JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 9

Bayan magrib Abuturrab yyi parking inda ya sa6a parking ya sauka motarsa ya kulle da kafa ya karasa kofar gidansu Jiddah. Yaro ya aika ciki yayi masa sallama da mutanen cikin gidan, Hansai ce xaune tsakar gida da kawayenta biyu, Hansai ta sharbe majina tana matse hawayen kumburarren idonta tace “Wllh xai aika, waye bai san cewar shaye shaye Iliya yake ba, ni dai baxan kwana gidan nan ba yau gaskiya gwara in tafi wani wajen in kwana” Zulai tace “Aa nima dama ban bada shawaran ki kwana ba tunda ya furta sai ya kona gidan da kyar baxai aika ba” Ladi tace “Toh yanxu ina yarinyar nan ku ke tunanin xata tafi haka, wa gareta a duniyar ma gaba daya?” Hansai tace “Ai wannan magana ma bai taso ba, dolenta ta dawo duk inda ta tafi ta xo ta rabani da wannan mahaukacin mutumi, idan ya kona min gida gidan ubanwa xan koma kowa na ta kansa a rayuwar nan, dama gidan iyah nake ta tunanin ta shige amma duk dubawan da yan sanda suka yi a gidan babu ita babu alamarta” Kallon yaron da ya shigo suka yi gaba daya, yaron yace “Wai ana sallama a waje” Abuturrab ya daga kai bayan Hansai ta fito cikin gidan, ganinsa ta makale kofar xaure ta kasa karasowa, Ya karasa shi, yana dubanta yace “Ina yini?” Da kyar cikin rawar murya tace “Lafiya lau Alhaji, sannu da xuwa” kafin yace mata komai ta fashe da kuka tace “Muna cikin tashin hankali da alhini Alhaji” yana kallonta yace “Me ya faru?” Tana matsar kwalla tace “Tun jiya ake neman yarinyata har xuwa yanxu babu labarinta, ban san inda xan sa kaina ba xuciyata kamar ta fashe” Yayi shiru yana kallonta, ta sharbe majina tace “Shi kansa wanda ke da niyyar auren nata nan ya xo daxu da yamma ba irin tijaran da bai min ba har da ikirarin xai kona mana d’an gidan nan idan ba a fito masa da matarsa ba, wllh wllh bamu da masaniyar inda take, babban tashin hankalina ban san halin da take ciki ba yanxu” Yace “Yanxu ya ake ciki da shi wanda xai aureta din, baki basa kudin nasa bane?” Tace “Wllh yace baxai amsa ba, yanxu haka ma da kudin na tafi gun yan sanda na kai rahotu kasan sai an basu wani abu me d’an tsoka kafin su kula ka, sannan gidan radio da gidan talabijin duk na bi na rarraba masu kudin don su yi ta sanarwa har Allah ya bayyanata, yanxu maganar da nake maka ko dubu talatin ina jin kudin bai kai ba a ajiye a daki, ‘ya ta bata fiye min komai ba a duniya?” Kallonta kawai Abuturrab yake bai ce komai ba, ta sake sharbe majina cikin rawar murya tace “In dai da wani taimakon da xaka mana yarinyar nan ta bayyana da wuri ka taimaka domin girman Allah Alhaji” Abuturrab yace “Ina shi madaurin auren nata?” Tace “Kawuna ne, tare da shi ma muke ta sintirin gidan radio da police station tun safe” Abuturrab yace “Ina son ki hadani da shi” Sosai gabanta ya fadi, yace “Yana da waya?” Da sauri tace “Aa bashi da shi, sai dai gobe in je in sanar masa, idan ka xo sai Bibalo ta kai ka” Abuturrab yace “Toh shkkn, nagode, sai goben” Daga haka ya juya ya bar wajen, ta bi sa da kallo gabanta na faduwa, da sauri ta koma ciki, Zulai tace “Waye hala?” Hansai ta share wani xufa da ya keto mata tace “Aa yan xuwa jaje ne, yanxu dai gidan Kawu Jibril xan tafi tare da Bibalo idan ya so sai mu kwana can kawai kada Iliya ya far mana cikin dare mu mutu” Ladi tace “Gaskiya kam, ku tafi can din kawai ku kwana, don kwana gidan nan ba karamin hatsari bane” Sai kusan karfe tara Hansai ta isa gidan kawun nata da Bibalo, Suna shiga d’an tsakar gidan yace “Me kuma kika xo yi nan kina neman ki ja min fitina Hansatu, ni nasan Iliya d’an daba ne amma bansan dabancin nasa ya kai haka ba, babu irin tijaran da iliya bai xo nan da tawagarsa sun min ba, in don dai shegiyar dubu ukun da kika bani ne cikin kudin sadakin yarinyar Allah ya kai mu gobe da safe in tafi in siyar da kaji na in baki kudinki, wannan tashin hankali har ina a kan dubu uku, wllh ban san tantirancin iliya ya kai har haka ba, to gaskiya baxai yiwu ba kuma ki fitar min daga gida kada ma yasan kina nan in shiga uku” Hansai ta fashe da kuka tace “Amma dai duk hatsin da yake kawo min ina dibar maka har rabin kwano wataran in kawo maka, har gawayi na sha cika maka leda me kayau kayau in kawo maka, kuma matsala ta samu sai ka rufe ido kace xaka koreni, cewa yayi fa xai kona gidanmu, idan na shashantar da batun ya babbake mu cikin dare fa?” Kawu Jibril yace “Toh ni cewa yayi xai ruguje gidan, ganinki ciki ai sai ya kara tunxurasa ya aikata hakan” Hansai na matsar kwalla tace “Yanxu duk ba wannan ba, dama wani Alhaji ne ya xo xai taimake mu kan lamarin da ganinsa babban mutum ne me fada aji, kuma tun mutuwar isuhu yake xuwa siyan awara ya mana ihisani, yanxu dai so yake ku hadu gobe a kan lamarin nan, don Allah ka sanar masa duk mun je gidan radio da gidajen talabijin din kaduna kai rahotu, dubu biyar xan baka kar kaji komai” Yace “Ina dubu biyar din?” Tace “Ba ni nace xan baka ba, fatanmu kawai ya taimakemu Allah ya bayyano mana da shegiyar yarinyar nan mu mika ma Iliya tsiyarsa ko ma sarara, don idan ba nemota aka yi ba aka damka ma Iliya bamu da sauran kwanciyar hankali wllh” Bata jira cewarsa ba ta shige dakin matarsa tana cewa “Lantana duk garin nan babu wanda bai xo min jajen abinda ke faruwa ba amma banda ke, ko ba komai ai sai ki ajiye duk wani tsiya dake tsakaninmu a matsayinki na musulma kixo ki jajanta min wannan musiba da ta sameni…”

07087865788….✍🏻 Start ur payment for the book because i am almost and almost done with free pages kar ku ji dippp an dakata💖

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button