Labarai

Yan bindiga sun sace wata mata da diyarta jim kadan bayan sun gama rabawa jama’a kayan fitan sallah a Kaduna

Masu garkuwa da mutane sun sace wata mata da ke aikin tallafawa marasa karfi, Ramatu Abarshi da diyarta

An sace su ne jim kadan bayan sun gama rabawa al’umma kayan fitan Sallah a garin Mariri da ke karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce bai da labarin faruwar al’amarin

Kaduna – Yan bindiga sun yi garkuwa da wata mai aikin taimakon jama’a, Ramatu Abarshi, da diyarta Amira, bayan sun gama raba kayan fitan sallah ga al’umman garin Mariri da ke karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Wata majiya ta kusa da iyalan ta sanar da cewa yan bindigar sun farmake su ne a ranar Asabar da rana a kusa da Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kachia, a yankin kudancin Kaduna, Daily Nigerian ta rahoto.

Misis Abarshi, tsohuwar shugabar sashen Injiniyan Lantarki na kwalejin jihar Kaduna, ta yi suna sosai wajen aikin taimakon jama’a da shirin zaman lafiya a kudancin Kaduna.

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce bai da labarin faruwar lamarin.

Ya ce:

“Kun san mutane basa kaiwa yan sanda rahoton irin wannan lamari a nan take.”

Daga Hausa Legit

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button