Uncategorized

WAYAFI SONTA 6


 P6

 …..Bayan sun Gama gaisawa,ta body language…kafin Hamza  yafito da kud’i masu yawa aleda yamik’oma zainab! Yace gashi zainab inji abokanmu muka had’amiki wannan sbd kije asibiti “bbu yawa dubu dari 3da75 ne…. ahankali tamasa godiya da hannu kafin tashige ciki…Hamza yabar gun cike da tausayin zainab azuciyarsa Dan yasan Umar yamutu dasonta aransa…

gd zainab ta shiga ta yiwa mama bayani tana hawaye! Mama tayi godiya had’e da saka albarka ,kafin ta Adana kud’in har baba yadawo….. xainab ta bud’e alk’ur’ani Mai girma tana karantawa saratu k’awarta ta shigo d’akin da sallama abakinta” ta zauna gefen zainab harta idar ‘ta ajiye alk’ur’anin ,tad’akko book d biro ta rubutawa saratu cewar Hamza yazo da abinda yabada… kasancewar itada saratu basa b’oyewa juna komai k’awayene na ku’d d k’ud..saratu tayi murna sosai da saka albarka….da Abba yadawo mama tabashi kud’in yagani “yyi godiya….hakan  yakasance duk asibitin da baba yaji labari ko wani Mai bada magani Alan lalurar zainab sai anje ,Amma bbu sa’a aciki”duk abinda suka mallaaka Saida yak’are akan ciwon zainab”duk masu taimakawa sunayi bakin iyawarsu.

Amma abin sai hakuri… zainab ta fauwala ALLAH al’amarinta tasan komai da saninsa hakan Kuma na aka’ddararta” malaminsu na islamiyya yyimata nasiha sosai ,yace tacigaba da zuwa islamiyya ana karatu da ita tunda naji…hakan yasa aka mayar da ita skul tana zuwa part time,tunda tanaji ,inma exam za’ayi zata rubuta… Gaba d’aya Abba ,mama ,Inna dasu Maryam tausayin zainab suke,yau kimanin wata 4 da rasuwar Umar Amma kallo guda zakayiwa zainab kasan tana cikin damuwa! Tayi Rama ,sai tak’ara haske,fuska bbu walwala ga bbu mgn ,danma yanzun sbd Takoma islamiyya da skul yasa damuwar cikin Kashi 10  3 yaragu,Amma kullum jin mutuwar Umar take tamkar sabuwa,in anyi wani Abu yasa ta tunasa,saitaita kuka ,duk sallar dazatayi saita Masa addua….

 

Zaune take tana gurza kubewar da mama tasakata sbd   batasan ganinta zaune tana tunani….ahakan baba yashigo” cike da tausayi yake kallonta ,tamkar yyimata kuka,yanajin tausayinta sosai ,Amma bbu yadda ya iya da ikon ubangiji,yaso afita da zainab  k’asar waje to Amma bbu halin hakan , sannan shi mutum ne dabaison zuwa neman wani Abu gun mutum yafiso yanema agun ALLAH! Mutane sun bashi shawara akan yanemi taimako gun masu kud’i”akan afitada da zainab k’asar waje”Amma yace bazai iya ba… ahankali  baba yace zainab sannu da aiki kinji! ALLAH yyimiki albarka ya albarkaci rayuwarki yabaki ladan jarabawarki….. murmushi tayi ta na d’a hannu sama,shima murmushin yyi Dan rabonda yaga tayi murmushi tun kafin Umar yarasu…. biscuits da cheewingum da chocolate yafito dasu dg aljihu yamik’a Mata….akan idon goggo haule! Gsky mlm baka adalci agdn nan! Sbd ALLAH saika rik’ason Kai Dan ita k’adaice mace agdn nan kana bata Abu,bakaba isah ,Kuma k’anintane….cewar goggo haule ta rik’e k’ugu…Wai miyasa kk hakane?” Ke yanxun bazakiji tausayin taba kodan halin datake ciki”isah dakike maganar k’anintane ,ince ga khalifanan k’anin isane Kuma banbasaba”kirika’ Abu da lissafi,duk ranar da kk koma mun mgn akan abinda yashafi zainab zanbaki mamaki Dan sai ranki yab’aci da uwarta zakiyi kishi bada itaba….cewar baba Yana shigewa d’akin sa…mama ta girgiza Kai tacigaba da gyara wutar tuwo datake tukawa… zainab kuwa dama ta Saba da hakan ,kullum sai goggo haule ta yi abinda zai b’ata Mata Rai ko sakata tuno Yaya Umar..

