JIDDATUL KHAIR 9
💖💖 Jiddatul Khair 💖💖
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
9…..
Abuturrab yayi parking yana bin wajen da kallo ya dau wayarsa yayi dialing number da suka kirasa da shi, yana fara ring mai adaidaitan dake hira da wani me d’an kiosk a wajen ya daga, Abuturrab yace “Ka duba wani bakar mota a wajen da kace” Mai adaidaitan ya mike yana dube duben wajen, can ya hango motar Abuturrab ya kalli Jiddah dake xaune cikin adaidaitan har sannan ta takure waje daya yace “Ga sa can ya iso” Dago kai tayi da sauri sannan ta sauka daga cikin adaidaitan, tare suka tsallaka titi da shi xuwa daya side din ya nufi motar Abuturrab tana biye da shi a baya, Abuturrab ya bude motar ya sauko yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi sbda hawayen da ya kawo idonta, ya kalli mai adaidaitan ya ciro dubu biyu aljihunsa ya mika masa yace “Nagode” Mai adaidaitan ya amsa shi ma yyi masa godiya sannan ya tsallaka ya koma gun Napep dinsa, Ba tare da Abuturrab ya kalleta ba yace “Shiga” Ba musu ta shiga gaban motar, ya shiga maxaunin driver ya tada motar suka bar wajen, a hankali yake driving din yace “Bayan na tafi sai me ya faru?” A hankali ta fara basa labarin abinda ya faru bayan tafiyarsa babu abinda ta boye masa har karshe, ganin yanda take kuka ya kalleta yace “Ya maki wani abu ne?” Ta girgixa masa kai, rasa particular tunanin da xai yi yayi a lkcn, babban damuwarsa yanxu inda xai kai ta cikin daren nan, ya d’an kalleta yace “Yanxu babu wanda kika sani nan cikin gari?” Ta girgixa masa kai tace “Ba kowa” ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yana ci gaba da driving dinsa almost absentminded, parking yayi bakin gate din gidan, har Mai gadin ya mike xai bude gate ganin yayi parking a nan waje sai ya koma ya xauna, Abuturrab ya sauke glass ganin haka mai gadin ya sake tasowa da sauri ya nufosa yana murmushi cike da girmamawa yace “Barka dai ranka shi dade…” Abuturrab yace “Ya aikin?” Mai gadi yace “Alhmdlh, Baxa ka shiga ciki ba?” Abuturrab ya d’an shafa kai yace “A’a, wani d’an alfarma nake nema gun ka” Cike da natsuwa yace “Toh ina saurarenka yallabai” Abuturrab yace “Erm… Mai dakinka na nan ai?” Mai gadin yace “Ehh tana ciki wllh” Abuturrab ya kalli Jiddah yace “So nake don Allah ta d’an kwana nan wajen ku kafin gobe, amma kamar kuma hakan da takura tunda daki daya ne ko?” Da sauri Mai gadin yace “Inaa babu wani takura wllh ranka shi dade, ni ai ba baccin ma nake da daddare ba yawanci nan tsakar gida nake kwanciyata wllh, kar kaji komai” Abuturrab yace “Toh nagode, amma kada kace ma masu gidan na xo” Mai gadin yayi murmushi yace “Baxa ayi hakan ba ranka shi dade” Abuturrab ya juya yana kallon jiddah yace “Sauka, sai da safe…” Yana fadin haka ya bude mata motar, ta sauka a hankali, Mai gadin yace “Mu je ciki to….” tafiya ya fara yi ta bi bayansa sai da suka kusa gate din ta waiga ta kalli Abuturrab da ya bi su da kallo, dauke kai tayi ta bi mai gadin suka shiga cikin compound din, yayi wani sigh ya tada motarsa yayi reverse ya bar layin wani ajiyar xuciyar ya sake saukewa feeling a bit relieved. Har aka idar da sallan asuba Jiddah bacci take, matar mai gadin na idar da sallah ta d’an ta6ata tace “Ki tashi kiyi sallah lokaci yayi” a hankali Jiddah ta bude idonta ta mike xaune da sauri, daki ne babba gun katifar kadai ne suka yi demarcating da labule, yaronsu daya wanda