katon ya gilla min karya wai an rushe gidansu Jiddah daga karshe ma gaya maka ne kawai ban yi ba Usman wllh a tsakiyar titi ya yasar dani yyi wucewarsa kamar mara galihu duk na hada xufa, har ya kai ya kawo mutane suka xata almajira ce idan
an xo wucewa sae a mika min ashirin, goma….” Sosai Hajja take kuka tace “Ni a tarihin duniya ma ban ta6a jin an haifi me hali irin na Aliyu ba, kuma a bisa dokan Masar duk wanda xai iya aikata abinda ya aikata to xae iya kashe rai babu ko darrr, shi yasa ma ake garkamesa a gidan gyaran hali, ni dae xan xuba ido kawai in ga hukuncin da xaka dauka a kan wannan d’a naka Usman, dalilin abun nan da Aliyu ya