 

 

   *************

Bayan shekaru 3….

 

Haka dama akace kwanci tashi asarar Mai Rai…. zainab na nan bata warkeba! da larurarta, sannan tagama karatunta dukda ansha wahala da gwagwarmayar rayuwa,…gaba d’aya tasake kyau ta murje dukda batadawo da walwalarta ba,sbd rashin masoyi akwai d’aci,amma tarage yawan damuwa sosai,bbu ruwana da kowa asalima inzata fita nik’eb take sakawa , sannan duk Wanda yanuna yanasonta tun askul bata kula shi,dg baya insungane tanada larura Basu dawowa ,akwai wani Bashir dayasota dukda tana bebiya, amma ita be mataba! hasalima, soyayyar bata gabanta” wannan karatun data Ida da kyar ,tanaso tasami aiki dukda tasan da wuya adauketa aiki Bata mgn…gefe guda Kuma aminiyarta saratu tayi aure… zainab dama can batada yawan k’awaye Dan batasan raini” tafiso ta tsaya matsayinta na talaka…   sukansu iyayenta abin sai hkri wadatar bbu ba kamr daba,danma Yaya Ahmed (Yayan zainab babban D’an mama) Yana aiki agdn Mai ,Yana taimakon baba sosai Dan yanzun haka baba Yana gd bbu sa’a,kud’ad’en jarinsa dasukayi saura yabiyawa zainab su amakaranta,yanzun haka abinda Ahmed yabada kowace ke cikawa tayi girki ranar girkinta”yyinda duk girkin goggo haule sai tayi mita,dukda cewa yanxun Musa yanada adedeta yanasamun kud’i Amma saidai yabata ,baya taimakon baba! Sauran yarnta Kuma akwai masu shaye shaye sai autanta dake SS 2 yanxun…kullum buri. Zainab ALLAH yabata abinda zata taimakawa Iyayenta musammun mahaifinta…

 

Babane kwance k’ofar d’akin sa” Yana waya da Baffa Sule akan Yana hanya zasuzo shida matarsa anty mariya…bayan yagama wayar yadubi goggo haule dake wankin Kaya, kasancewar mama bata nan ammusu haihuwa”yace Kinga haule ajiye wankin nan ki aza abinci ga sule da matarsa nan ahanya zasuzo!…batace komai ba,ta ajiye ta nufi gun baba ,tace to kawo kud’in muga me yadace asiyo a aza…..hannu yasaka a aljihu yafito da wata dari biyar da mama zata fita tabashi Dan tasan goggo haule keda girki,zata iya masifa tace bazata rantaba…awulakance ta dubi kudin Taki karb’a”had’e da cewa banganeba gsky?” Wannan abin yafara isata, yaza’ace Ina aure Kuma Ina ciyar da kaina? Be yuyuwa,yanzun haka Ina binka dubu da d’ari bakwai kak’i biya to wlh bazan rantaba,nagaji….kiyi hkri ki ara wani Abu kihada da wannan d’ari 5 d’in lokaci na tafiya”inkuma bazakiyiba to kibari, wannan halin danike ciki ALLAH ne ya azamun…kadai azawa kanka,wacce kayi Dan ita ,Kuma bbu riba tana nan yadda take…cikin tsawa yace wace irin wawiyar macece ke?” Kafin tayi mgn zainab ta fito fuska bbu walwala da kud’i dubu2500 ta mikawa baba tana Masa nuni Yana goggo haule kud’in ta1500 datake binsa ,yabata 1K tayi girki…yayi shiru kafin yace Ina kika Sami kud’i zainab?” Nuni ta Masa da kakanta mlm yabata 5K ,tabe Baki goggo haule tayi had’e da karbe kudin… zainab kuwa  khalifa ta aika bacin ta rubuta Masa abinda zai siyo Mata…bayan yakawo! Furace da nono da yogurt sai indomie da kwai,ta tada wuta ta aza kafin ta dama furar tasaka acikin fridge din mama  D’an k’arami dake parlourn…Tana xuba indomie d’in taji sallamar baffa sule d anty mariya…da gudu tazo ta rungume anty mariya tana murmushi” cikin sakin fuska anty mariya tace zee y’anmata! Kink’ara girma” kafin ta gaisheda baba da goggo haule dake ta tab’e Baki” tanufi bayi tayo alwallah,suma su baba suka wuce masjid”