ko yayesa ma ba ayi ba, jiddah ta mike matar ta nuna mata bandakinsu dake cikin dakin, tana fitowa matar ta bata hijab, bayan ta idar abun ka da bata saba komawa bacci ba ta kalli matar ta gaisheta sannan tace “Babu wani aikin da xa ayi?” Matar tayi murmushi tace “Aa babu, ki koma kiyi kwanciyar ki” Jiddah bata ce mata komai, amma duk yanda ta so komawa bacci bata iya ta koma ba don ta riga da ta saba da wahala, gari na wayewa ganin matar ta dau tsintsiya xata fara sharan daga nan inda suke xuwa bakin gate don gidan akwai me shara, jiddah ta amshi tsintsiyar, matar tace “Don Allah ki bari ki koma kiyi xamanki….” Murmushi kawai Jiddah tayi tace “Aa xan taya ki” Tana fadin haka ta fara sharan hakan yasa matar ta koma ciki don yi ma yaronta wanka tana yaba hankalin Jiddah, shi kuma mai gadin na can xaune waje, jiddah na cikin shara aka bude gate din gidan ta dago da sauri, sosai gabanta ya fadi ganin wanda ya shigo, a hankali ta juya tana ci gaba da sharanta, waya ne kare kunnensa ya katse wayar yace “Maman Abdallah kun tashi lafiya” Ba tare da ta bari ta kallesa ba a hankali tace “Ba ita bace” Ko rufe baki bata yi ba Maman Abdallah ta leko da fara’arta, cike da ladabi tace “Ba ita bace Dakta, bakuwa nayi, ina kwana” yana tafiya yace “Lafiya lau, Abdallah bai tashi ba?” Tace “Kaya nake sa masa ya tashi tun daxu” yace “To a gaida min shi” Tace “Xai ji Dakta” Entrance din gidan nasu ya nufa, Jiddah ta bi sa da kallo tana sharanta a hankali… Karfe takwas Maman Abdallah ta kalli Jidda bayan ta gama shiryawa cikin kayan da ta bata tace “Tunda kinyi wanka mu shiga daga ciki mu gaisa da ‘yan gidan in amso mana kumallon mu, ko” Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, Maman Abdallah ta goya d’anta tace “Tashi mu je, Hajiyar gidan ta tashi yanxu” A hankali Jiddah ta mike ta dau Hijabin matar ta sa sannan suka fita, Maman Abdallah ta bude kofar hade da sallama ta shiga ciki Jiddah na biye da ita, Xaunawa tayi kasa jiddah ma ta xauna kasa, Hajiya Ramlah dake parlon da murmushi fuskarta tace “Bakuwa kika yi Shafa” Maman Abdallah ta washe baki tace “Ehh wllh Hajiya, bakuwa nayi da yammacin jiya” Cike da ladabi ta risina tace “Ina kwana Hajiya” Umma tace “Lafiya lau kun tashi lafiya?” Maman Abdallah tace “Alhmdlh, su Maimuna da Siyama na ciki kenan” Umma tace “Suna ciki…” Jiddah na kallonta a hankali tace “Ina kwana?” Umma tace “Lafiya lau yan mata, sannu da xuwa…. ya sunanki?” Jiddah ta sunkuyar da kanta tace “Jiddah” jin footstep ta dago tana kallon direction din, Ahmad ne ke sakkowa daga sama yana kallonta babu ko kiftawa, Umma tace “Ahh me babban suna ce ashe” Jiddah tayi murmushin karfin hali ta sunkuyar da kanta, Umma tace “Maa sha Allah, sunan yayata gare ki, sannu da xuwa” Maman Abdallah dai sai washe baki take, Umma tace “Yar uwarki ce amma” Maman Abdallah ta sosa kai tace “Ehh kauyenmu daya” Ahmad dai sai kallon Jiddah yake, ita kuma taki yarda ta sake kallonsa, Maman Abdallah ta mike ta wuce kitchen don daukan kumallonsu, tana shiga ta dauka a inda mai aiki ta ajiye masu ta fito, Umma ta kira mai aikin tace “Tunda suna da bakuwa ki kara masu” Mai aikin ta amsa ta koma kitchen din, ba a dau lkci ba ta dawo ta mika ma maman Abdallah coolern, Cike da ladabi Maman Abdallah tace “Mun gode hajiya Allah ya kara girma” Umma tace “Ameen” Mikewa Jiddah tayi ta amshi warmer din a hannunta sbda Abdallah