Kafin rasuwar Nura Mustapha Waye akwai maganar aure tsakanin mu – Hajara ‘Izzar So’
JARUMAR Kannywood, Aisha Babandi, wadda aka fi sani da Hajara a cikin shirin ‘Izzar So’, ta bayyana halin da ta shiga bayan rasuwar fitaccen darakta Nura Mustapha Waye.
Jarumar, wadda ke fitowa a matsayin ‘yar Matawalle a shirin mai dogon zango da ake nunawa a YouTube, ta faɗa a hirar da aka yi da ita a gidan rediyon Freedom FM da ke Kano cewa kafin rasuwar daraktan sun shaƙu sosai har maganar aure ta shiga tsakanin su.
A hirar, wadda mujallar Fim ta saurara, ta ji jarumar ta na bayani kan irin ƙaunar da ta ke yi masa, har ta ce, “Tun da ma mu na tare kuma shi ne mutum na farko da ya taimaki rayuwa ta har na zama wata, kasancewar ba ni da uwa ko uba, kuma na tashi ne gaban yayar mahaifiya ta.
“Kasancewar ban yi rayuwa da iyaye na ba ya sa rashin su bai taɓa ni ba sosai kamar yadda rasuwar darakta Nura Mustapha Waye ta taɓa ni.”
Ta ƙara da cewa: “Soyayya da maganar aure a tsakanin mu ta yi ƙarfi kafin rasuwar sa, don haka na shiga damuwa har ma ban san irin yadda zan kwatanta yadda na ji ba.”
Jarumar ta bayyana rashin a matsayin abin da ba za ta manta da shi ba, sai dai ta yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayin, ya mayar mata da makamancin sa.