Bayan anty mariya ta idar da Sallah, zainab ta xubo Mata indomie da kwai” da fura a jug…kafin takaiwa baffa sule dashigowarsu kenan sundawo dg masjid…baba yyi murmushi yace ALLAH yyimiki albarka zainab yabaki ladan karrama bak’o kinji…tayi murmushi. Kafin ta ajiyewa baffa sule agabansa Dan tasan baba bayacin indomie…furar ta dibarwa baba ta kamasa” baffa sule yyi murmushi yace oh zainab nada hankali wlh ” inajin tausayin yarinyar nan,dama Yaya mak’asudin zuwana akantane gsky! Baba yace banganeba?”

Baffa Sule yace kasan kwanakin baya kafin Umar yarasu naso karb’an zainab ta dawo guna “alokacin Kuma naga yadda suke son juna basa Yi nesa da junaba!baba yace eh nasan da hakan! Baffa Sule yace gsky Yaya inason zainab ta dawo gummu abuja kaga bantab’a haihuwaba ,gdn danike Kuma bbu yara… sannan hankalinta zai kwanta tarage tunani da kewar Umar insha ALLAH zakayi farin ciki da zamanta guna ,Yaya, xainab nada hankali d nutsuwa had’e da tarabiyya,nasan zamuji dad’in Zama da ita”Kuma insha ALLAH akwai wata hospital dazan ruk’a kaita acan,ba’asan inda ake dacewaba….baba yyi ajiyar zuciya yace to shikenan sule ALLAH yasa hakan shi yafi alkhairi” Amma bara mamanta tadawo inji ta bakinta ,dakuma ita zainab d’in”

Baffa Sule yace to shikenan…

Anty mariya kuwa tare da zainab sukaci abinci suna firar kurame ,wata Kuma zainab ta rubuta Mata,gaba d’aya tausayinta yakama anty mariya,fatanta ALLAH yasa iayayen zainab subasu ita ruk’o dukda zainab ba yarinya bace”anzun shekaran ta19_20…Cike da jin dad’in yadda zainab ta tarbisu baffa sule baba ke fira ,Yana kallon goggo haule dake kirgi”

Girkinda sai bayan la’asar akagamashi”su baffama sukace sunkoshi”goggo haule ta tab’e Baki had’e da cewa yak’ara auki….Koda dare ma ,mama data dawo  tayimusu jallop rice sukaci”

Babane zaune ad’akinsa suna mgn da baba akan tafiyar zainab Abuja” Yana Mata bayani tayi shiru tana nazari… yyinda goggo haule ke lab’e bakin kofa tana sauraronsu ,sbd yau girkintane ” taga Kuma baba yakira mama..mama taji ajiyar zuciya tace naji bayaninka ! amma bara na Kira mlm( mahaifinta) nayi mezaice?” To shikenan rakiya ALLAH ya zaba abinda yafi alkhairi….cewar baba yyinda mama kefita” sukaci Karo d haule dake lab’e! Girgiza Kai mama tayi had’e da cewa Wanda yyi nisa bayajin kira!

