BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 36-40

Page 3⃣6⃣ to 4⃣0⃣

Haka washegari ma data tashi abin mamaki baya karewa,,inna asabe da su rabi ne wai ke aikin gida????karasa wa tayi gurin da suke kafin tace inna kawo wanke wanken in miki,,,da sauri inna asabe tace haba jiddah ai yanzu lokacin hutunki ne ki bari kawai muyi kinji yata ga abincin ki can a dakina ki dauka kije kici sai ki koma bacciin ki,,har ta bude baki zata yi magana inna asabe ta kara katseta haba jiddah baki daukeni uwa bane kome,,aa inna ba haka bane..to kiyi abinda nace kinji jiddah ta,,,juyawa tayi taje ta dakko abincin cikin dakin su ta shige ta zauna tana godema allah daya sa inna da yayanta suka gane gaskiya,,cikin kwanciyar hankali take cin abincin can kasar zuciyar ta kuma tunanin ammar ne fal cikinta..

sai da inna asabe taga shigewarta daki sannan taja tsaki,,rabi ce ta fara cewa,,gaskiya inna jiddah wawiya ce wallahi lokaci daya muka sauya mata kuma wai harta yadda dan shashanci,,hmm kedai bari yarnan ji nake kamar in shaketa amma inaa sai lokacin da burina ya cika sannan zanyi bacci me dadi ina so inga jiddah ta wulakanta ta zama abar kwatance ta yanda ita kanta sai ta tsani rayuwar ta(nikam nace ta allah ba taki ba jiddah tafi karfinki eheee????????)

tunda da dare ammar ke tunanin halin da zai bar jiddah,,ya rasa gane me yake ji akan ta soyayya ko kuma tausayinta kawai yake,,maganar auwal ne ta fado masa a rai..a koda yaushe maganar shi kenan son jiddah kake matuka amma ka kasa ganewa koda yake watarana zaka gane,,hmm ajiyar zuciya ya sauke a hankali daya tuno inna asabe dole ne yakama mata warning kafin ya tafi da wannan tunanin bacci ya daukeshi…

tana gama cin abincin ta fara shirin skul fitowa tayi dan tafiya har takai bakin gida taji inna asabe na kwala mata kira,,juyawa tayi ta koma ciki,tsaye ta ganta a bakin daki,,kudi ta miko mata naira 100 gashi kyasai wani abu ko,,amsa tayi tana godiya kafin ta juya ta tafi,,,tana isa bakin layin ta tarad da shi tsaye,,shima yana ganinta ya taso ya karaso inda take,,gaeshe shi tayi a ladabce..bai amsa ba sai ma kura mata ido da yayi,,dan yaga alamun kamar tayi kuka,,tambayar yayi meya faru,,murmushin yake kawai tayi sannan tace bakomai..jinta kawai yayi amma yasan akwai abinda ke damunta,,kodai asabe ce,,da sauri ta dago ta kalleshi kafin tace ai inna ta sauya yanzu tana sona ta fada tana murmushi..me kika ce ya fada da sauri,,abinda ya faru duk ta fada mishi..shidai yaji kawai amma fa bai yadda da canzawar asabe ba,,akwai wata a kasa yace a hankali,shareta kawai yayi ya taran mata napep tahau,,tana wucewa shima ya wuce gida domin da yamma jirgin su zai tashi,,amma kuma zuciyar shi ta kasa yadda da asabe dan tabbas akwai wata a kasa amma kafin ya tafi sai yaje gidan tabbas…

karfe 1 jiddah ta dawo gida tana shiga daki ta samu abincinta a rufe sai da tayi sallah kafin ta ci abincin..wayar da ammar ya bata ta dakko tana dubawa,,daga yau shikenan ba zata kara ganin shi ba har sai bayan 5yrs hawaye ne ya fara zuba a idonta kafin ta fashe da kuka,,lafiya jidda taji an fada daga baki kofa da sauri ta fara goge hawayen idonta ta fara kokarin kakalo murmushin dole,,karasowa tayi ta zauna kusa da ita kafin tace ki fadamin meke faruwa yanzu nice mahaifiyar ki jiddah kinji fadamin,, maganar tafiyar ammar ta fada mata,,ai inna asabe kamar an mata bushara da gidan aljannah haka taji,,amma da yake munafuka ce sai ta kwabe fuska alamun tausayi ayya jiddah ni kaina naji ba dadi amma wannan shine daidai kinga fa karatu zaije kawai ki masa addu’a da haka ta rinka kwantar mata da hankali har ta samu nutsuwa,,,har ta juya zata fita a dakin ta hango waya a gefen jiddah,,dawowa tayi ta dauki wayar wannan fa jiddah,,abinka ga yarinta sai cewa tayi ammar ne ya bani har da atm card dinsa ya bani,,kinga yanzu ki kawo in aje miki su idan ya tafi saiki fara amfani dasu ko jiddah ta,,washe baki tayi tace to inna asabe

inna asabe na komawa daki ta samu su rabi zaune dama jira suke ta dawo,,ya akayi ne inna indo tace,,kwashe duk yadda suyi da jiddah ta fada musu,,kai amma fa munji dadi aikin mu zai tafi yadda akeso kenan wannan dan daban bayanan,,inna asabe ce tace ke rabi zo in aikeku unguwan rimi keda jiddah kada ki dawo har sai na kiraki a waya dan bana san su hadu har ya tafi nima fita zanyii….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button