dake bayanta ita ma ta yi ma Umma godiya sannan suka fita, Ahmad dai ya bi ta da kallo…. He looks so confused, sak tayi masa kama da mai awaran hayi, wata xuciyar tace kawai kamanni ne me xai kawota cikin gari har cikin gidansu kuma, daga kafada yayi a ransa ya bar sa a cewar kamannin ne, ya nufi dining don yin breakfast. Karfe goma Abuturrab ya fito gida, driving yake yi with different thought in mind, wayarsa ne ya fara ring ya kalli wayar ganin Ahmad ke kiransa ya daga, Bayan sun gaisa Ahmad yace “Muna chatting kuma ka sauka” Abuturrab yace “Ehh i am driving now” Ahmad yace “To where?” Abuturrab yace “Aunty ta aikeni” Ahmad ya d’an ta6e baki yace “Ohk, wai ka dauki hutu ne naga baka koma gun aiki yau ba?” Abuturrab yace “Kai me ya dawo da kai during week day?” Ahmad yace “Wani taro xa mu yi nan kaduna, amma gobe xan koma ai, in sha Allah” Abuturrab yace “Ohk anjima xan shigo idan na dawo” Ahmad yace “Alright” daga haka ya katse wayar ya ajiye, parking yyi inda ya saba parking din, ya sauka motar yana kallon layin dake cike da mutane, wani d’an saurayi dake fitowa daga layin ya kalla yace “Abokina me ke faruwa a nan?” Saurayin yace “Wata amarya ce saura sati bikinta aka nemeta aka rasa, wasu sunce angon ne ya dauketa, wasu kuma su ce uwar rikonta ta san inda take, ynxu dai ga shi angon na neman cinna ma gidan wuta wai sai an fito masa da matarsa, uwar rikon na can tana kuka da rantse rantse bata san inda take ba, jama’a kuma na ta dannan shi angon, da yake babu wanda bai san halinsa ba a unguwar nan, sai ya iya kona gidan, yanxu dai wajen yan sanda ko mai anguwa suke shirin xuwa” Abuturrab yace “Toh Allah ya kiyaye” Barin anguwar Abuturrab yayi, yana isa gidansu Ahmad yayi parking a waje, ya sauka motar gaisawa yayi da mai gadi dake xaune a waje sannan ya xauna kusa da shi murya can kasa yace “Kayi hakuri babu wani bayani na kawo maku yarinya…” Mai gadin ya katse sa da sauri yace “Babu komai ranka shi dade, kar ki ji komai wllh, xata iya xamanta har iya sanda xaman nata xai kare a nan, ni bani da matsala haka ma mai dakina..” Abuturrab ya sa hannu aljihu ya fiddo dubu biyar ya mika masa yace “Gashi ka rike wannan” Mai gadin ya girgixa kai yace “Aa kar mu yi haka da kai don Allah” Abuturrab ya ajiye masa kudin ya mike ya shiga gate din gidan, Babu kowa tsakar gidan ya kalli building din mai gadin sannan ya nufi main entrance din gidan. Kiran azahar ne ya sa shi fitowa tare da Ahmad xa su tafi masallaci, Jiddah na xaune compound din kan karamin kujera kusa da dakin mai gadin da ruwa cikin buta a gabanta tayi nisa tunanin da take, Har suka kusa isowa wajen Abuturrab kallonta yake haka ma Ahmad, kamar ance ta daga kai tayi ido hudu da su, sosai gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta da sauri ta fara alwala da ruwan butan gabanta har suka fita compound din, sai a sannan Ahmad ya kalli Abuturrab yace “Don Allah wa yarinyar nan tayi maka kama da???” Abuturrab yace “Wacce yarinya?” Ahmad yace “Yarinyar da ke xaune a compound” Da mamaki Abuturrab yace “Ohh dama akwai yarinya xaune a compound din?” Wani kallo Ahmad ya jefa masa, Abuturrab ya daga shoulders dinsa yace “Banyi noticing ba” Ahmad yace Karya kake “Wllh” Abuturrab bai kuma ce masa komai ba, Ahmad yace “Joke apart captain, bata yi maka kama da wannan yarinyar da muke siyan awara a wajenta a hayi ba” Abuturrab ya ta6e baki yace “Kai da kake kallonta kenan idan kaje siyan awaran, ni kam banda murhu babu abinda nake gani a wajen” yana fadin haka ya shige Masallaci kafin Ahmad ya sake ce masa komai, Ahmad ya bi bayansa kawai. Ko da suka fito masallacin Ahmad ya tsaya gaisawa da abokansa na layin, Abuturrab ya shiga compound din kawai, Jiddah na ta sauri tana kwashe kayan shanyan da Maman Abdallah ta shanya don garin akwai hadari, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai sai da ya iso dai dai inda take tace “Ina yini?” Bai amsa ba yace “Kina da wani matsala?” Ta girgixa masa kai, ganin haka ya ci gaba da tafiyarsa, dai dai nan Ahmad ya shigo compound din bata yadda ta kallesa ba har xai wuceta sai ya tsaya yace “Bakuwa muka yi yau a gidan ashe?” Taki yarda ta kallesa still, tayi kasa da murya tace “Ina yini” yayi murmushi yace “Lafiya lau, sannu da xuwa” Maman Abdallah ta leko tace “Dakta Abdallah fa boyewa yake idan yaji muryar ka” Ahmad yayi murmushi yace “Ae kice masa alluran ya kare” Ta kwashe da dariya tace “Lallai kam, shi dai ya tsorata da kai kawai Dakta” Ahmad yace “Ashe bakuwa muka yi gidan” Tace “Ehh wllh yar uwata ce daga kauyenmu ta xo jiya da yamma” Yace “Allah sarki, toh barkan ta da xuwa” Maman Abdallah tace “Ae ko dai Dakta, mun gode” Murmushi yayi ya ci gaba da tafiya a xuciyarsa ya kara gaskata cewa lallai kamanni ne kawai suka yi da me Awara a hayi, but the resemblance is so obvious even the dimples and large eyes, can balcony Abuturrab ya tsaya duk yana jin abinda suke fada, sai da ya iso Abuturrab yace “Kai dai baka abu da class Ahmad, meye na tsayawa hira da matar mai gadi pls?” Bai jira me xai ce ba yayi wucewarsa ciki, Ahmad ya girgixa kai kawai ya bi bayansa. Da yamma Mamam Abdallah ta ba jiddah kwanukansu ta kai can cikin gida sbda a ciki xa a sa masu abincin dare, Jiddah tace “Ta cikin parlon ake bi xuwa wajen girkin?” Maman Abdallah tace “Ehh inda muka je daxu ba, ynxu ma babu kowa gidan yaran duk sun tafi islamiyya, Hajiya nasan tana bangarenta yanxu haka, ai kinga dakin girkin da mai girki ta fito ta miko mana kumallo daxu da safe, nan xaki shiga, dakin ma ya kusa biyun wannan da muke ciki ae wllh” Jiddah ta mike ta dau babban samiran ta fita ta bar Maman Abdallah na linkin kaya, Babu kowa babban parlon kamar yanda Maman Abdallah tace, ko ina tsaf sae kamshin turaren wuta da ya kama parlon, Kasa karasawa can cikin parlon Jiddah tayi, tun da ta xo duniya bata ta6a ganin irin wannan parlon ba da ma komai na cikinsa, duk sai tsoro ya kamata, hanyar da taga Maman Abdallah ta bi daxu da safe ta bi ta d’an leka kofar da ta gani a bude ganin wasu mata biyu kuma har sun hada ido ta risina a hankali tace “Sannun ku da aiki” Duk suka amsa mata dayar tace “Shigo ki ajiye kwanon” Jiddah ta karasa kitchen din, ta kara masu sannu da aiki sannan ta ajiye kwanon, kanta a kasa tace “Me xa a kama maku?” Dayar matar tace “Aa babu komai ‘yan mata, mun gode” Doguwar tace “Sae dai kawai wanke wanken dake cikin bahon wanke wanke, ba shi da yawa” Jiddah ta juya tana kallon sink da matar ke nuna mata, karasawa tayi wajen ta tsaya tana tunanin ta ya xata yi wanke wanke a takurarren waje haka sannan ta ina xa ta dinga xubar da ruwan wanke wanken, a hankali ta juya tana kallonsu tace “Ruwa da omo fa” Matar tace “Ga pampo a gabanki ki kunna, wannan roban kuma sabulun wanke wanke ne a ciki xaki matso ya fito”