LabaraiYan LuwadiYan Nigeria

Jirgin Da Ya Kwaso Korarrun Ƴan Luwaɗí Da Ƴan Maɗígo Zai Sauka a Nijeriya Yau Alhamis

Daga Shuaibu Abdullahi

Rahotanni a safiyar yau ya nuna cewar wani jirgi ɗauke da wasu korarrun mutane ciki har da ƴan Luwaɗí da ƴan Maɗígo zai sauka a Nijeriya.

Gwamnatin Nijeriya tace tana saka rana karbar mutanen 38 masu neman mafaka waɗanda ƙasar Birtaniya ta ɗauki nauyin dawo da su asalin ƙasashen su.

Rahotan yace ma’aikatar harkokin waje ta gaya wa manema labaru cewa za a dawo da mutanen gida ne saboda laifukan da suka danganci ƙa’idojin shige da fice.

Har ila yau rahotan yace sauran mutanen sun hada da tsofafi maza da mata da kuma masu taɓin hankali.

Sun ce kusan mata 10 daga cikin waɗanda za a mayar na fama da tsananin cutar hauka, kuma ana ba su magani a Birtaniyar.

Masu fafutukar sun ce suna ganin idan aka mayar da mutanen kasashensu, wasu daga cikinsu za su iya fuskantar tsangwama da cin zarafi saboda addininsu ko kuma ɗabi’arsu ta neman jinsi ɗaya.

Kazalika ana saka a cikin wanda za’a kwaso akwai ƴan ƙasar Ghana dake fakewa a ƙasar ta Burtaniya kuma dukan su za’a sauke su a Lagos.

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button