Duk bayanin dayakamata mama tayiwa mlm tamasa awaya,yakuma bata goyon baya d’ari bisa d’ari had’e da fatan alkhairi ga rayuwar zainab d’in,dukda yaso ace zainab aure tayi sbd shine darajar mace,to Amma komai nada lokaci,yakuma ce aturo Masa ita yabata addu’oi yamata nasiha…washe gari mama ta sanar da baba yadda sukayi da mlm, baba yaji dad’i sosai ” kafin yasanarma baffa sule cewa subari sai gobe saisu wuce tukum in zainab tagama kimtsawa…

 

 

   *********

 

Zainab Tasha kuka jin Wai Abuja zata koma da Zama , Iyayenta zasuyi Mata nisa ,ga lalurarta,wato zata sake wata rayuwa”ALLAH sarki Yaya Umar da yanzun suna gdnsu sunyi aure….tuni mutuwarsa tadawo Mata sabuwa”yyinda mama da anty mariya ke rarrashinta da cewa inbataso bbu tilas tayi zamanta anan kadunan… girgiza Kai tayi sbd zainabu yarinya ce me biyayya”.

Koda taje gdnsu mama gun mlm yamata nasiha maishiga jiki,yabata ADDUA kafin tadawo tasami mama ta had’a Mata kayanta masu darti ta wanke matasu tas dukda masu dattin basuda yawa” gdn saratu k’awarta taje sukayi sallama ta karb’i number in saratun dukda cewar yanzun batada waya,wayarda Yaya Umar yabata ta siyar da ita da dadewa tabawa mama kud’in taja jari…

 

Gaba d’aya adaren ranar zainab batayi bacciba”sbd zulumi da fargaba , musammun inta tuna cewa gdn dasu anty mariya take ,banasu bane,Kuma basu kad’ai bane..ga faduwar gaba da

takeji…washe gari duk Wanda yakamata zainab tayi sallama dashi tayi ,kafin suhau hanyar Abuja itasu anty mariya…. yyinda zuciyar zainab cike da tausayin Inna( mahaifiyar Yaya Umar) sbd sadda zasutafi sai kuka take alamar ta tuna Umar da yanzun ya auri zainab d’in”….

 

 

    Basu isoba sai byn Sallar azahar “suka shigo wata had’add’iyar anguwa”kallo guda zaka Mata kasan ta masu hannu da shuni ne….wani gd had’ad’d’e suka nufa me get fari …suka shige bayan anbude musu get..abinda yafi bawa zainab mamaki ganin gdn zagaye yake da jami’an tsaro(police)byn sunfito , baffa sule yatsaya gun jama’ar Gurin suna gaisawa” yyinda zuciyar zainab ke bugawa har anty mariya taja hannunta sukabi wata hanya dazata sadasu part d’in su…

 

Bayan sun Yi wanka da Sallah ,sukaci abincin da aka aikomasu dashi dg cikin gdn…kafin baffa sule yawuce masallaci sbd sallar la’asar” yyinda anty mariya ta Kira mama tasanar Mata sun sauka lfy…kafin ta dubi zainab tace tashi muje part d’in mutanen gdn dukda sunsan mundawo.. zainab ta tashi dukda aranta bataso zuwaba Amma Yaya ta iyane?” Tabi bayan anty mariya suka  nufi part d’in…. y’ar tafiya ce sukayi kafin su iso gun wata had’add’iyar rumfa atsakiyar rumfar ga kujerunan na hutawa da canter table”sau daya zainab ta kalli gun ta dauke Kai”anty mariya ta k’wank’wasa k’ofar ,kafin ta murda’ suka shiga cikin babban parlourn gdn…wani k’amshi yadaki hancin zainab,ta lumshe ido”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button