Labaran Kannywood

Kalli Jaruman Kannywood 6 da suka rasu da kuruciyar su da kuma cutar da tayi sanadiyar mutuwar su

Dukkanin mai rai mamaci ne! Kamar yadda Allah ya fada mana…

A cikin masana’antar kannywood anyi jarumai da dama,wadansu har yanzu ana bugawa dasu,wasu kuma sun koma ga Mahaliccin su da kananun shekaru,wasu kuma da girman su.

Haka daman rayuwa take babu tabbas,yau kaine gobe kuma waninka…

Ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakken rahoton jerin Jaruman da kuma cutar da tayi sanadiyar komawar su ga Mahalicci.

Ga bidiyon,muma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani.

 

Amfani 5 na gurji a jikin dan Adam:

ABUBAKAR MUHAMMAD USMAN:

Gurji wanda aka fi sani da Cucumber a turance, wani nau’in kayan abinci ne da ke taimakawa wajen saukaka sarrafa abubuwa masu tarin yawa a jikin dan Adam.

Yana dauke da sinadarin ‘Vitamin C’ da ‘Caffeic acid’ wadanda suke taimakawa wajen gyara fatar jiki.

Ga biyar daga cikin amfaninsa a jikin dan Adam:

1. Narka abinci cikin sauki: Cucumber na taimakawa wajen narka abincin da mutum ya ci cikin sauki. Yana kuma taimaka wajen kara garkuwar jiki daga kamuwa da cututtuka.

2. Rage kiba: Cucumber na dauke da sinadarin ‘fibre’ wanda yake taimaka wajen rage ko hana yin kiba.

3. Daidaita ruwan jikin dan Adam: Kashi 96 cikin 100 na cucumber ruwa ne, wanda hakan ke taimaka wa jikin mutum wajen fitar da abu mara amfani daga jikinsa cikin sauki.

4. Warin baki: Wani amfani da cucumber shi ne maganin warin baki. A wasu lokutan mutum na samun warin baki sakamakon wata cuta ko abinci da ya ci, amma cucumber na iya maganin hakan cikin sauki.

5. Kariya daga cututtuka: Cucumber na dauke da ‘antioxidants’ inda yake taimaka wa gangar jiki wajen yakar duk wata cuta da ta shiga jikin mutum a matakin farko.

Cucumber na da amfani mai tarin yawa a jikin mutum, don haka yake da kyau mutane su rika amfani da ita don su amfana.

SHARE

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button